MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL
MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Itako Malika saukan hawayen hajiya bisa Fuskarta,yasa ta farka daga Suman datayi,idanuwanta take kokarin budewa jinta tana jikin wani,Zabura tafarayi tana wani kame jikinta,kamar wacce wanI shoking ke janta,Da hanzari hajiya ta mike tana Fadin”Alhaji kalli kaga Abunda Malika keyi..? mu dauketa zuwa asibiti…”Ganin bayama cikin Hayyacinsa,yasa tayi waje da gudu ta kira su Dose sukazo suka kama mata Malika,suka dauketa zuwa mota,shiko Alhaji sai da Hajiya tazo ta kamashi ya iya mikewa,Ko driving din bashi yayi ba,Deraban Malika ya tukasu zuwa General hopital.
Suna zuwa aka amsheta da gaggawa zuwa emargency,wanda Tunda suka Shiga da ita,har wajen Shida na safe Shuru basu Fito,shiko Alhaji, Abdulmalik kamar wani Mutum Mutun baya mgana sai kuka da sharan kwallah,Tun hajiya na lallashinsa hartazo ta zuramai ido,domin kuka fa yazama dole…
Chan gida kuwa anata cigiyarsu ba”a gansu ba gashi duka wayoyinsu sun barsu gida hankali fa yatashi balle da Joda ta ci karo da lbrin asocial media yana yawo cewa LABARI DA DUMI DUMINSA,AUREN DA”AKA DAURA NA DIYAR SHAHARARRAN DAN KASUWAN NAN DA YARON IGP,TO KUMA AJIYAN MUKA SAMU LBRIN YA DANKARAMATA SAKI,WAI SHIN JAMA”A YA KUKA KALLI WANNAN AL”AMARIN? TABBAS AKWAI ZENCE CIKIN DUHUHankalinta tashe take sanar da mutane Abunda ke Faruwa nan fa gida ya rude da hayaniya ga wayoyonsu duk suna gida,ita kanta malikar wayarta na shiga ammh ba”a dauka,cikin wannan Halin wasu mazan suka tashi suka tafi gidan Malika chan sukejin lbrin Abunda ya faru da kuma asibitin da suke,basai kai ga komawa gida bama,suka rankaya sai asibitin koda sukaje har zuwa lokacin likitoci basu ce komai akan Malikar ba kuma tana cikin emargencyn basu Fito da ita ba.
Achan gidansu Saleem da Abun suka tashi Domin Tun asubayin Fari Ya marwan da Sadiq suka ci karo da Abunda ke yawo hankalinsu tashe suka sanarma Abbi,nan fa cike da mamaki sukayi ta gwada kiran lambar Saleem,ammh akashe sai suka koma kiran Na Alhaji Abdulmalik ammh shima still tana ringing no answer hankala fa sun Tashi nan da nan Abbi ya sanya aka kira chan headquater nasu Saleem ana tambayansu nan take suka sanar dasu cewa jiya jirginsa yatashi zuwa kasar chicago,domin karo cos din da ma”aikata ta turashi na wata uku.
Jin haka yasa gabadaya jikinsu yayi sanyi,domin ga duk alamun akwai kamshin gaskiya,don su basu san da lbrin Tafiyar saleem ko”ina ba,Nan da Abbi yace su marwan su Shirya su tafi katsina suga meke Faruwa,Hajiya babba ko Hannu ta aza bisa kai tana salati tare da kunduma Saleem Allah ya isa,Itako Ummu Zuru tayi tana mamakin ace Dansu da suka haifane ya saki matarsa tun daren Biki,to Abun tambaya bashi yace yana sonta ba ,aka daura mai ba..? bata da me amsa mata wadannan Tambayoyin dole ta hakura,Tuni gidan biki yakoma gidan jimami da takaichi.
****
Karfe 10:30am na safe su Abbi suka isa gidansu Malika nan sukejin mugun lbrin cewa Tun daren jiya suna asibiti da ita,Basu tsaya ba,Tunda suka ji sunan Asibitin suka rankaya zuwa chan,Wani Abun tashin hankalin da sukaje suka tarar shine bayan Malika dake kwance cikin halin ciwo,Shima Alhaji Abdulmalik tun bayan bayanin da likita yayi misu na irin illar da Saleem yayima Malika,don yayimata raga raga ne,bai shigeta da sauki ba,domin sai da suka dinketa sosai bisa yadda ya lalata wajen sosai,kuka yakasa zuwarmai saboda Takaichi da Nadama,Illah jin Likitan kawai yake sanda suke Fadin yakamata su Shigar da karar duk wanda ya aikata musu haka.
Ya Fito daga office din kenan Yaji joda na fadin Irin yadda mganar Sakin na Malika ya zaga Duniya,babu inda lbrin baije ba,Jiri ne ya kwasheshi ya zube kasa babu Numfashi,Shima haka aka kwashe zuwa ciki domin bashi taimakon gaggawa,Koda su Abbi suka kariso babu wanda yayi musu mgana banda Hajiya Binta wacce ta mika musu takardan da Saleem ya Rubutu,Abbi da hannunsa ya karba ya karanta,yana jin kunyar Duniya duk ta lullubesa,tun takardan na hannun Abbi marwan da Sadiq suka karanta Abunda ke ciki,sunma kasa mgana saboda Shiga Rudani da mamaki ko amafarki babu wanda yayi zaton Saleem zai aikata hakan.
Abbi saboda bakincikin kunyar da kuma Yadda Saleem ya bata mishi suna aduniya sai da yayi kwallah,Wani Abun tashin hankali kuma da sanya Raunin zuciya bayanin likitoci kan Fadauwar Alhaji Abdulmalik,wanda sukace zuciyarsa ta harba jininsa yayi bala”in hawa yanzu haka sanadiyar Faduwar dayayi yasamu Shanyewar barin jikinsa na dama.
Gabadaya yan”uwansa haka suke kuka suna tsinema Saleem,da irin cin Amanar dayayi musu,itako Hajiya binta Faduwa kasa tayi hannu bisa kai tana karanta Hasbunallahi wani”imal wakil,Lalle bawa bai isa ya Wucema kaddaransa,ammh wannan Abunda ya faru tasan hakkine da kuma alhakin irin Abubuwan da Malika take aikatawa,wanda mahaifinta Shine silan komai…
Abbi shima banda salatin Babu Abunda yake Furtawa,sai gashi an gunguro Alhaji Abdulmalik zuwa wani daki na musaaman,yayinda ita Malika itama take wani killataccen daki domin samun hutu,,Abbi ko yana share kwallah ya Fito daga Asibitin su Marwan suka Rufamai baya sun Shiga mota kenan Abbi ya kalli marwan yana Fadin”Ka Turama saleem sako ta E-Mail dinshi ka sanar dashi nace Wlh tallahi matukar bai janye sakin dayayima Malika ba,Toh ni Kabir kumo na cireshi har abada daga cikin ya”yana…”Yafada yana jin kamar ya kurma ihu saboda Nadama.
gyada kai Marwan yayi yana Fadin”Toh Abbi…”Daga haka motar tayi Shuru suka Fice daga asibitin suka dauki hanyar Abuja,Shiko Sadiq kara gwada nombar Saleem yake,ammh bata aiki sam,sai kawai ya hakura,ammh shima yayi alqawarin Turamai sakon Abunda ya aikata ta E-mail dinshi..
Kuyi hakuri da Typing errors,ban samu lokacin Editing ba.
Ammh ta hanyar nuna min kauna da soyayyarku wajen Siyan MALIKA MALIK Akan Naira 200 kachal????,ta wannan account Nombar, *0552179550 JAMILA UMAR GTB,sai ki Turo Shaidan biya ta wannan nombar *09069067488* ko kuma katin waya na MTN,shima sai ki Dauki hoton katin aturo kai tsaye ta wannan Nombar 09069067488 Sai kun zo ina maraba daku masoyana..
Karku manta da garabasanmu mai son Siyan Biyu KISHIN MATA,na HAFNAN,300 ne kachal????shima zai iya Turo ta nombar bankin dana bada ko katin waya na MTN ta nombar saman dana bada, ko kuma kai tsaye ku Tuntubemu ta wadannan Nombobin domin karin bayani…
07065481260..Ko kuma 09069067488
Shakira
MALIKA MALIK…!
(Sai na rama..)
ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى ASSɷ????
Mallakar:Janafty????
Littafin MALIKA MALIK Na kudi ne ki biya akan Naira 200kachal????ki turo ta account Nomba kamar haka 0552179550 JAMILA UMAR GTB bayan kin dauki hoton Sreenshoot din Transaction din,sai ki turomin ta wannan Nombar 09069067488,Ko kuma katin Mtn ta wannan Nombar 09069067488 shima kai tsaye bayan an dauki hoton katin sai aturo*
I Dedicated dis page to u guyzs MALIKA MALIK PAID GROUP,and HAFNAN AND JANAF PAID GROUP,Tanque Dearests,For u true Love and Support,and A big Thanks to u For ur wonderfull and Amarzing commenting, Sakallahu Fil Jannatul Firdausi Ameen????
11
“Da wannan bakin lbrin su Abbi suka koma ma su Ummi,wanda suma Abun yadakesu sosai,Abbi kuwa daki ya shige,ya kwanta yayi Shuru cike dadamuwa domin Tundaga wayewar gari zuwa yanzu baisan adadin mutanen da suka kirasa ba,suna tambayansa,game da al”marin ba,Toh mezaice musu banda eh,Domin bashi da ikon boyee Abunda ya Fito Fili,gabadaya kunyar Alhaji Abdulmalik da Duniya gabadaya ta kamashi,yarasa ina zai saka kanshi,saboda yana Tunanin koda zai kwana yana rantsuwan baisan gudurin Saleem akan Malika ba,wlh karyatashi za”ayi,Tunda da kafarshi ya taka yaje nema masa auren nan,ammh wlh ko alama baida sani game da mugun kudirin Saleem.