MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Hankalin Daddy ya bala”in kwanciya lokacin daya ga Malika ta kwantar da hankali,bata kara nuna damuwarta kan cikin ba,Dr Abbas da kanshi ya kawo mata magungunar karin jini,da kuma na sa cin abinci,yawan tarun miyau kuma datakeyi,ya umarce ta data rika yawan shan sweet hakan zai taimaka ya rage tsinka mata yawu.

Mganar Amai kuma yace sai zuwa cikinta in yayi kwari,ammh yace taguji Abunda bataso,saboda shima yawan aman yana sakarma damai ciki jiki,duk sai tazama ba kuzari atare da ita,wani lokacin ma sai anyi mata taimako da drip ko zata samu karfi,ta karbi duka dokokin likita da hannu biyu kuma ta shiga kokarin kiyayewa,Sai dai Abun da bata gane ba Hajiya binta ta taimakamata.

Sai washegari kana Daddy ya kira Abbi ya sanar dashi Abunda ke Faruwa,
Abbi na zaune bisa kujera afalonsa Ummi na gefensa alokacin,Mikewa yayi Tsaye yana Fadin”Allahu Akbar..!Allahu Akbar..!Allahu akbar…”!Har sau uku yana nanatawa kafin yace”Kaji ikon Allah ko Abdulmalik,Wlh rabon dake tsakaninsu ne yasa akayi auren nan cikin gaggawa,da”ace munyi tsaiko ko munyi gaddama toh da Allah ya nuna mana karfin rabo,ko wani cikinmu ya bar Duniya,ko asamu cikin ta wata hanya,wanda dukkanmu bazai mana dadi ba,Kai Allahamdulillahi Allah Abun godiya,ina malikar tana lafiya ko? Yafada yana bayyana Farincikinsa Amganarsa.

Daddy yana mirmishi yake Fadin”Hakane wlh Abokina,sai mu godema Allah,Malika na nan lafiya,sai dai Abunda ba”a rasa ba,kasan masu shigar sabon ciki sai ahankali,wuni take amai komai taci sai ta dawo dashi,abincin ma ba sosai take ci ba…”Jinjina kai Abbi yayi kafin yace”Allah sarki hakane Abun sai ahankali agaisheta kafin muzo,kuma insha Allahu mijinta nadawo zai zo ya dauki matarsa ya kuma baku hakuri insha Allahu.

Daddy yace”Ayyah bakomai kumo,Allah dai ya Rufamana Asiri kawai..”Nan suka Cigaba da tattaunawa kafin su yanke kiran,Ummi dake gefe ta zaku ya gama wayar taji wani Abun Farinciki ne ya samu haka,yake ta faman washe baki yana kabbara.

Nan yake sanar da ita Abunda Daddy ya sanar dashi,Washe baki tayi tana hamdala ga ubangiji take Fadin”Masha Allahu da samun Surikar Farko,kuma Alhamdulillah da samun karuwar jika agidanan akaron Farko…”Take Fada duka hakoranta waje,Mikewa tayi tana Fadin”Bazan ji wannan Abun Farincikin ni kadai ba,dole sai Hajiya taji itama..”Ta fice yana mata tsiyan ko kunya,itako tana Fadin”Ba marwan bane,saleem ne ba Dan Fari bane balle yace wani Abu..”

Da Hajiya Babba Taji rike Ummi tayi tana Fadin”Don girman Allah Da gaske kike Aisha…? Tafada tana zaro ido,Rantse mata tayi tana sanar da ita shi mahafin malikan da kanshi ya kira waya ya sanar da Abbi,ai Hajiya Sakin Kabbara tayi itama kafin tace”Kai Salihu Dan albarka ne,da haushinsa nakeji game da ta”asar da yayi ammh yanzu ya wankemun zuciyata kal,kai ni wlh duk gidan nan ko Kabiru yanzu bai kai Saleem Farantamin ba,shi yafara yin aure agidan nan,gashi kuma shi zai Fara haifamin tattaba kunnina ina raye…”Tafada tana sharan kwallah Farinciki,lbri fa ya zaga ko”ina hatta Saleema dake mkranta tasamu lbrin nan,wanda Sadiq yake sanar da ita,shima Ummi ta gayamai shiko Marwan yana chan ya samu lbri jinjina kai kawai yayi yana Kiyasta dama ana samun ciki daga zuwa daya????????,lalle ko in hakane ya jinjinama Karfin mazankutan kanin nasa.

  *

Jirgin daya kwaso al’ummah Dabam Dabam daga birnin na ikko wato lagos shine ya yada zango A babban Filin jirgin Mallam Aminu kano international Airport.

Acikin wanda jirgin ya sauke harda Acp Saleem kabir kumo,wanda ya sauka jiya da daddare,daga kasar ta chicago,to dama dayake jirgin daya shigo wanda zai yada zango a lagos ne,shiyasa ya kwana a hotel da safe kuma ya biyo jirgi zuwa kano.

Tafe yake wayarsa makale akunnasa yana sanar da Inspector sale,gayinnan karisowa,sanye da riga da wando black and White,na kamfanin armani,sai wata jaket daya dora asaman farar rigarsa,jakar brief case dinsa ne makale ne kafadansa,sai kafarsa dake sanye da Rufaffen Takalmi na Fatan damisa.

Hankalinsa na kan wayar da yake yi sai ji yayi gam!an ban gaje shi yayi baya har sai da wayar hannunsa ta subuce masa ta fadi kasa ta tawartse, dagowa yayi cikin zafin nama yaga wani banzan ne,wanda ke Tafiya baya kallon gabansa.

Ita kuma ta taho tana sauri hankalinta yana ga Best dinta tada hango,hannu ta dagamata jikin ta na rawa ta nufeta,ashe shi kuma saleem ya taho,kawai sai ta bangajeshi batare dama ta lura ba,sai da mai afkuwa ta Faru.

Durkushewa tayi tana tararra mai wayar tana Fadin”Oh! my god…Na bani ni Zahra…”Take Fada tana kwaso mai part part din wayarsa data baje akasa,Dagowa tayi daga tsugunnan ta mikamai wayar tana Fadin”Am so srry  I don”t know dat u ar coming kayi hakuri…”Ta fada lokacin data sanya idanuwanta akansa bata san sadda ta Furta “Wow…!!!…”Saboda yadda gayen ya Tafi da duka imaninta.

Shiko sagale yayi yana binta da kallo,kyakyawan Budurwace,doguwa mai kyan tsari da jiki dana Fuska,fara tas,ammh daga kallon Farko zaka Fahimci tana da rawan kai da kaudi,Sanye take da riga da sikat na wani leshi mai adon duwatsu,ta sanya babban mayafi ta Rufe jikinta,cikin Abunda baifi sakan goma ba,ya kare mata kallo,itako bakinta sake tana binshi da kallon kurillah zuciyarta na bugawa.

Yaken baki yayi mata kafin ya mika hannu yana fadin”Is ok…”Ya fada yana mikamata hannu da nufin ta bashi wayarshi,gani yayi hankalinta baya jikinta ta saki gabadaya hankalinta akanshi tana kallonshi,wani takaichi ya cikashi,da dan karfi ya Furta”Hy…”

Sai gashi tayi Firgigit ta dawo hayyacinta,bai mata mgana ba,illah hannun daya mika mata,kunya duk ta kamata tana sosa keya ta mikamata tana fadin”Tanque sir…”Kanzil bai ce mata ya ratsa ta gefenta zai Wuce ganin da gaske yake tafiyan zai yi yasa da azama tace”plz Nace ba…?.

Cak ya tsaya kafin ya waiwayo yana Fadin”U say what…? Mirmishi ta sakamai kafin ta mikamai farin hannunta tana fadin”Am ZAHRA BUKAR MADA by Name, inko…? Wani kallo ya watsa mata kafin ya dan ciza gefen bakinshi yace” Am ACP SALEEM FREEKING KABIR KUMO…”Da hanzari ta katseshi tana Fadin”Wow Fabulos,ashe ina tare da ACP ne,kai Nice to meet u Sir…”

Mirmishi yayi mata,ganin yadda take wani rawan kafa,yana shirin barin wajen takara cewa”Plz sir can i hv ur digit…? Zaro ido yayi yana fadin”Whta…? Langwaba kai tayi tana Fadin”Plz Sir…,? Bata rai yayi saboda tsakani ga Allah ta isheshi agogon hannunsa ya duba kafin yace”Ok 080…….'”????Haka ya rattabamata tana kwashewa bisa wata faskekiyar wayarta kafin ta gama tana Fadin”Tanque Sir…”

Juyawa yayi yana Fadin”U ar wlcom…”Da kallon sha”awa ta bishi ganin yadda yake takunsa cikin isa da takama,tana kallonsa har suka hadu da inspector sale,suka yi musabaha suka gaisa,kafin su danyi wani mgana,suka kara musabaha,kafin ya bashi key din motarshi sukayi Sallama daganan shikuma ya Fada motarsa kirar 4matic ya Fice daga Airport din da hanzari.

Hankalinta na wajensa sam bataji karosowar mutum akusa da ita ba sai ji tayi an daka mata duka abaya,Zabura tayi zata saka ihu sai ganin BEST NADIRA  Dinta wacce ke tsaye jaye da Trolly dinta tana zabgamata harara,da hanzari ta Fada jikinta tana Fadin”Wlcm home my best,kefa nake ta jira tun dazu..”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button