MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Adan kaikaice yabi bayan Saleem da kallo,Ransa ya baci da Abunda Saleema tayi mishi,yanzu ko bashi ba,ko malika ai ba sa”arta bace kuma a al”adance tana mtsayin Antintane,ammh saboda ta rainashi shi takema tsaki,Tunda ni sa”anta ne,bai yi yunkura binta ba ya kada kai yabi hanyar dakinshi yana cije baki.

Malika bata bi bayanshi ba,sai da taya Ummi suka maida Kayan da suka bata zuwa kichen,Ummi taso ta hana Malika wanke wanke,ammh taki,tace sai tayi hakan ta barta suka wanke tare,sunayi suna hira,Ummi na kara mata nasihan hakuri da rayuwa,da kuma hakuri da biyayyah da mijinta,sannan Ummi ta roketa alfarma kada bayan sun koma zamfara ta yada karatun data fara koya,tace zata sanar da Saleem yasata a mkranta islamiya na matan aure,wanda zai taimakamata sosai..

Hakika taji dadin Nasihan Ummi da shawaranta,ita kuma tayi mata alqawari zata sameta mai Bin umarninta,Ummi ma taji dadi tayi ta sakamata albarka,wanda Malika taji dadi harda kwallah,saboda Farinciki don bata taba samun saka albarka daga wani ba,bayan Daddynta,sai gashi Ummi na sakamata haka Abbi,ai ita babu Abunda zatace da Ahalin Kabir kumo,sai godiya da Fatan alheri.

  Koda ta koma dakin ta iske Saleem kwance ya juya baya yana kallon bango,wayarsa kuma sai daukan Tsuwa take,ammh sai ya dinga saka hannun yana latsewa,ganin bai mata mgana ba yasa ta fada tiolet ta wanke baki kafin Ta fito,wajen akwatun nanta ta isa,tana kokarin budewa taji yana Fadin”Meyasa kika ce zaki bini..?baki tsoron irin zaman da zai gudana tsakani na dake..? Waigowa tayi tana kallonshi sai taga baima juyowa ba, Fuskarsa tana kallon bangon dakin kamar ba shine bane,yayi mgana.

  Bayanshi ta kurama ido,tana jin wani sanyi na Shiganta,Kasa mgana tayi illah kuramai ido kawai datayi,bata ankara ba taga ya juyo yana mikewa zaune bayan ya jingina bayanshi da gado,ido ya zubamata yana kallonta,kunya ne ya kamata sai kawai ta duka tana kokarin bude akwatinta taji yace”Ina tambayarki baki bani amsa ba,kuma kin tsaya kina kallona..,?”Ya Furta yana harde hannuwanshi akan kirjinsa..

Tana duke tace mai”Armmm me kace..? Wani kallo yayi mata kafin yace”Bansani ba kina nufin bakiji ni ba,bansan rainin wayau fa..?yafada muryansa acunkushe,diridiri tayi tana kallonshi Shiko ya sakarmata idanuwansa kamar zai daketa dasu,Sunkuyar dakai tayi tana Fadin”Kawai bani so kamin nisa ne..”Ware ido yayi yana Fadin”Really…? Saboda mene..?

Kanta na duke tace”Saboda bani son karatun dana fara ya tsaya ne..”Yamutsa Fuska yayi yana Latsa wayarsa datake ta neman Dauki,yana sakin wani kafirin mirmishi,yace”Ba gaskiya bane,ko bani ba akwai masu koya miki karatu,baga Ummi ba ga kuma hajiya ko Saleema,duk wanda kika ma mgana zai koyamiki..”Idanuwanta ne suka ciko da kwalla,sai kawai tajuyamai baya tana share hanci.

Mikewa yayi yana Fadin”Kinsan wani Abunda baki sani ba game dani? na tsani muna mgana da mutum ya juyamin baya,ko kuma yayimin tsaki? i hate does wlh..”Yafada yana daga kiran dake shigowa wayarsa bayan ya Fice daga dakin.

Ajiyar zuciya ta sauke tana bin bayanshi da kallo,agurguje ta saka rigar barcinta,doguwar rigace mai kalan ja da fari,hijabinta ta saka ta haye gado,ta lafe gefen datake kwanciya,Tun tana sa ran dawowarshu har wani barci mai dadi ya kwasheta bata farka ba,sai da taji yana tashinta da asuba,lokacin ma harma yayi alwala Sanye da jallabiya,yace tatashi tayi sallah ta shirya yana dawowa masallaci zasu Wuce.

Wanka tayi kafin ta dauro alwala,sai da tayi sallah kafin ta shirya cikin wani riga da Sikat,Rigar Farace da digon baki,sai sikat din na roba ne baki,yana da budewa daga kasa,sai vail dinta baki wanda ta yane kanta dashi bayan ta daure gashinta da band,Tana cikin sanya takalminta ne ya Shigo dakin,tana ganinshi ta rankafa tana fadin”Gud mrnig mallam..”

Mrning..”Kawai yace yana kallonta kasa,,kasa,kafin yace mata”Baki da wani kayane sai wadannan..”tana durkushen tace”Eh..”karamin tsaki yaja yana Fadin”Ok,.Kada ki dauki kayan duka juz akwatu daya ya isa,munje chan zansa adinka miki kayan mata mai mutumci..”Gyada kai tayi kafin tace”Tanque..”Bai amsa mata ya shige tiolet,ita kuma ta mike tana hada kayanta akaramin akwatunta guda daya.

Baijima ba ya Fito daure da babban Towel,kirjinsa na Fitar da maikon Ruwa kallo daya tayimai taji gabanta ya fadi,saurin dukar dakai tayi tana jin wani sanyi sanyi na Shiganta,bata jira komai ta Fice daga dakin kamar zata kifa saboda yadda jikinta ke rawa,da irin kallon da Saleem yake binta dashi,batasan dalili ba,ammh da zarar ya samata ido,shikenan sai taji tana neman rasa natsuwarta.

Tana Fitowa Falo babu kowa,kichen ta Shiga,nan babu kowa Ummi bata riga ta Fito ba,kila yau bata da zuwa aiki da wuri ne,dakin hajiya ta wuce suka gaisa,ta sanar da ita zasu tafi,tamata Fatan Allah ya tsare hanya,Sai da ta Fiti daga dakin Hajiya kana taga Ummi ta Fito,tana kokarin hada breafsat,gaisawa sukayi cikin girmawa,Fere dankali Ummi keyi Malika ta kariso zata karba,Ummi taki bata tace tabari kawai kada ta bata kyanta,suna cikin hakane sai ga Saleem ya leko yana Gaishe da Ummi,gabadayansu suka waigo,yana sanye da Suit Red and black,ya daure wuyanshi da bakin Tie,jakar brief case dinsa ne sagale akafadanshi yana duba agogon Fatan dake hannunshi ne yake cema Ummi..

“Ummi zamu wuce,ina da Meeting 12..”Wukar Fera dankalin ta ijiye tana Fadin”Da wuri haka saleem…? Fita yayi daga kichen din yana Fadin”,Eh Ummi,bari nayi ma Abbi sallama,Ke dauko kayanki ki Fito mana..”Yafada yana haurawa sama,Ummi tace”Maza kije ki dauko kayanki,Saleem bayason jira..”Jikinta asanyaye Ta koma dakin ta jawo karamar akwatunta tana kallon dakin cikin kewa,littafanta ta manta da hanzari,ta Daukosu ta saka cikin aljihun akwatun ta Fito,koda ta Fito Abbi da saleem sun Sauko kasa, har kasa ta duka ta gaishe da Abbi ya amsa yana tambayanta jikinta,ita kuma Ummi kichen takoma da hanzari ta Daukoma Malika Dambun nama dayawa cikin wata katuwar roba,ta damkamata karba tayi tana ta godiya,A gurguje Saleem ya Shiga bangaren hajiya suka yi sallama har bakin mota suka rakasu suna saka musu albarka,sai da motarsu ta fita daga gidan kana suka koma cikin gida cike da kewa.

  ***

  Wurgi tayi da wayar bisa gado,tana zuba tagumi hannu bibbiyu,Nadira dake gefe tana kwance Ruf da ciki tana Danne danne bisa system dinta ta dago tana kallon Zahra take Fadin”Wht happend best..? Hawaye ne suka cikamata ido,ta girgiza kai tana Fadin”Best baya picking call dina,Tun Shekaranjiya nake kiranshi yana yankemin kira..”Tafada hawayen na zubomata.

Ture laptop din tayi ta mike zaune tana Fadin”Shine ya isa ya sakaki kuka..?Kara Narke baki tayi tana Fadin”Haba best,do u know how much i luv him? wlh inajin in ban aureshi ba zan iya mutuwa..?Tafada wasu hawayen nakara zubowa mata.

  Cike da mamakinta ta karisa gareta tana Rike hannuwanta take Fadin”Kinga srry inaga baya kusa ne,kimai uzuri kibar kiransa har zuwa gobe,in bai kira ba,ni zan nemasa ta wayata,kinji..? Kan jikinta ta kwanto tana Digan hawaye tace”Sai dai gobe ki kirasa,saboda bazan iya jurewa ba har nan da wasu Awanni ba..’Kanta ta Shafa tana Fadin”Ok don’t wrry i will try my best,kibar kukan hakanan,yans tabamin rai kinsani..”Tafada tana dagota ta share mata kwallah tana Fadin”Oya smile..”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button