MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Ammh ta hanyar nuna min kauna da soyayyarku wajen Siyan MALIKA MALIK Akan Naira 200 kachal????,ta wannan account Nombar, *0552179550 JAMILA UMAR GTB,sai ki Turo Shaidan biya ta wannan nombar *09069067488* ko kuma katin waya na MTN,shima sai ki Dauki hoton katin aturo kai tsaye ta wannan Nombar 09069067488 Sai kun zo ina maraba daku masoyana..

Karku manta da garabasanmu mai son Siyan Biyu KISHIN MATA,na HAFNAN,300 ne kachal????shima zai iya Turo ta nombar bankin dana bada ko katin waya na MTN ta nombar saman dana bada, ko kuma kai tsaye ku Tuntubemu ta wadannan Nombobin domin karin bayani

07065481260..Ko kuma 09069067488

JANAFTY

  ????MALIKA MALIK????..!
(Sai na rama..)

ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى ASSɷ????

Mallakar:Janafty????

3

KANO

MALLAM AMINU INTERNATIONAL AIRPORT KANO

“””Jirgin karfe 12:00pm shine ya sauke mutanen daya dauko daga birin London

Acikin jerin mutane na 8 masu Fitowa MALIKA tana daya daga ciki bayanta kuma Amintattun Excorts dinta ne joy and peter,sanye cikin bakaken court kowanne ya toshe bakar Fuskarsa da wani makeken bakin gilas,Joy shike rike da Brief case dinta,wanda manyan bayanai game da document na kamfafonin mahaifinta ke ciki,ma”ana kowani Kundin bayanai,Shiko peter dama kullum dan Rike jaka ne da wayoyi dama aikinsa kenan.

Yau din ma tana sanye ne cikin shigarta,buh na yau Suit tasaka na mata riga da sikat,Ash and white,wanda sikat din,da kadan ya wucemata gwiwa,Fararen kafafunta kal,duk suna waje bayan ta kawata kafarta da wani Ash din cover,wanda yake da dan Dudu,Yau anci sa”a bayan ta dane gashinta atsakiyar kanta ta Makaleshi da band,tasaki jelan ta baya,sai ta dora wani ash din vail,ta yaneshi daga tsakiyar kan,Fuskarta sanye da wani glass,mai duhu wanda ko kwayan idonta baka iya hangowa.

Farace Tar sosai,irin Farin ne bamai launin jaja ba,Doguwa ce ammh ba sosai ba,Allah yabata wani Abu waishi tsarin hip,ga kuma madaran shanu suma babu laifi,daga tsayenta tana da Shape din,cocacola ne,Hancinta ba dogo bane sosai,ammh yadace da Doguwar Fuskarta,mai dauke da karamin bakinta,wanda yake Fari tas,shima Gashin idonta zarazara ne kamar yadda idanuwan nata keda girma,Gashin giranta ko baki silif,yana ta Sheke,.

kallo daya zakamata Kazata wannan bata hada komai da Hausa Fulani ba,kai infact ma, zaka zata irin bakin nan,ne dake Shigowa Nageria harkan kasuwanci ,daga yanayin dresssing dinta da yanayin yadda take mgana zaka  Shaida tabbas wannan ko Aturawan takai makura.

MALIKA MALIK..” Kenan Y’a kwaya daya Tak,ga ALHAJI ABDULMALIK DAN KASUWA Wanda saboda kudinsa da tarin kaddarorinsa da kamfafononi,tundaga gida Nageria har zuwa kashashen ketare,yasa ya zamanto cikin jerin masu kudi na hudu A kasarmu ta Nageria.

Tana Saukowa daga kan Step din jirgin Tuni dama motocinta tare da Sauran Excort dinta sun zo daukanta,Duka motocin wannan karan 4matic ne,kuma 12 ne,kowane akwai tambarin MALIKA MALIK1 har zuwa 12 akallah excorts dinta masu tsaronta zasu kai su ashirin,kuma babu dan musulmi ko daya kuma babu jinsi mace,duka mazane kuma wasu gardawa konace samudawa,Tunkafin ta kariso suka bude mata Daya daga cikin motocin,ta Fada cikin isa da takama,nan da nan kowa yakoma motarsa suka bata Wuta sukabar Aiport din aguje,babu wanda ya damu domin indai malika malik ne kaf Nageria,yaro da babba babu wanda baisanta a Talabejin ba,in ma Mutum baita ganinta ba,to babu Shakka yasan lbrin sangarta tare da lalacewa ta malik malik,da sunan wayewa ko kuma nace GATA.


KATSINA

GRA..

Cikin Gra ne Tamkamemen gidan mahaifinta yake,mai kama da yanki Guda saboda girmansa da kuma Fadinsa,inda za”ayi Estete,tsab za”a iya yin guda 40 kuma kowanne da girmansa,Hon suka zuba masu gadin dake sanye da Uniform sukazo suka budemata don sunsan hali,minti daya suka kara korace Awajenta.

lokacin da motocin suka Fara sulalawa parking space,kowani Excort ya fito daga motarshi yana bin motarta da gudu bata tsaya ba,sai A babbar kofar da zata sadata da cikin babban Falonsu,Budemata sukayi jikinsu na Rawa masu,gadin kuwa fadi suke”Wlcm back madam…”cikin isa ta zuro kafarta waje kafin ta bayyana waje Fuskarta babu Fara”a  ko kadan bata kallesu ba,kawai tafara Tafiya joy da peter suka take mata baya,ajiyar zuciya sauran suka saukesu,suna Fatan yasa anrabu lafiya kenan.

Tana Shiga Falon wanda ya kawatu dawasu royal chairs hadaddu masu kyau da tsari sai wani tamkamemen plasma,daya kusa cinye rabin bangon dakin,ko sallama batayi kamar ba,don ba dabi”arta bace, HAJIYA BINTA ,Dake zaune tana kallon Atashar Arewa24 ta dago tana kallon Malika wacce ko kallonta batayi ba,saima zuwa datayi ta gabanta zata Wuce,tasa Tudun takalminta ta murje mata kafa,Azaban da Hajiya binta taji ne yasa ta saka ihu,wanda ya Fito da Alhaji maleek da hanzari wanda ke kayatattacen Falonsa na sama yana hutawa,Dattijone don zai iya kai shekara 67 aduniya Abun mamaki baki ne silif,ammh kuma yana da kyau  da hanci,Fuskarsa tacika da Farin gemu ammh kana kallonsa zaka Fahimci Farin gemun na halitta ne ba wai na Tsufa bane,domin duk inda jin dadi da Hutu yake toh Alhaji Malek na tare dashi,don Shida iyalansa basayin wata Daya A nageria sai Sun Fita waje sun Huta.

Ihun Hajiyane yafito dashi yaga ko lafiya,ammh sai ya ci karo da Malika tana kokarin karisowa gareshi da hanzari ya tafi gareta yana Fadin”Wlcm back my Sweetbbby….”Yake Fada yana Rumgumeta matseshi tayi tana Fadin”Dddylove i really miss u…”Kiss yayimata agoshi yana Fadin”Miss u more Sweetbby,yanzu mrs Suzan takirani tace komai yayi daidai..”

Wani mirmishi tayimai Tana Fadin”U know me Daddy,bazan taba baka kunya.”Wata Dariya yasa yana Fadin”Hhhh..Datz my Sweetbby,maza ki wuce daki kiyi wanka ki Shirya ki sauko muyi lunch..”Tabe baki tayi kafin ta cire glass din idonta tana Fadin”No not now, Daddy naci abinci a cikin jirgi,but now zan Shiga in huta sai na Fito we tok later..”Shafa kanta yayi yana Fadin”ok maza my Sweetbby ahuta lafiya karki sake kitashi sai around 6 haka kinji..?”Kai tadagamai tana bashi kiss a kumatu tace”Daz why i love u,my Daddylove much wlh..”dariya yayi kafin Shima ya maidamata da kiss din,da hanzari Ta nufi wani Daki dake kusa da Inda Abbanta ya Fito tana Shiga dakin su peter suka rufamata baya.

Alhaji Malik ya kalli Hajiya binta yana Fadin”Lafiyanki kuwa naji ihunki daga sama…? dagowa tayi daga murza kafarta, datakeyi Yar matashiyar matace wacce ashekaru bazata gaza 36 aduniya ba,farace tas,ammh tana dan jiki,idonta cike da kwallah tace.

“Haba Alhaji,malika ce fa tashigo babu ko sallama kamar ba yar musulma ba,kuma don rashin kunya tabiyo tagabana zata wuce hakan bai isheta ba,sai da ta takani da Katon takalminta mai Tsini..”Tafada cikin takaichi.

Tsaki Yaja yana Fadin”Gaskiya Binta fitinarki da tseguminki yafara isata fa,Haba kin sakama yarinyarnan ido,ita da gidan Ubanta in bataji dadi anan ba,waje kikeso taje taji dadi ehe..”?Yafada yana tsareta da ido.

Kallonsa tayi baki bude tana Fadin”Ammh tsakani ga Allah Alhaji Abunda Malika tayi yanzu ya kyautu..?”Hannu ya dagamata yana Fadin”Kinga Binta kifita daga idona indai akan Malika ne,banda Abunki nawa malika take,haryanzu fa yarinyace wani Abun sai ana nusar da ita,kuma kibar wannan mganar kada ki kuskura ki tankamata,yanzu nan sai takama Fushi,kuma kinfi kowa sanin yadda Fushin malika yake awajena Atoh.”Yafada irin Abun ya isheshi haka,ya sa kai yakoma cikin kayatattacen Falonsa bayan ya saki Siririn tsaki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button