MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Hajiya binta tasauko taje ta mai jagora har zuwa sama Falon Malika,inda sukayi musabaha da Daddy yana tambayanshi ya jikinsa,amsamai yayi da”Jiki yayi sauki,don Allah Dr Bby zaka dubamin tun jiya take fama da zazzabi,yau da safe kuma jikinta yayi zafi,yanzu haka ka ganta nan amai tagama..”

Yafada yana nuna mishi ita,Jinjina kai yayi ya karisa gareta,durkusawa yayi gabanta yayi yana Fadin”Sannu Madam,…”Dakai ta amsa idanuwanta na lumshe,ita kadai tasan halin data ke ciki,kallonta yayi yana nazarinta kafin yace”Plz madam,ko zaki iya tashi,saboda na dubaki da kyau…”jin haka yasa tafara yunkurin tashi da sauri Daddy yace”Don Allah Binta taimakamata…”Yafada yana Tura keken nashi zuwa gaban Malika.

Ita ta riketa tatashi zaune bayan ta jingina da cussion din kujera tana maida numfashi,mikewa yayi kafin yadan rankwafa,yasa hannu ya dalle mata ido duka biyun,yana kallo kafin ya saketa,ya koma ya riko duka tafukan hannuwanta yana kallo kafin yace”Arm madam plz yaushe rabonki da ganin period dinki..? Bude ido tayi ahankali tana kallonshi kafin ta bude baki ta kyar tace”2 month kenan,+ dis month shima ban gani ba haryanzu,kuma date dina 16 ne.. “Tafada tana yamutsa fuska.

Gyada kai Dr Abbas yayi kafin yace”Is ok bari na Dibe jininki na tafi dashi lab,su auna buh ina kyautata zaton madam u are pregnant…”Gabdayansu suka raazana da jin wannan mganar daga bakin Likitan,Daddy ne ya zaro ido yana kallon Hajiya binta,wacce tayima Malika kuri,domin dama zuciyarta tun shekaran jiya take hasasomata Allah yasa Malikar ba ciki ne da ita ba.

Itako Malika tana da kishingide sai gata zaune digigir da kanta idanuwanta duka awaje tana Fadin”Dr Wit pregnant,plz stop dis joke don Allah…”Tafada cikin tashin hankali,da Sauri Dr Abbas yace”No bani da tabbas,buh duk wasu symtoms na masu juna biyu ya bayyana atare dake,so yamzu mu bari har na kai jininki zuwa lab,su auna su gani….”Ya fada yana bude wani karamin akwati daya zo dashi.

Siranji ya dauko tare da allura ya hadasu waje daya,ya riko hannunta ya dibi jininta,kafin ya sanya mata auduga ya danne wajen yana jeramata”Srry..Srry….”yana gamawa ya maida komai cikin dan akwatun nashi ya mike yana fadin”in na tashi aiki kafin na wuce gida,zan biyo na kawo muku result din…”Godiya Daddy yayi tamai kafin su sake musabaha ya fice yana Fadin”,Allah kara lafiya Madam….”

Koda Dr Abbas ya fita ba wanda ya samu zarafin magana,banda shesshekan kukan Malika daya cika dakin,Daddy ko kansa ya sunkuyar yana jin kamar zuciyarsa zata Fito waje saboda yadda take harbawa.,Hajiya binta ko na zaune gefe tana girgiza kai kafin tace”Sai hakuri Alhaji,ammh tabbas ko ni naga alamun Shigan karamin ciki atare da malika,bandai yi mgana bane saboda ban tabbtar ba….”

Dagowa Yayi idanuwansa jawur yana fadin”Ciki kuma binta,innalillahi ina Bby zata kai ciki awannan halin datake ciki…”Yafada yana kallonta,gyada kai hajiya binta tayi tana Fadin”Haihuwanshi zatayi Alhaji,toh zamu zubar da Abunda yake da shakikin mahaifi na sunnah,ai da an tabbatar da cikin ka kira Kabir kumo ka sanar dashi Abunda ke Faruwa,nasan suma bazasu ki karbanshi ba,tunda dansu ya digashi…”

Ajiyar zuciya ya sauke yana jinjina kai alamun gamsuwa da mganarta,kawai basu ankara suka ga Malika ta mike tana tsalle bisa kujera tana dukan cikinta tana kuka da ihu kamar wata mahaukaciya tana fadin”Bani son wlh bazan haihu ba,zan kashe kaina wlh…”Take fada tana buga jikinta da duka hannuwanta biyu tana kuma tsalle atare…..

Da hajiya binta Da Daddy dake kan keke ba”a san wanda ya riga wani ba,shidai Daddy ji yayi kafarshi na rawa kokarin mikewa yake ammh yakasa saboda yanayin jikinsa komawa yayi ya lafe bisa keken yana Fadin”Binta taimakeni ki riketa kada tama kanta ta lahani, Wayyo Allah!…? yafada wasu kwallah na zuraromai,…

Dakyar Hajiya binta ta riketa,rumgumeta tayi tana kuka mai cin rai take fadin”Hajiya ya zanyi…? me zanyi kuma? Hajiya ki sanar dani wata addu”a akeyi mutum ya mutu ya huta da wannan Duniya da babu komai cikinta sai bakinciki,…”Take fada tana kamkameta cike da tashin hankali,

Rumgumeta hajiya binta tayi wani tsausayinta na Tsirgamata tace!”Ki daina Fadin Haka,babu wata addu”ar mutuwa aduniya sai dai Addu”ar da in wani bala”i ya kusanto ka sai ka karanta,ki maida kukanki ga Allah Malika,don bazaki iya chanza kaddaranki ba,kiyi ta karanta INNALILLLAHI WA”INNA ALAIHIRRAJU’UN…Insha Allahu zakiji sauki azuciyarki…”

Ahankali ta shiga maimata kalmar asarari,tanayi tana zubar kwallah,Hakama Daddy dake gefe shima tayata maimatawa yake yana sharan kwallahn shima,Malika ne ta kalleshi taga yana kuka,saboda tsausayinshi da kaunarshi bata san sadda ta saki hajiya ba,tatafi gareshi ta fada jikinsa tana kuka harda sheshaheka tana Fadin”Am srry Daddy,plz stop carrying,i love u, i dont want to lose u…..”

Take Fada tana zame kanta bisa cinyarsa tana kuka da duka karfinta,Kanta yake shafawa har zuwa bayanta,hawayensa suna gangarowa zuwa Kanta yake Fadin”Nabari Babby,ammh nima ki taimakeni kada ki kashe kanki,in kika aikata haka wlh zan zama gafaalle,aduniya kuma asararre aranar gobe kiyama…”Damke hannunshi tayi tana Fadin”Am wit u Forever and every Single day of Forever Daddylove,plz Forgive me….”Take fada muryanta ciikin kuka.

Hawaye yake share mata itama tana sharemai,Hajiya binta dake tsaye gefe,itama kwallar ta share tana jin kamar tayima Malika da Alhaji kuka mai yawa,yau din da suka bata tsausayi Fiye dana kullum.

Ammh ta hanyar nuna min kauna da soyayyarku wajen Siyan MALIKA MALIK Akan Naira 200 kachal????,ta wannan account Nombar, *0552179550 JAMILA UMAR GTB,sai ki Turo Shaidan biya ta wannan nombar *09069067488* ko kuma katin waya na MTN,shima sai ki Dauki hoton katin aturo kai tsaye ta wannan Nombar 09069067488 Sai kun zo ina maraba daku masoyana..

Karku manta da garabasanmu mai son Siyan Biyu KISHIN MATA,na HAFNAN,300 ne kachal????shima zai iya Turo ta nombar bankin dana bada ko katin waya na MTN ta nombar saman dana bada, ko kuma kai tsaye ku Tuntubemu ta wadannan Nombobin domin karin bayani

07065481260..Ko kuma 09069067488

Janafty(Momyn ladingo)

MALIKA MALIK…!
(Sai na rama..)

ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى ASSɷ????

Mallakar:Janafty????

Kada ki karanta inda baki biya ba,inda kina so kiyi karatu cikin salama ki biya kudin karatu akan 200???? ta wannan account 0552179550 JAMILA UMAR Gtb din,ko kuma katin Mtn ta wannan Nombar 09069067488,Aturo hoton kai tsaye,Bazan muku Allah ya isa ba,ga wanda ya karanta bai biya ba,sai dai zan bar mutum da mai Duka wanda ke sama yanan nan madakata

KURIKE GIRMAN AMANAR DANA BAKU,KUYI MIN ADALCI KAMAR YADDA NAYI MUKU KADA KU FITARMIN DA BUK WAJE DON ALLAH????

13

   “”A daren Ranar Dr Abbas,ya kawo sakamakon gwajin Malika inda sakamakon ya nuna Malika tana dauke da ciki har na tsawon Sati goma,wato wata biyu da sati biyu kenan, malika ta karbi takardan ta Tsurama ido,sai taji kwallah na zuraromta,lokaci daya dawani takwalli da kuma natsuwar zuciya Tun bayan data dinga maimaita Innalillahi wa”inna Alaihirraju’un,kawai don kuka ya zama dole ne gareta,ammh lokaci daya tana jin tana bukatar itama abokin da zai kasance shi kadai ne zaiji kanta Aduniya,shiyasa ta daura kudirin kullah kawance da Abunda ke cikinta,kila watarana shi zai zama gatanta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button