MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Yana ganinta yafara taku zuwa gareta yana Fadin”Yauwa hajiya don…”Saleem zanci mutumcika nace kayi baya kaficemin daga gida ko?

Cak ya tsaya yana kallon Abbi shiko kara tamke Fuska yayi yana Fadin”Ficemin daga gidana,ai kaji sakona wlh tallahi indai ni kabiru ni na haifeka bazan yadda kacigaba da amsa sunana amtsayin sunan mahaifinka ba,sai ka juya daganan katafi katsina ,kaje kabama Mahaifin Malika hakura ka kuma dauko matarka ku dawo cikin gidan nan tare,na ganka ka Shigo kafarka kafarta,sannan zan yarda ka sake shigomin gida har ka rabi suna na amtsayina na mahaifinka,in kuma ba haka ba,Wlh tallahi bani ba ka Saleem har Abada kuwa kajima na rantse….

Yana gama fadar haka ya juya yana Fadin”Aisha kawomin Ruwan zafin..”Daga haka ya haura sama ransa bace,toh Ummi tace bata ko kara kallon Saleem ba ta koma kichen ta dauko Fulas din ruwan zafi da kofi tayi hayewarta sama,Hajiya babba ma kallonsa tayi kafin ma tayi mgana taga ya juya Fuu..!ya Fice kamar zai tashi sama baki ta rike tana fadi afili…

“Anya wai yaron nan kalau yake…? kai ban yarda ba kila dai ya fara shan kwayoyin zamani…”Tafada tana kara rike Haba, kafin ta juya ta koma dakinta tana sababi ita kadai.

Ayi hakuri Typing errors am too busy bansamu lokacin tantancewa ba

Shakira
 

MALIKA MALIK…!
(Sai na rama..)

ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى ASSɷ????

Mallakar:Janafty????

Ki biya ki karanta cikin Salama,akan 200????Akan Account Nomba, 0552179550 JAMILA UMAR Gtb,ko kuma Katin Mtn ta wannan nombar 09069067488

Wannan page din ya zama Free page ga kowa da kowa,sakamakom samun wata baiwar Allah masoyiyar kwarai gareni daku gabadaya data sanya zunzurtun kudi ta Siya wannan page din tace ayadashi ako’ina,kuma kowa ya karanta,hakika baka iya ganin masoyinka na gaskiya sai hakan ya Faru dakai,wlh tallahi dalilin Rubuta Novel din MALIKA MALIK na hadu da masoyana Wadanda banta  zato ba,balle tsammani babu Abunda zence ga Allah sai godiya garesa domin da kudiransa komai ke Faruwa,Ina rokon don Allah duk wanda ya karanta wannan page din ya sanya MY BEST HALIMATU Cikin addu’anku,Tare da fatan Allah yayi mata sakayyah da gidan Aljannah Firdausi Ameen

* I love u so very much from d bottom of my hrt, may Allah shower his blessing upon u, u are indeed more than a frnd but sister love u…MY BEST HALIMATU*????????

14

………………..Koda ya Fita Fuu,haka ya Bude motarsa ya fada yana sauke Numfashi,sama sama jingina kansa yayi da jikin kujeran motana yana sakin wani Huci mai zafi,kansa yafarawa shafawa zuwa sumar sajensa,lokaci daya yana tsigen gemunsa wanda ya fara taruwa,duka idanuwansa suna Rufene

Ya dade ahaka kafin ya bude idanuwansa yana cija lips dinshi na kasa,Abunda yafimai bakinciki shine cewar da Abbi yayi wai yaje yabama Malika hakuri? to uwarta yayi mata da zai bata hakuri? Shi ba”a ce ta duka har kasa ta bashi hakuri ba,sai shine za”ace ya bata hakuri,Durun uwa ne ma..? yafada yana sakin wani dogon tsaki kafin ya gyara zamanshi yana kokarin Daura Set belt yake fadi abayyane.

“Zanje dai na taho da ita kamar yadda Abbi ya bukata,ammh mganar bata hakuri wlh Uwarta bata haifeta bama,wacce zan ba hakurin gaskiya..”Yake Fada yana kunna motar nashi Afusace yayi mata kwana kafin ya shiga sakarma megadin hon ba sassautaawa kamar zai cirema mutane kunni,koda ya budemai get din a guje ya Fice yana kara sakarma motar Speend kyace zai tashi sama ne.

Ransa amatukar bace yake kwarara gudu bisa Kwalta,yadda zuciyarsa ke tafasa haka yake tuka motar,cikin abunda baifi awa uku ba,sai gashi yana zuba hon makeken get din gidansu Malika,koda aka wangalemai get din afusace ya danna kai gidan,har yana kusa takema megadin yatsun kafa,da kallon mamaki yabi motar sanda take gyara parking.

Sai da ya daidata kanshi kana ya Fito daga motan,ammh Fuskarsa tamau babu alamun Fara”a ko kadan,Megadin ya, ya Fito da hannu,wanda dama yake tsaye yana kallonshi cike da tsoro,jikinsa na rawa yazo yana Fadin”Brka da zuwa yallabai..”giransa ya hade yana Fadin”Ka shiga ciki kace ana mgana da mai gidan..”Kallon mamaki megadin ya bishi dashi,yana so yace mai ai Alhaji baya da lafiya bai Tafiya yanzu,ammh yanayin Saleem din yasa dole ya Wuce sumu sumu jikinsa na rawa.

Megadi Hajiya binta ya sanarma da sakon,wacce ta kalleshi cike da mamaki tana Fadin”Waye shikuwa..? baisan Alhaji baida lafiya bane..”Yace”ina ga hajiya…!”

Tabe baki tayi tana Fadin”koma waye sanar dashi ya shigo ciki Alhaji baida lafiyan da zai Fito ya sameshi..”Jikinsa na rawa ya Fice da hanzari,koda yazo ya iske saleem jingine jikin motarsa yana faman latse latsen waya,rankwafawa yayi yana Fadin”Yallabai hajiya tace ka shigo ciki,don Alhaji kam bai da lafiyan da zai Fito ya sameka..”Sai alokacin ya tuna ance fa Alhaji Abdulmalik ya samu shanye barin jiki,Basarwa yayi kafin ya wuce kai tsaye bayan ya tusa wayarsa cikin aljihu lokaci daya yana Tura duka hannuwan nasa,cikin aljihun cikin takunsa na isa da takama ya nufi kofar da zata sadashi da babban Falon gidan.

Da sallama ya shiga Falon lokacin da wani sanyi hade da kamshi ya dakeshi,ga taushin wani shigen grass cafet dake malale afalon,Tabe baki yayi yana bin Falon da kallo,nan ya cikaro da taftafkan hotunan Malika akowani kusurwa na bangon Falon,Yatsine yake kallonsu kafin yay tsaki aransa yana kara jin tsanarta,Yana nan tsaye sai yaji motsin Ana saukowa daga saman Bene,Dama aleeady yabama Steps din baya ne,so sai ya waiwayo daidai lokacin da Hajiya binta ta karisa Saukowa,idonta karaf akanshi tana karemai kallo.

Duk da sau daya Tak ta ganshi,ammh ta shaidai shi,shiko ganin yadda ta kureshi da ido ne yasa,ya dan rankwafa yana Fadin”Ina yini hajiya…”Ta amsa da “Lafiya lau,sannu da zuwa,kamar Saleem ko? mijin Malika..”Wani haushine ya kamashi,nan da nan ya hade giransa kafin ya dan saki yake yana Fadin”Eh…”Daga haka ya tsuke bakinsa,yana kallon gefe.

Baki ta washe tana Fadin”Ah!Masha Allah sannu da zuwa yaushe ka dawo,domin kamar naji ana zencen baka kasar ko.? Fuskarsa ba Fara”a yace”Eh wlh jiya na dawo..”Juyawa tayi tana Fadin”Allah sarki,biyo muje Alhajin yana sama ne..”Tafada tana Taka Step,shima ya bi bayanta yana zabgamata harara sai kace ita ta kirashi Dole.

Suna shiga Falon sama,inda Daddy yake zaune kan kekenshi yayi Shuru yana Tunanin Rayuwa,Sai yaji hajiya binta ta Shigo tana Fadin”Alhaji kayi bako..”Waiwayowa yayi yana Fadin”Bako kuma..? Ya fada da sigan Tambaya,Eh tace kafin ta cigaba da cewa”Saleem ne Mijin malika…”Tafada daidai lokacin da yake saka kanshi cikin dakin bayan ya cire takalminsa.

jin Abunda Hajiya binta ta Fadane yasa Daddy ya washe bakinsa duka yana Fadin”Masha Allahu….”Yake Fada sanda Saleem ya kariso  gareshi shikuma ya danna Abun tafiya da keken atare suka tarbi juna,Saleem yayi saurin yin kasa yana bin Daddy da kallo,ganin yadda lokaci daya y koma kamar wanda ya Shekara yana ciwo.

Hannayensu sarke ana juna Daddy yake Fadin”Saleem sannu da zuwa,yaushe ka dawo kasar,don Kumo ya sanar dani daga wajen aikinku an turaka wani karatu ko…”?Kan Saleem na kasa kunya duk ta kamashi,bai taba zaton wannan karban mahaifin Malika zai mai ba,sai gashi yaga sabanin Tunaninshi,Kasa hada ido yayi dashi kansa na kasa ya Furta..”Eh Daddy jiya na dawo..”Daddy yace”Masha Allah,an samo Abunda akaje nema ko..”?Kara sadda kai yayi yana Fadin”Insha Allahu Daddy…”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button