MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL
MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Gyara zama tayi tafara karantamai yadda ta iya,Sai da tagama kana shi ya sake biyamata cikin Taushin murya da kira”a mai dadi,yayi mata gyaran sosai acikin nata karatun,sai da yayita maimatamata kafin yafara karantamata tana amsawa,bai kyaleta ba sai da Fatihan ta zauna bisa kanta sosai,kafin ya karbi Joter din daya bata ya Rubuta mata abunda zata Fada yayinda Sujjuda da Ruku”u da yayin Zaman tahiyan farko data karshe,wato Tahiya da salatin Annabi ya mika mata yana Fadin”Ki rike wannan,kidinga bita har ya zauna miki,zuwa gobe zan fara biya miki kananun Surorin kinji ko..?…
Karba tayi bakinta na motsi bai bari tayi mgana ba,ya mike yana shafa kanshi ya Fada tiolet,Itakuma sai ta samu kanta da bin bayanshi da Kallo kafin ta Furta ahankali”He is so nice…”,Tafada kafin ta mike tana Fadin”Alhamdulillah na samu MALLAM…”Ta fada tana jin dadin Abun har ranta,Jotern tayi ta dubawa tana zaune gefen gado,dayake yayimata Rubutun cikin kalmomin hausa,ammh kuma da Turanci yadda zata gane sosai.
Har yafito tana zaune awajen alwala ya dauro yazo ya Shimfida darduma ya fara shafa’i da Wuturi,tun tana bin karatun har tafara hamma,saboda gajiya batasn sadda ta sulale bisa gefen gadon tana barci ba,shine daya idar da sallahn yazo ya gyaramata kwanciyar ya rufamata blanket,Shikuma bisa sallanyan ya yada Filo ya kwanta bayan ya Tube rigansa dagashi sai dogon wando don baya Hunce gaban yarinya ba ta rainashi,joter nata ya adana mata saman Side drower din gadon,addu”a barci yayi ya kwanta bayan yayi kasa da Hasken dakin ya kunna Dumlight.
WASHE GARI
Yau Saleem bai samu Fita masallaci sallar asuba ba,saboda malika,bayan ya jasu sallar sun idar yayi musu addu”o’i sai ya dauko Qur”aninsa ya biya mata Sura daya,Suratul Nas,yayi ta nanata mata harya zauna mata,sai kuma ya koma kara nanata mata Abunda ya Rubuta mata jiya,shima sai da ya tabbata ta iya wasu,babu laifi ya lura kwakwalwarta naja,tana da sharp brain sosai yarinya,ya yabamata ta wannan bangaren.
Basu tashi daga karatunta ba sai da ya sanar dani yadda addini ya koyar damu mu”amala da mutane,ya sanar da ita babu kyau yima wanda ya girmeka rashin kunya ko mgana gatsal,kana ta koyi mu”amala da mutane da kuma girmama Manya,kuma yana daga cikin al”adun mu na hausa Fulani taimakon manyanmu,da koda munga suna wani aiki,yana daga cikin tarbiya sakaya sunan wanda ya girmeka ko ya kusa haihuwanka koda bai haifeka ba din,Kuma ya sanar da ita babu kyau girman kai,ko izigilanci duka haramun ne,zalunci Allah yahana kanshi kuma muma bayinshi yahanemu da yinshi,daga karshe ya sanar da ita Tayi Istigifari ga laifinta na baya Allah gafirun rahimun ne.
Jinjina kai kawai takeyi tana jin dadin mganarshi,balle yadda yake mata mgana cike da dattako ne da kuma jarumta babu alamun sanayyah kawai yana koyamatane don taimakonta,daganan yace su dakata da karatun sai anjuma da daddare zai dora mata daga Abubuwan da suke wajabta wanka,da kuma shi kanshi wankan..”
Yana kokarin tashi ne ta katseshi ta hanyar cemai ” MALLAM.. Ina da tambaya…? Yajita sarai ammh sai ya barsa wayarsa ya laluba yana kallon lokaci kafin ya waiwayo yana Fadin”Ba sunana Mallam ba,kirani da Saleem dina kai tsaye..”Mirmishi ta sakarmai mai taba zuciya wanda sai da ya tsaya yana kallonta.
Motsa bakinta tayi tana Fadin”Nasani ba sunanka Mallam buh awajen malika kai Malamina ne,wanda yake kokarin tsamoni daga duhu zuwa haske,Ina da mahaifina ammh bai tsaya ya koyar dani yadda zan samu aljannata ba,duk da ban tashi hannun duka iyayena ba,ammh duk da haka bazan ki jinjinama Daddyna ba,domin shi yayi kokarin min gata wajen Tilastani aurenka,Bansan da wani baki zan godemaka ba mallam buh komai miye ina maka fatan Allah ya baka mai saka maka Fiye da yadda kamin..”Tafada hawaye na gangaro mata.
Jikinsa ne yayi sanyi sai yayi saurin komawa ya zauna gabanta yana Fadin”Kin yarda ni malamin ki ne,wanda zai koyar dake hanyar tsira..? gyada mai kai tayi tana sharbe hawaye.,Daure fuska yayi kafin yace”To yazama dole duk Abunda nace kiyi do it ba gardama,? ta gyada kai kawai alamar gamsuwa,jinjina kai yayi kafin yace”Kizama daliba mai biyayyah da niyyar Neman ilimi,kuma mai biyayyah akowani lokaci,sai kiga Allah yabaki nasara kan Abunda kike nema..”
Gyada kai tayi tana Fadin”Insha Allahu mallam,ngd sosai god bless u…”Cije baki yayi yana Fadin”Yi tambayarki,barci ne a idona..? Dukar dakai tayi tana Fadin”Dama game da abubuwan dana aikata abayane,shine nake tambaya,duk Allah zai iya yafemin..? Mikewa yayj tsaye yana gyara zaman jallabiyan jikinsa yake Fadin”Mezai hana,kin manta karatuntunmu,abaya na sanar dake Allah gafirull rahimu ne,so kiyi tuba zuwa garesa tare da Alqawarin da kuma yakinin bazaki koma ga zunubin ki na baya ba,ki kuma yawaita istigafari,Allah shi kuma zai Yafe miki..”Yana gama fadin haka ya haye gado yana lumshe ido,don har ga Allah bayanshi ya gaji da zama.
Itako nan ta zauna tana bitan karatun daya koyamata,sai da tagaji don kanta ta hakuri itama nan bisa sallanyan barci ya kwasheta,bata Farka ba sai da taji Ummi na tashinta,kuma lokacin wani zazzabi mai zafi yagama Rufeta ko iya bude ido batayi saboda zafin jiki,goshinta Ummi ta dafa tana salallami,fita tayi taje ta sanar ma Abbi,shikuma ya kira Saleem wanda already ya dade da Fita
Malika dai ranar haka ta Wuni da zazzabi,Hajiya babba ne tace ita irin cikinta kenan zazzabi da kuma amai domin wunin ranar hararwa tayi tayi kome taci sai ya Fito,dole ta hakura da cin komai,sai da yammah ne Ummi ta mata tuwo miyar kubewa,sai gashi ko taci sosai kuma batayi aman ba,Wuni Ummi tayi ita da Hajiya suna dawainiya da ita,haka Abbi bini bini ya leko yana tambayan ya jikinta,ita dai taga gata a Duniya,sai da wajen yammah ne taji zazzabin ya barta ta Rarrafa tayi wanka,ta sauya kaya tayi sallar mangariba,Sai lokaci Saleem ya dawo daga cikin gari,kuma bai manta ba ya taho mata da Abunda yayi mata alqawari,Qur’ani izu biyu,sai Ahalari,sai Bagadadi,sai bari wa biba,da littafin koyan baki,dana koyan Rubutu duk ya siyo mata,ammh ranar basu samu damar karatu ba,don Tunda takara cin tuwon da Ummi tayi mata tayi ta kelaya Amai,sai kuma zazzabi Daga baya,duk rashin imanin Saleem sai da ya tsausayama malika ganin yadda take bari da jiki saboda zazzabi,sai gashi saboda halin datake ciki bai iya kwana akasan ba,sai bisa gadon ya kwana kusa da ita yana kula da ita,duk da basu hade da juna ba,kowa na gefe,sai dai in yaji tana hada hakora sai ya waiga ya mata sannu,ya maida kai kawai aransa yana ayyana jibi jibin zai koma bakin aiki bazai iya da wahala ba.
Ammh sai me washegari Sai Malika tatashi garas kamar ba ita,sai kuma Aranar ne ta kunna wayarta ta kira Daddyta da hajiya suka gaisa sun dade suna mgana dashi yana ta kara bata hakuri da Umartanta datayi biyayah ga mijinta,ada taso ta sanar dashi tafara zama cikakkiyar mace mai daraja,sai kuma ta fasa ta Fiso ta bashi mamaki ne,har tabama su Ummi waya suka gaisa da hajiya binta cike da fara”a.
Tunda taga ta Samu sauki sai ta dukufa kan duba bitan karatunta Tunda dazu da safe ya bata qur”anin daya siyomata hade da sauran littafan,yanzu surorin dayayi mata take so haddacesu,mganar sallan ta kuwa tuni babu abunda bata gane ba yanzu sai dan Abunda ba”a rasa ba.