MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Koda ya koma gida,gim da rai yayima malika,yana ijemata takeaway dinta ya Shige daki,ya kulle koda tazo da littafan karatunta taji kofarshi akulle,sai kuma taji jikinta yayi mata sanyi Ranar dukkansu ba wanda yayi barci,shi yana Mukurkusun Ciwon mara da fama da sha’awarta,ita kuma tana juye juyen damuwar da Saleem yake ciki,kwata kwata hankalinta yaki kwanciya,Har da safe ma daya Fito data gaisheshi dakyar ya amsa yana wani cin mgani,Tana so ta sanar dashi Abunda yafaru a asibiti ammh kuma tana jin tsoro,shine da kanshi ya tambayeta,cikin faduwar gaba ta sanar dashi,Harara ya zabgamata yana mata fadan meyasa bata kirasa ta gayamsa ba..? saboda ta rainashi ko? toh in tagaji da zama dashi ne,toh shima ya gaji zai maidata wajen mahaifinta bazai iya karban amanar ba,ta inda yake shiga batanan yake Fita ba,Zuru tayi tana digan hawaye,hakuri takeson bashi,ammh ganin yana cikin zafi shiyasa ta kyaleshi har ya Fice daga gidan yana ta bata rai,shiko aranshi baijin dadin Abunda yake mata,ammh haushin shi daya shine ita tajamai yake kwana yana Fama da tamkewar mara,shiyasa sai ya sauke komai akanta,Kuma Abun takaichi sai yayi mata fada,yakoma yana Fama da damuwa,duk da bazai iya bata hakuri ba,ammh babban Abunda ke dafamai zuciya shine Kukan Malika.,Kukanta na bala’in dagamai hankali barin ma ta kalleshi tana share hawayen,sai yaji jikinsa yayi sanyi kamar ya Rumgumota yayi ta lallashinta,ammh jin kai yahanashi.

Ina godiya sosai da addu’o’inku ga Mama,Allah ya saka muku da alheri….

Momyn ladingo ce

MALIKA MALIK…!
(Sai na rama..)

ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى ASSɷ????

Mallakar:Janafty????

MALIKA MALIK..,Mallakina ne Halak malak ni Janafty ba mallakin Wani ba,so kudin karatu kuka biya bana Mallaka Ba,ni nake da hakki sarrafa buk dina yadda naga dama,Littafi bazai zama mallakinki a #200 kachal ba,Inhar zakuyi ma kanku Adalci..BAZAN GAJI DA MAIMATA KALMAR KURIKEMIN AMANABA KADA KU FITARMIN DA BUK WAJE DON ALLAH????????

19

————————“Har Weeked din tazagayo Saleem bai sakarma Malika ba,Kullum Fuskarshi ba Fara”a,Karatunta kadai yake kokarin yimata shima ba cikin dadin rai ba,kamar yadda ya saba ba,Shiyasa duk karatun ya Fita akanta,Damuwa tayi mata yawa kuma bata da wanda zata Fadamawa,sai Allah shi kadai take kaima kukanta dayayi mata mganin Abunda ke damunta.

Daga wannan Fushin rashin dalilin da Saleem ya hauta dashi Ta fahimci ta fada tarkon sonshi mai tsanani,Domin ta azabtu sosai,ashe koda baya mata mgana sosai,Fuskarshi dayake sakar mata ma kadai Tana sata nishadi,ammh da zarar ya bata rai Shikenan itama zata Shiga damuwa,balle wannan karon da Fushin nashi ya tsauri dayawa ne ta rasa ina zata saka kanta taji dadi….

Yau ta kama Lahadi ne,Tun safe ya Shirya cikin wata dakakkiyar Shadda Navy blue,mai maiko da yarari tana Falo tana gyarawa ya Fito daga dakinshi yana daura agogon hannunshi,da ganin yadda yake komai cikin hanzari zaka Fahimci sauri yake,ganin Fitowarshi yasa ta rankwafa tana gaisheshi akufule ya amsa kafin ya dago kanshi yana kallonta kanta na duke kasa,tana wasa da Kwalliyan hannun Bakar Doguwar rigar dake jikinta.

ido ya samata kawai yana kallonta,cike da mamakin ganin yadda tayimai rama ido,Gyara tsayuwa yayi kafin yadan yi gyaran murya yana Fadin”Armm nace ba..”Dagowa tayi cikin tsoro da mamaki tace”Na”am me kace..? Kur yayi mata da manyan idanuwanshi yana wani shafa gemunsa da hannunsa guda,saurin kauda kai tayi jikinta yakama bari haka kurum,yana lura da ita,kawai sai ya barsa yace”Zan yi Doguwar tafiya yau,bansan ya zamuyi da abincinki ba..”Yafada yana kara gyara zaman rigar jikinsa.

Kanta na kasa tace”Ba damuwa akwai sauran Fura jiya,kuma maman Abba ta kawomin Faten wake jiya,toh banci ba,sai naci shi yau..”Bai damu ba kawai ya tabe baki ya Wuce yana wasa da makullin motar dake hannunshi yana Fadin”Ok sai na dawo..”Mikewa tayi tana bin bayanshi da kallo cike da sha’awa murya chan kasan makoshi ta Furta”Adawo lafiya Allah ya tsare..”Addu”arta tamai dadi sosai har sai da ya waigo yana kallonta,ita kuma tayi saurin Kauda kai,tana cigaba da kakkabe kujera,Mirmishi yayi yana kallon cikinta wanda ya tasa,kafin ya kada kai ya juya yana Fadin”Nagode da adduanki..”Ya furta cikin muryan kulawa da jin dadi,Kafin ya Fice da sassafa yana takunsa na isa da takama mai cike da jarumta.

Sai da ta tabbatar daya Fice kafin ta koma bisa cafet din Falo tayi zaman dirshan hannuwanta dafe da kirji tana dan ware ido kafin ta bude Lebe kamar tana kwakwaiyon mgana ta furta..Nagode da addu’anki..……” Tafada tana Wani lumshe ido,kamkame jikinta tayi tana dariyan jin dadi,cikin jikinta tabi da kallo kafin ta kuramai ido tana shafashi take fadin”Boy katayani murna Abbanka ya yafemin laifina,har yayimin mirmishinsa din nan,mai tsada kuma yayimin godiya..”Tafada tana bayyanar da jin dadinta,ganin babu mai bata amsa yasa ta rarrafa tatashi ta cigaba da Abunda takeyi,ammh ranta fes,gefe daya kuma yau Saleem din yafi koyaushe yimata kyau,don ta yaba da wankan sosai,sai kuma ta Fahimci cewa kamar in yasa manya kaya yafimasa kyau sosai,barin ma ya karya hulan nan nasa,wayyo kamar taje ta Rumgumeshi ta lasan mai baki haka takeji.


Sai da ya Shiga cikin kano kana ya kira Zahra ya fadamata gashi a kano,kinga zahra kamar kanta zai Fado kasa saboda zumudi,dama already Tun jiya da sukayi waya ya sanar da ita yau din yana tafe,so Tun safe gidan ya rikice da hidiman taron bakon Zahra,wacce takejin kamar ta bude ido ta ganta agaban Saleem.

Hajiya saratu wacce suke kira Momi itama Zahra har mamaki take bata ganin barin jikin Datakeyi,har sai da tayimata fadan saura in saurayin yazo karta kama kanta Tunda ta riga tasan halin kayanta,Mirmishi kawai Zahra tayi aranta tana Fadin”Momi bata san so ba..”Koda Saleem ya kira Yace gashi ya shigo kano sun riga sun kamallah komai har zahra ta buga wanka da kwalliya cikin wata dakakkiyar Shadda mai ruwan orange,ammh light dinta dinkin Riga da zani ne,Tayi daurin ta wanda ya Fitar da gashinta wanda ta daureshi da band daga baya,Fuskarta cikin Simple make up,wanda Nadira ta bata lokacinta wajen tsansara mata ita,abinci ko basu san adadin kala nawa suka girkamai ba,balle ababen sha da suma babu kalan wanda ba”ayimai ba,ga kuma surkin irin na kwali ma”ana na bature

Kai tsaye Zahra ta sanar dashi ya tambayi Anguwan GRA,in yazonan ya Tambayi gidan tsohon alkalin alkalai Bukar mada,za”a nuna masa,haka ko akayi dayake gidan ba batattace bane,bai sha wahala ba,sai gashi ya faka motarshi kirar 4matic acikin kayatattacen haraban gidansu zahra,Koda ya Fito daga motan ya hankalce yake bin gidan da kallo yana Dan tabe baki,Megadi ne ya kariso da hanzari ya rankwafa yana gaisheshi ya amsa daidai yana kiran zahra,sanda ta Dauki wayan yake sanar da ita gashi aharaban Gidansu ta Fito.

Tsalle ta buga tana dafe kirji bakinta yaki Rifuwa,zaman mayafin jikinta Nadira ta gyara mata tana kara Fesa mata Turare take Fadin”Oy act very well best,nasanki banda rawan jikin nan,naki da kuma shegen kanki dabaya zama waje daya.”Tafada tana dunguremata kai,dariya tayi tana Ficewa cikin wani taku,kafarta sanye cikin wani ubansu takalmi mai dan Tudu ammh ba sosai..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button