MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Zaman shuru ne yayi mata yawa adakin ta tattaro littafanta tafito Filo ta zauna sanye take da riga da wando na pakistan red and black,sai wani red vail data yane kanta dashi gefenta hajiya ce wacce ke zaune tana kallon Tibin dake ta dimi shi kadai,ammh ba fahimta take ba,wani lokacin in malika bata gane wani waje ba, ita take nunawa ta gyaramata ko ta tadata,Hakika Su Ummi sunji dadi domin ko bakomai ilimantar Da mace ma lada ne,balle kuma Abu ne mai kyau miji yadinga karantar da matarshi domin sunnar ma”aiki ne hakan.

Ta dukufa abitar karatunta taji sallama daga saman kanta tana dago kanta suka hada Four eyes da mai kama da Saleem,sak sai dai ita tafishi manyan ido,da Dan kiba kadan, dauke da wata katuwar jaka,irin ta baya din nan,sai katon trolly dinta wanda take jaye dashi,kallon kallon sukama juna kafin saleema ta dauke kai tana yatsina fuska,wajen hajiya ta nufa ta fada jikinta tana fadin”Oyoyo hajiyata i miss u…”

Need ur pryers…????????????

Momyn ladingo????

MALIKA MALIK…!
(Sai na rama..)

ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى ASSɷ????

Mallakar:Janafty????

KURIKE GIRMAN AMANAR DANA BAKU,KUYI MIN ADALCI KAMAR YADDA NAYI MUKU KADA KU FITARMIN DA BUK WAJE DON ALLAH????

  17

………….Rumgumeta hajiya tayi tana Fadin”Kai Saleemata,sannu da zuwa…”

Saleema na dariya tace”Yauwa hajiya,ya gida..? Kewar gida ya dameni sai kuma muka samu dan break shine na taho gida..”

Kafadanta ta dafa tana Fadin”Muna munsha kewarki sosai ma kuwa..”Mirmishi tayi mata tana mikewa daidai lokacin da suka sake hada ido da Malika,wacce tun kallon da Saleema tayi mata taji ta muzanta,Sai ta koma gefe ta rabe,kanta duke ta kurama littafin gabanta ido,kamar tana karatu nan ko, ba karatun take ba,Jikinta duk asanyaye.

Ganin sun kara hada ido ne yasa Malika tace ma Saleema”Ina yini,sannu da zuwa..”Wani dirty look Saleema ta watsa mata kafin kawai ta dauke kai,don ta Shaida ta tantiriyar matar Ya saleem ce,domin Abbi ya sanar da Ya marwan duk Abunda ya Faru,shiko ya sanar ma da  gindin rasit,wato Sadiq,shikuma ya sanarma patner dinshi Saleema,wacce kwata kwata Abun bai mata dadi ba,ita fa bata ga dalilin Abbi na takurama ya saleem kan wata chan banza jinin arna ba.

Ganin yadda tayi mata ne,yasa malika taji idanuwanta sun kawo, ruwa Hajiya ce taga Abunda ya Faru ranta bai mata dadi ba,ta kalli Saleema tana Fadin”Saleema bakiji Matar yayanki na miki sannu da zuwa bane..? Tabe baki tayi tana jan akwatunta take Fadin”Wace…? ta fada tana dan kallonta cike da raini.

Ganin haka yasa Hajiya mika mata dakuwa tana Fadin”Uwarki ce..”Baki ta tura kafin tayi gaba tana Fadin”Au kefa hajiya,baki ma mutun kawaichin marmari wlh..”Tafada ranta bace,ganin an zageta kan wata banza.

Da Ummi taci karo ta Fito daga kichen,Rumgumeta tayi tana Fadin”I miss u my Ummi..”Shafa kumatunta Ummi tayi tana Fadin”Likita na wasa da karatunta ko? baki da aiki sai tahowa gida..”Dan dira kafa tafarayi tana Fadin”Kai Ummi break fa muka samu na one week,kuma nayi kewaeku ne,shiyasa nazo ganinku..”Sakinta Ummi tayi tana Fadin”naga alama,toh baki tsayawa chan kiyi karatu? .

Tura baki tayi tana Fadin”,Kai Ummi,ga kayan karatuna na nan cike da jaka,..”Dariya Ummi tayi mata tana Fadin”Uwar zence,kinganki Saleema bamai kadake azence..”,Itama dariyan ta kyalkalyalace dash tana Nufar hanyan dakinta tana Fadin”Kai Ummi,me kike dafa na mana ne..?

Shiga kigani..”Ummi ta bata amsa,Yar dariya tayi tana Fadin”Wai ni banga Abbi ba,kuma banga Malalacin Acp ba..? Tsaki Ummi taja tana Fadin”ke wai bana rabaki da sha”anin saleem bako.? Sun fita shida Abbi..”Dariya Saleema tayi tana

Fadin”Kai Ummi bafa ni na sakamai sunan ba hajiya ce gatan chan..”Tafada tana nuna hajiya.

Hajiya ko datake da cikinta na Abunda tayima malika,kyabe baki tayi tana Fadin”Kwarai ni na samai sunan,ammh sai na kirasa ya amsa don dole,kuma koda yaji haushi ban dakuwa,ke kuwa wlh kika kirasa da wannan sunan dakaina zan umarceshi daya nada miki na jaki Tunda baki da mutumci..”Tafada tana kumfar baki,Bude baki Saleema tayi kafin ta kada ta Wuce dakinta tana Fadin”Tabdijam,gamdamemiyar budurwan,da sake kam..”Tafada tana Shigewa dakinta dake yammah da na hajiya.

  Malika ko na jinsu duk Abunda ke Faruwa ammh kanta na duke takasa dago kanta,Hajiya ce ta kira sunanta tana Fadin”Malika kiyi hakuri kinji ko? ahankali zaku saba da ita,ita kebima saleem..”Mirmishin yake tayima Hajiya tana Fadin “Babu komai..”Tafada tana kokarin maida hawayenta,kara sunkuyar dakai tayi tana Tunanin rayuwarta abaya ta tabbata da adane da kudi aka hada Saleema akace tayi mata Abunda tayi mata bazata taba yi ba,ke ko kusa da ita wlh bazata iya zuwa ba,ammh gashi yanayin rayuwa ya chanza da ita,har ana mata duk cin kashin da”aka ga dama Ammh babu komai tayi niyyar Tuba ga Allah kuma bazata koma ga halayyyata ta baya ba.

Tashi tayi ta tatarra littafanta takoma daki ta kwanta bisa gado tana kuka,saboda takasa rike zuciyarta waje daya tsausayin kanta duk ya lullubeta,sai da tayi kuka ya isheta kafin ta mike ta fada tiolet ta dauro alwala tazo tayi sallar azahar,Bata son sake Fita taje su hadu da Saleema ta kara Wulakanta ta,shiyasa tayi zamanta adaki tana cigaba da duba littafanta,.

Har akayi sallar mangariba Bata fito ba,sai da Ummi taji ta Shuru ne ta Shigo har dakin ta isketa saman darduma tana duba karatunta,Har ga Allah Abun Nama Ummi dadi ganin yadda malika take maida hankali wajen koyon ilimin addini,Gefen gadon ta zauna tana Fadin”Dota Anata karatun ne..? Gyada mata kai tayi tana Fadin”Eh Ummi sannu da aiki..”amsa mata tayi da kai tana Fadin”Yayi kyau in kingama ki Fito Falo,yau mu taru muyi Dinner kinji..”Gyada mata kai tayi kafin tace”Toh Ummi..”Tashi tayi ta Fice ta barta nan tana cigaba da karatunta.

Koda Malika ta Fito babu kowa cikin Falon sai Ummi dake kwaso kololin abinci ,tana ganin haka ta isa gareta Da Sauri tana Fadin”Sannu da aiki Ummi..”

Tafada tana karban kololin ahannunta,sakarmata Ummi tayi tana Fadin”In kin kai wannan maza kije ki zauna kinga baki da lafiya kinji ko? mirmishi kawai tayi tana Fadin”La wlh Ummi naji sauki bakima gani Ba..”Tafada suna karisawa bisa Dinining din,duk yadda Ummi taso tahana Malika kin hanuwa tayi,tare suka Jera komai,sai alokacin Saleema ta Fito daga daki,cikin riga da sikat,Wayace ahannunta tana latsawa kallo daya tayima su Ummi da malika ta dauke tana tabe baki

Ummi ce tace”Sarkin waya,sai yanzu kika Fito na shiga naga kina wayarki na fama..”Ashagwabe Saleema tace”Kai Ummi,ni fa da ya sadiq ne..”Tafada tana zama bisa daya daga cikin kujerun Falon,tana dariya,Kafin Ummi tayi mgana sai  gaAbbi yayi sallama yana sawo kai falon,bayanshi kuma Saleem ne yana sanye da wata danyar gezner Light blue,wacce taji kyau dinkin muhammed,da hulansa zanna bukar,kayan su matukar amsanshi fuskarshi babu alamar fara”a ko kadan,sai dai bai tamketa sosai ba.

Da Gudu Saleema tatafi gareshi ta fadamai tana mai sannu da zuwa,Riketa yayi yana tambayanta yaushe ta dawo,tace dazu ba dadewa Saleem dake bayan Abbi hankalinshi na bisa waya yaji saleema ta fadomai tana fadin”Mai girma Acp.”Ta fada tana Rumgumosa.

Wayarsa ya maida aljihun yakama kunnan Saleema ya murde yana Fadin”Ke wai bakison karatu ko? baki da aiki sai guduwa gida,Allah sa wannan Semister akori wlh..”tanajin haka ta sakeshi tayi baya tana diddira kafa sai kuka tana Fadin”Wlh Ta Allah bataka ba,Abbi kaga ya saleem ko? wai za”a koreni daga faculty mu..?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button