MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Ita ke zama da ita koda bazasuyi dogowar hira ba,mutum ma rahama ne,kuma Afuskar Malikar zaka Fahimci tana jin dadin zama da joda sosai,haka joda zata dage tayi ta bata lbrin rayuwarsu ABU chika da suka je pratical,itako tana Saurarenta sai dai kawai taga ta murmusa alamar tana jin dadin zama da ita sosai.


Lokacin da Ya marwan yaga sakon Saleem,tsaki yaja ya Fice ko amsa bai bashi ba,sai dai ya kira Abbi ya sanar dashi Abunda Saleem din yace,yaji dadin hakan duk da bai nunama Marwan din ba,ammh shi ya Fahimci hakan..

Abbi bai yarda al”qawari ba lokaci bayan lokaci yana zuwa ya Duba Daddy,su Wuni suna shan hiransu,wani lokacin in yazo har yatafi baya saka malika a idanuwansa,wani lokacin ne takan Fito su gaisa sama sama ta koma daki gwanin ban tsausayi,Duk da yanzu tana kokarin sallah akan lokaci,sai dai Abunda ta gaza samu wanda zai zaunar da ita ya koyamata addinin da kyau shine bata dashi,sai dai kawai Abunda ta iya takeyi,sallan nata ma ba cikakka takeyi ba,balle in ta idar tana son yin addu”a akan Halin data ke ciki,ammh bata iya ba,sai dai ta zauna tayi zuru tana sharan kwallah,tana fadin aranta Allah ya sakamata kawai.

Shiko Saleem,tundaga wannan sakon bai kara turama kowa sako daga gida ba,duk da yaga Ya marwan din ya bude sakonsa,ammh ya Fita batunsa bai bashi amsa ba,bai damu ba dama burinsa sakon ya isa ga Abbi,kada sai ya koma gida Abbi ya batamai rai Fiye da yadda shi ya bata mishi.

Shiyasa ya maida hankalinshi kan Abunda ya kaishi yana kokarin yagama komai kafin ya koma gida ya Tunkari Abunda ke gabanshi,domin yasa tabbas,zai Fuskanci barazana daga iyayensa nasa,wadanda suka dauki Fushi dashi sosai akan lamarin Yarinyarnan,koma menene ya Shirya tsab wlh ko da anshashi dole ya zauna da yarinyarnan,Tohpha sai ya kara amfanin da wannan damar domin Ninka ramuwarshi gareta.

   *

AFTER 2 MONTH

  Kwance tace bisa makeken gadonta ta dunkule cikin blanket,tana ta rawan sanyi domin kana jin yadda hakoranta ke bugan juna,Tun kwana biyu da suka,wuce takasa gane kanta,kwana take da zazzabi ga tashin zuciya,kuma sometimes tana Fama da taruwar miyau abakinta,ga kasala da yawan Mutuwar jiki,barci ko bata gajiya da yinsa,tarasa wazata fadama damuwarta ne,Ko jiya Da hajiya ta ganta sai da ta tsaya Shuru tana kallonta kafin ta tambayeta meke damunta,yamutsa fuska tayi kafin tace itama bata sani ba,kuri tayimata da ido kafin ta kada kai kawai ta Wuce batace komai ba,ammh cikin ranta gabanta yana bugawa kada Allah sa hasashenta yazama gaskiya.

Yau Abun yayi tsanani don dakyar ta iya tashi tayi sallar Asuba,ta koma zazzabin ya rafketa,ganin har karfe 10:00am na safe bata Fito ba,toh a kidanta gari na waye zata Fito taje Falon Abbanta inda yake xaune bisa kekensa ta gaisheshi,su dan taba hira kafin ta koma daki,ammh yau ko Duriyarta baiji ba,shiyasa ya damu yama hajiya binta mganar don Allah ta Dubomai Bby tana lafiya kuwa?..

Ita ta shiga da kanta har dakin nata,ta iske su Dose suna ta gyaran Falon,gaiaheta sukayi ta amsa tana tambayansu ina Malika,nan suke sanar da ita Madam,tun jiya bata Fito ba kada kai tayi,kafin ta tura kofar bedroom din ta shiga da sallama,Sai dai ta dade tsaye tana dube dube kafin ta hango malikar kundundune cikin bargo tana makyarkyata,da hanzari ta karisa gareta tana Fadin”Malika…”Take Fada tana zama kusa da ita,

Jin Shuru yasa ta yaye bargon jikinta tana Fadin”Lafiyanki kuwa yau shuru….Ashhh..!Mganarta ta katsene sanda ta taba goshinta taji zafi rau,waigowa Malika tayi tana rike bargon jikinta na rawan Sanyi tace’Banda lafiya ne Hajiya Tun jiya da daddare…”Hajiya binta tace”,Wayyo sannu bari naje na sanar da Alhaji dama shi yace na duboki yajiki shuru,ammh ki tashi kiyi wanka ki karya kafin nayima Dr Abbas Waya..”Da kai ta amsa kafin takara dunkulewa cikin bargon.

Hajiya binta tadade tsaye tana kallon Malika kafin ta Fice daga bedroom din,Su Dose ta umarta dasu hadama Malika Ruwan wanka itama Merry tace mata ta sauka kasa,taje kichen ta amso breafsat din Malika,awajen Atika da toh suka amsa kafin kowacce Ta nufi inda aka sata.

Koda Hajiya binta ta sanar da Daddy hankalinshi ya tashi jikinsa na rawa yace ta kiramai Dr Abbas tace yazo da hanzari Babby ba lafiya, hajiya na sanar dashi yace gayinan ahanya zashi asibiti ammh gashinan zuwa.

Tagumi yayi yana Fadin”Haba shiyasata najita shuru,meke damunta ne Binta..? ajiyar zuciya ta sauke kafin tace”Zazzabi ne inaga,don jikinta yayi zafi sosai…”Girgiza kai yayi yana fadin”Binta zuciyata takasa natsuwa taimakamun zuwa dakin Baby don Allah..”Bata yi gaddama ba ,ta isa bayanshi tafara turashi zuwa dakin Malika.

Koda suka shiga harta fito wankan,ta shirya cikin wata doguwar riga,ta koma ta kwanta tana nishi,Hajiya ce ta shiga ta rikota suka Fito falo ta kwantar da ita kan kujera,Daddy ya karisa gareta yana kan kekenshi yake fadin”Sannu Babyna…”Dakyar ta dago tana kallonshi hawaye suna gangaromata,bata iya amsawa ba,illah rarrafowa datayi ta kwantar da kanta bisa cinyarsa tana nishi dakyar.

Hannu yasa ya dafa kanta yana jin yadda jikinta ya dau zafi sosai,Shafa kanta yake yana jeramata sannu,kafin ya kalli Hajiya binta yana fadin”Binta nace ko zata ci wani abun ne kafin Dr Abbas yazo,kila yace zai maka allura ma..”gyada kai Tayi kafin tayi mgana ma merry dake gefe ta shiga kwaso kulolin data dauko da kasa tana jerawa gaban Alhaji Abdulmalik,wacce malika take kwance kan kafafunsa,rabin jikinta na kasa tana nishi sama sama.

Dakyar Daddy ya iya lallabata ta sakeshi ta zauna ta jingina da kujera tana yamutsa fuska,tunda aka bude Ferfesun kayan cikin,taji zuciyarta na tashi,ta kauda kai tana wani toshe hanci,mamaki ya kama Daddy ya kalleta yana Fadin”Bby menene…? Kuka ta fashe dashi kafin tace”Daddylove zuciyata tana tashi adaukemun shi daga gabana,inaji kamar zanyi amai…”

Da Sauri ya umarci merry data Rufe kolan kafin ya kalleta yana Fadin”To an dauke yanzu me zaki ci,ta hada miki tea,…? Gyada kai tayi duk da batason cin komai,ammh bata so tabar Daddynta yana zama cikin worry akanta.

Tea din ta hadamata ta mikamata cikin wani kofin glass,mai kyau karba tayi tafara kurba ahankali,ko Kurba uku batayi ba tafara jin zuciyarta na tashi,tayi saurin mikama merry Kofin bata kai ga mgana ba,taji Daddy na Fadin”Haba Babby ki daure kisha mana,ga Dr nan zuwa yanzu sha kigani…”,tana so tayi mgana Abun takasa saboda yadda madarar ke taso mata,amai taji ya zomata da karfi ko kafin ta mike tafara kelayashi awajen cikin kayan abincin dake gabanta.

Daddy yace”Subhannallah..,Binta kamata karta fadi…”Da sauri Hajiya ta karisa tana riketa tare da jeramata sannu,sai da ta amaye dan shayin data sha tas,kafin wani ruwa ruwa ya biyo baya yunkuri take,ammh komai baya Fitowa saboda babu komai acikinta,shiko yana gefe yana jeramata sannu kamar zai mata kwallah Fadi yake”Kai wai ina Dr Abbas ya tsaya ne..? yake Fada cike da damuwa.

Sai da tagama kafin tayi baya jikinta babu karfi hawaye suna Fita daga idanuwanta,Saboda yunkurin aman har Fitsari tayi awajen duk ta bata rigar dake jikinta,Kan kujera Hajiya ta kamata ta kwanta tana maida numfashi,su kuma su Dose suka fara kokarin kwashe kololin da ke wajen ita kuma ta dauko Abun goge goge, tafara goge wajen,suna cikin hakane Dr Abbas ya kira wayar Daddy yace gashi awaje.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button