MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Koda Marwan ya kira Abbi,bayan sun gaisa yake sanar dashi Abunda Saleem ya gayamai,Mirmishinsu na manya Abbi yayi kafin yace”Rabu dashi Marwan,Yarinta da Shirme na damun kaninka,Nayi alqawarin bayan na shiga mganar auren nan daya dauko zan zare hannuna a sha”anin Rayuwar Saleem,saboda naga kamar ni na zama mai Takura gareshi..”Jin haka yasa Ya Marwan ya dinga ba Abbi baki,ammh yace shifa ya riga ya rantse so kawai yama barma mganar,dole ya hakura domin yafi kowa sanin Abbi kaifi daya ne.

Mganar da Abbi ya sanar dashi ya tabbata domin Ranar sati,da daddare bayan sungama karatu da malika sai ga wayar Zahra,nan take sanar dashi dazu su Abbinshi suka bar gidansu,kuma ma wani karin albishir an sanya musu ranar aure wata biyu masu zuwa,mganar tazomai abazata,haka yayi tagumi rike da waya yana jin zahra kamar ya fashe da kuka,Zuciyarsa bata karkata da Abbi ko Ummi, ba tafi karkata ga Malika tana tambayanshi anya ko yayi mata adalci Abunda yake Shirin aikatawa,duba da Halin data ke ciki,cikinta ya Fito sosai dayake tana da girman ciki,yanzu kawai ya sanar da ita zai kara aure ya zataji..”? Kawai zuciyarsa takasa natsuwa waje daya,duk sai yaji Danasanin biyema Zahra ma dayayi balle har yaje gidansu.

Zuciyarsa taki bashi karfin gwiwan sanar da Malika Abunda ke Faruwa,sai kawai ya share zuwa gaba ya sanar da ita,Sati daya da saka Ranar Ummi ta kirata da yammah,ranar ko ta koma awo,tadawo agajiya tana kwance kan kujera tana maida Numfashi,Bayan sun gaisa Ta tambayeta jikinta ne,tace mata da sauki yanzu tadawo daga asibiti,sai Ummi ta fara mata Nasiha da zaman hakuri kafin ta gangaro tana sanar da ita sai ta kauda ido game da Saleem da sabuwar amaryanshi duk da batasan ina zai ijeta ba..”

Tana kwance ne sai da ta zabura ta mike zaune tana Dafe kirji cikin Fitan hayyaci,Tama kasa cema Ummi komai kawai idanuwantane suka ciko da kwallah tana girmama girman tsanar da Saleem yayimata,ashe duk hasashen datakeyi gaskiya ne ya rataye tane saboda amanar mahaifinta bawai don shi yana Ra”ayin zama da ita ba,gashi zai auro wacce yakeso su zauna tare,ita kuma ko oho,Bayan sungama waya da Ummi takasa zama waje daya,zuciyarta na mata zafi,dan cikinta sai motsi yake,nan ta zube bisa Cafet din Falo tana ta kukan tsausayin kanta,batason haka take mugun son Saleem ba sai yau da akace zai yi aure,ji take kamar ta kashe kanta saboda bakinciki,ta riga tasani ita tazama bora shara,dama yaya lafiyar kura balle tayi zawo.

Haka yazo ya sameta cikin wannan Halin,daya tambayeta meke damunta,kawai sai tace cikinta ke ciwo,ya damu ya duka kusa da ita yana kallon cikin yake tambayanta ko su tafi asibiti ne? Kai ta girgizamai kafin tacemai ita ta sha mgani zai bari,Ganin yadda take kallonshi asace tana sharan kwallah ne zuciyarsa ta fara zargin wani abu,Daga karshe ma rarrafawa tayi ta mike ta shige dakinta tana Sharbe hawaye,da kallon mamaki ya bita,domin ranar ma ko takeawy din dayayimata ma bata kallah ba,balle har yasa ran zata ci,Dayakoma daki yayi ta tunanin kodai wani ya sanar da ita Abunda ke Faruwa ne,ammh kuma baya Tunanin haka,Saleema ce mai bakin rariya kuma basa shiri,ko shi din ma ya rage sakarmata Fuska don ya gane tana da raini ne,ganin bashi da amsa tambayoyinshi yasa ya watsar da batun ya cigaba da harkokinshi ammh bawai don bai damu ba,A”a sai don yana wofantar da Abun karya bashi muhimmanci.

Ko washegari da zai Fita sai da ya lekata tana kwance cikin bargo idanuwanta sun kumbura saboda kuka,Domin kwana tayu tana kukan tsausayin kanta da kishin Saleem daya hanata Runtswa,sai ajiya takara sanin cewa soyayyar Saleem yayi mata mugun kamu sosai,domin kishinshi ya kusa illata jiya,ga yunwa taki cin abinci.ganinta cikin wannan halin ya bashu tsoro har Saida ya zauna gefen gadon,yana yaye bargon data Rufa dashi,hannunta ya riko yaji zafi sosai,har saida ya dago yana kallonta kanta na bisa Filo tana kallonshi itama cikin wani yanayi.

Kuri yayi mata da ido,yana kallonta kafin yace”ke wai meyasa kin cika Taurin kai ne MALIKA....”Yafada cikin wani yanayi yadda yakira sunan nata,sai da tajishi har tsakiyar kanta,Lumshe ido tayi tana jin wani yarr,balle ma yadda yaketa murza tafib hannunta,Cigaba da cewa yayi”Tun jiya nace miki ko zamu tafi asibiti ne kika ki yarda wai kinsha mgani,don Allah kalli idanuwanki yadda suka kumbura suka chanza kala?ko haka kikeso na barki daga baya wani abu yafaru Abbi da Ummi ko Daddynki suce da gangan  naci amanarki ko..?

Dakyar ta iya bude idanuwanta cike da kwallah tace”Bafa wani abu bane,nama ji sauki..”Tafada tana kauda kai,Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya mike bayan ya saki hannunta,wanda shi kanshi Taushin hannun nata yafara dibamshi zuwa wani yanayi na dabam,A kaikace yace”Toh naji kin samu sauki,yanzu dai kya bari ko Maman Abba nama mgana tashigo ta dubaki kafin tatafi asibiti..”,Jin ya ambaci Maman Abba da hanzari ta dagamai kai,tana share kwallah,Ido ya sakamata har ya kada kai zai Fita ya dawo da baya yana Fadin”,Wai don Allah na tambayeki mana? wannan Koke koken duk miye silanshi,da nayi miki mgana daga jiya zuwa yau sai ki kama min kuka kina Share min kwallah,Nayi miki wani abu ne Daya bata miki rai..?”Yafada yana mai kureta da ido,duka hannunsa Sarke cikin aljihun wandonsa,na american Suit dinsa.

Runtse ido tayi tana Kyabe baki tace”Allah ba komai..”Ta fada tana juya baya,kada yaga hawayenta,Ya dade yana kallonta kafin ya kada kai yafice Abun na mishi ciwo,ace yarinya bata da aiki sai kuka,haba ai abun yayi sosai,gashi kukanta damunshi yake,in yana kaunar mutuwarshi toh yana kaunar kukan Malika,ita kuma bata ganewa

Yayi sa”a yana Fita yacikaro da Baban Abbah zai Tafi kai danshi mkranta Daga chan ya Wuce wajen aiki,wajensa ya karisa suka gaisa kafin ya tambayeshi ko Maman Abba na nan,don Allah yana so ta shiga ciki ta duba mai dakinsa ce,batajin dadi,Baban Abba da kanshi yakoma cikin gida ya sanar da Maman Abba sakon Saleem batayi jinkiri ba ta sanyi hijabinta suka Fito tare,nan suka gaisa da Saleem din yace zai Wuce in akwai wata mtsalane su nemasa awaya,Adawo lafiya tayi mai kafin ta Shiga gidan Aranta tana Fadin”Insha Allahu ma ba mtsala”Sukuma magidanta kowanne ya Shige motarshi zuwa wajen aiki.

Halin Da Maman Abba taga Malika ya bata tsoro,da hanzari ta dagota daga kwancen tana Fadin”Madam meya sameki haka? jikinki ya dau zafi,Allah yasa ba maleria bace ke son kamaki ba..,? Rau rau Malika tayi da ido kafin tace”Bansani ba,kilama itace…”Tafada wasu hawaye masu zafi na zubomata,Kuri Maman Abba tayi mata da ido kafin tace”Kinga idonki kuwa? kuka kisha haka,alhalin kisan irinku ba”a son suna shiga damuwa ko zama da ciwo haka..”Jin haka yasa kuka ya ciyo Malika batasan sadda ta fada jikin maman Abba tana Fadin”Toh ya zanyi..? Maman Abba ki Fadamin ya zanyi? Aure zai fa zai kara..”Tafada cikin gunjin kuka tana Rumgume maman Abbah.

Maman Abba datayi mutuwar zaune jin Statement din Malika na karshe da azama ta dagota hannuwanta dafe bisa kirjinta tace”Ki!…Me?Kishiya fa kikace? wai da gaske kike Madam..?Malika na kuka tace”Wlh da gaske nake,kuma bai sanar dani ba mahaifiyarshi ne, ta kirani take gayamin..”Zaro ido Maman Abba tayi kafin tace”Ke don Allah..? Kina nufin shi bai sanar dake ba? kan durun jar uba ni Samiha,Yo Allah na tuba ni kishiya ko tashiga motar hayace ai bana bukata,balle ta raba miji..”Tafada tana jinjina Abun.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button