MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL
MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Kan kafadarta Malika ta yada kai tana kuka,Rumgumota Maman Abba tayi kafin tace”Ammh ko bai kyauta ba,ai ko bakomai kyaci darajan cikin dake jikinki da kuma soyayyar data hadaku zuwa ga aure..”Dagowa malika tayi tana kallon Maman Abba kafin tayi mata mirmishin yake tace”Bazan ci wannan darajan ba Maman Abba,ba auren soyayyah mukayi ba,hasalima auren mu ba kan Turban zama bane,an kulla shine kan Turban SAI NA RAMA………”
Jagale Maman Abba tayi tana kallonta kafin tace”Ban fahimceki ba…”Tafada cike da mamaki,gyara zama Malika tayi tana kallonta kafin tace”Nasan bazaki gane ba,sai kinji lbrinmu daga Farko har karshe…”Nan Malika ta Shiga bama Maman Abba tarihin rayuwarta Tundaga farko har zuwa aurenta da Saleem,da komai da komai bata iya boyemata ba,ta karishe tana Fadin”Na sanar dake lbrina ne,Maman Abbah domin kila kina da hanyar da zaki Taimakamin,wlh inason Saleem so mai tsanani,ammh naga alaman ni bana gabanshi ya tsaneni,Tun kuskuren dana aikata abaya,ya zanyi..? Wani mataki zan dauka nima yasoni kamar yadda mazaje keson sauran matansu..?
Tafada tana tsananta kukanta,Sai gashi Maman Abba ma kuka take,kukan tsausayi Malika da kuma rayuwar datake ciki,Riko tayi ta mikar da ita tsaye tana Share mata kwallah tace”Hakika lbrin rayuwarki Abun tsausayi ne Malika,ki kwantar da hankalinki insha Allahu sai inda na gaza,zan taimaka miki wajen samun soyayyar mijinki ahannunki,wanda nake da tabbatacin cewa shima yana Sonki..”Malika ta girgiza kai tana Fadin”Bar gayamin haka saboda naji dadi ni nasan cewa Saleem bayasona ya tsaneni..”
Maman Abba tace injiwa? wlh dabaya sonki babu wanda zai tilasta mishi zama dake Malika,yana sonki buh Shikanshi baisan yana sonki ba,kece ya kamata kitafiyar dashi ta hanyar da zai bayyanar da son nashi batare daya sani ba..”Zuru malika tayi mata kafin tace”Ta yaya kenan..?
Mirmishi Maman Abba Tayi kafin tace”matso da kunnanki kusa kiji..”Da hanzari malika ta matso da kunnanta Maman Abba tayi mata rada,wanda ya sata sakin mirmish,gira maman Abba ta dagamata tana Fadin”To ya..? Mirmishi ta saki kafin ta bata hannu suka Tafa tana Fadin”Mu wayewar banza ai muna da ita Maman Abba,barikin ce kadai bamu kware akai ba..”Dariya suka sheke dashi kamar basu bane dazu suke kuka ba.
Maman Abba bata tafi ba,sai Da rana ta kana ta koma gidanta tayi aiki ta dora girki,Tunda yau Dutynt dare take dashi,Malika taji dadin shawarwarin Maman Abba,ko banza ta samu mai bata shawara da kuma wanda zata kallah yau amtsayin wacce suke da kyakyawan alaqa da ita,Shikenan jiki ya warware dama kishi ne da rashin abokin shawara,koda Saleem yadawo da rana ya kawo mata abinci ya ganta ta samu sauki,har Fuskarshi taga jin dadinshi ba kamar yadda ya fita da safe ba
Ita da kanta ta kira Hajiya binta take sanar da ita auren da Saleem zai yi,Hajiya tayi Shuru aranta tana salallamin Malika da kishiya ai sai Allah,toh meta sani banda gata da sangarta,Hakuri dai tayi ta bata da kuma kara jadaddamata data kula da kanta da Abunda ke cikinta,daga karshe tasanar da ita da zarar Joda ta kamallah Semester ta karshe zata turo mata ita ta taimakamata har ta haihu,Malika taji dadi sosai har sai da Ta nunama Hajiya murnanta tana ta mata godiya.
Hajiya binta batayi karambanin sanar da Daddyn Malika Ba,saboda gudun tashin hankalinshi balle akwanakin nan Ciwon nashi yatashi har suna Tunanin komawa ma asibiti asake dubashi,ko tashin jikin nasa ma Shi yace kar asanar da Malika saboda kar hankalinta yatashi har yataba lafiyan Abunda ke cikinta..
Bayan kwana biyu da yin haka Kawai yana zaune a cikin office dinshi misalin karfe Uku na rana sai ga wayar Abbi,gabanshi har yafadi daya ga kiran,cikin sanyi jiki ya daga kiran,Yana ma Abbi sallama bai amsa mai ba yace cikin wata murya mara Dadi..”Saleem don Allah komai kake yanzu ka bari kataho katsina,asibitin da”aka kwantar da Mahaifin malika zaka zo,domin nima da safe matarshi tamin waya akan nazo jikinsa ya tashi Tub jiya da daddare,basu kwana agida ba sai asibiti,kuma yana ta kiran sunanyeku kaida Malika..”
.
Zumbur ya mike yana Fadin”Innalillahi…Ganin nan zuwa yanzu insha Allahu..”Yafada yana goge zufan dake kwararo mai ta saman kanshi,bai dauki komai ba,sai makullin motarshi ya Fice da hanzari yana addu”an Allah ya tashi kafadan Daddy ko gida bai koma ba,daganan ya dauki hanyar katsina bai ma Tuna daya biya ya sanar Da malika ga inda zashi ba,jin yanayin muryar Abbi dayaji shi ya tabbatarmai da Jikin Daddyn ba dadi…
Shakira..”
MALIKA MALIK…!
(Sai na rama..)
ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى ASSɷ????
Mallakar:Janafty????
20
Gudu yayi ta shararawa bisa kwalta cikin lokaci sai gashi ya isa cikin asibitin da misalin karfe 5:30Pm na yamma,koda yaje ya tarar da Abbi da su hajiya binta da wasu yan”uwanshi dake Malumfashi dukkansu awaje abakin Emargency suna ta koke koke,Hankalinsa tashe ya karisa wajen Abbi yana rankwafawa ya gaisheshi.
Dagosa Abbi yayi idanuwansa sun chanza launi yana Fadin”Ina malika? meyasa baka taho da ita ba,?tana bukatar ganawa da mahaifinta..”,Jikinsa asanyaye yace”,Wlh Abbi daga office nake ko gida ban koma ba,na kamo hanya,ammh zuwa gobe sai naje na taho da ita..”Bai samu zarafin mgana ba wani likita ya Fito daga cikin emargency din hankalinshi atashe yake Fadin”Wai Saleem din ya kariso..? Da hanzari Abbi ya riko hannunshi suka nufi Dr yana Fadin”Allah ya kawo shi Dr,..”Bai yi mgana ba illah kallonsu da yayi yana Fadin”Ku biyu kadai na yarjema ku shiga,kuma don Allah minti biyar plz,kuduba halin dayake ciki..”Gyada mai kai Abbi yayi,shiko Saleem Tuni ya tura kai cikin dakin hankalinsa a matukar tashe.
Hajiya binta ta kariso tana hawaye Tun kafin tayi mgana liktan ya dakatar da ita da hannu yana Fadin”Don Allah hajiya ki koma baya,ko baki ga halin da yallabai yake ciki bane,Kuna fa ciki tun dazu kuna koke koke,kuma Numfashinsa baya tafiya sai da taimakon oxygen,so don Allah go back,ku barmu muyi aikin miu plz..”Ya fada yana hada hannunwanshi kafin ya juya ya Wuce cikin sassarfa,da kuka hajiya takoma baya tana Rufe hannunta da Hijabin jikinta.
Saleem bai san yadda hawaye yake Fitowa daga idanuwan Namiji ba,sai yau domin lokacin daya karisa gaban Gadon Daddy bai iya ganeshi ba,ganin yadda gabadaya halittanshi ta chanza Fuskarshi da bakinshi sun zaganye babu kyan gani,Numfashinsa baya tafiya sai da taimakon oxygen,Gashi dai yana kallonka,ammh kuma sai dai kaga yana zubar hawaye kawai,durkuso yayi agaban gadon yana riko hannun Daddy mai lafiya,lokaci daya yaji hawaye mai Dimi sun zubomai..
Daddy daya ga Saleem ne rike da hanunshi,sai yafara so yayi mgana ammh babu hali,sai mika hannu yake yana zaburar jiki,Kai tsaye saleem yasaka hannu ya ciremai Oxygen din yana Fadin”Daddy gani nan,nine Saleem..”Bakin da Daddy akarkace yana zubda miyau yake Fadin”Ina…Ina malika..? Cikin dabar dabar da bakowa zai gane ba,Saleem na goge kwallah yace”,Tana zamfara Daddy tafiyan agaucene shiyasa ban zo da ita ba,ammh gobe zan je nazo da ita insha Allahu..”
Shuru Daddy yayi yana maida Numfashi kafin ya damko hannun Saleem gam yana Fadin”A”a kabarta baisai tazo ba,bana so tazo taganni cikin wannan halin,nafison ta ga gawata Fiye da ganina cikin halin jinya,Amanar dana baka zan kara jadaddama,Saleem don Allah ga Amanar malika nan da Dukiyarta kaine gatanta yanzu bata da kowa,don Allah karka barta kada ka gujeta balle kaba Rauninta damar illata rayuwarta..”Yafada yana maida Numfashi sama sama.