MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL
MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Kanshi ya daga mata cike da jarumta don yana son yanzu ya sanar da ita Abunda ke Faruwa kafin su isa,Hannunta bisa saitin zuciyarta tana Fadin”Wani abu yafaru ko? ko wani abu zai Faru,Tun jiya naji ajikina wani abu na Faruwa..”Tafada hawaye na wanke mata Fuska,Saurin karisawa yayi gareta yana fadin”Waya ce miki wani Abu ya faru. ? Dagowa idanuwanta tayi da suka kada sukayi jawur tace”Karka sake cemin babu Abunda ya faru,Mallam in babu Abunda yafaru me zamu je muyi a katsina harda kaya kuma,Don Allah ka sanar dani Abunda ya faru da Daddyna ni musulma ce kai ka koyar dani yarda da kadaddara mai kyau ko mara kyau..”,Takarishe cikin gunjin kuka
Tuni tsausayinta ya lullubeshi da hanzari ya jawota jikinsa ya Rumgume yana lallashinta cikin tatattausan kalamai,,Tunda taji yafara Mata Nasihan yin hakuri da rayuwa tare da sanar da ita mutuwa dole ce ga duk bawa Tunda harta monzon Tsira salallahu alahi wasallam ya dandani Dacin mutuwa to kowama aduniya sai ya dandaneta,Jikinta ne yakama rawa ta dago daga kirjinsa tana fadin”Dad…dadd..Ya..aa rasu ko..”?Tafada bakinta da jikinta na rawa kura mata ido yayi shima yana jin kwallah ta cikamai ido,bai iya kallonta ba,ya Gyada mata kai yana Fadin”Allah ya karbi Abinshi malika domin yafimun sonshi,jiya ina asibitin Allah yamai cikawa,ya rasu yana ambaton sunanki tare da rikon na rike mishi ke Amana bisa gaskiya ya rasu yana Farincikin yabarki hannun na gari…”
Har yagama mgana bata kara motsi ba,illah wasu tawayen hawaye dasuke mata barin makauniya bisa fuskarta,kyam take kallonsa bakinta na wani karkarwa,lura da hakan da yayi yas,kamata da karfi tana kokarin Fizge kanta ya tusata cikin kirjinsa yana Fadin”A”a kar miyi haka dake ,Yanzu kika gama sanar dani kin yarda da kaddara mai kyau ko akasinta,ki daure zuciyarki kiyi kuka na salama,Indan kin rasa natsuwarki kiyi ta maimaita innalillahi acikin zuciyarki insha Allahu zaki samu ramgwane…”Kukan daga karkashin zuciyarta ya Fito da karfinshi bude baki tayi ta sakeshi tana wani kamkame shi kamar zata kadasu,..
Kyakyawan riko yayimata yana Faman bata baki,ammh ina haka take wani kukan gwanin ban tsausayi,Neman take ya saketa ta zube kasa,yaki sakinta sai ma kokarin Dago Fuskarta yake taki yarda Muryanta har ta Dishe saboda kuka fadi take”Daddylove din nawa ne ya rasu..? Wayyo Allah na!Na shiga uku yanzu bani da kowa..Wayyo ni Malika..!Take fada kamar zata Shide,ganin haka yasa ya toshe mata baki da bakinshi yana kissing dinta cikin gaggaawa,itako Fuskarta yana ta barin hawaye,sai da yakara lashe hawayen nata tas kana ya saki Fuskarta yana maida Numfashi,kamar yar maye haka takoma bisa kirjinsa ta lafe bayan ta kamkame shi tana wani shessheka.
Bayanta yake Shafawa yana Fadin”Take easy Malika,Kidaina fadin baki da kowa karki yi sabo,kina da Allah kuma kina da ni,ga su Abbi wanda na tabbata son da suke miki bai kai wanda sukemin ba ni da suka haifeni.,NAYI MIKI ALQAWARIN BAZAN BARI KIYI KUKA BA,MATUKAR INA RAYE TARE DAKE..”Yafada yana kamkameta saboda yadda take Fitar da sautin kuka,Yayi ta lallashinta yana mata nasiha,yana cemata ba kuka yakamata tayima Daddy ba,yanzu yafi bukatar addu”arta fiye da komai.
Dakyar ta yarda ta bar jikinshi ya zaunar da ita gefen gado zai shiga tiolet ta riko hannunshi,cikin sanyi jiki ya waigo yana kallonta,Idanuwanta da suka kala ta sakamar kafin tace”Yaushe Daddyna ya barni mallam..? Hannunta ya kama ya damke cikin nashi cikin taushin murya yace”Jiya da daddare,Daren da kika ga nayi ai chan naje,da rana Abbi yakirani yake sanar,tashin hankali ne yasa ban dawo gida ba,na wuce daga chan,…”Runtse ido tayi hawaye suna zubomata kafin ta bude tana Fadin”Yaushe za”a yi jana’izarsa..?Yana shafa bayan hannunta yace”Yau da misalin karfe 11 saboda bakin nesa da zasu so..,Shiyasa nake so mu tafi da Wuri..”Bata kara mgana,sai ma kokarin mikewa datake,ganin tana rawan kafa kamar zata kife yasa yayi hanzarin rikota ta fado jikinsa yadagata cak,ya shiga bayin da ita,Kasa komai tayi sai dai Shine yayi mata wanka anayi tana kuka,kyaleta yayi don yasan har abada bazai hana ta kuka ba.
Bai barta ba sai da ya wanketa tas,yanadota a towel ya maidota daki ya saukar da ita kan gado yana binta da kallo,duk hawayen da zai zubo mata shi zai sanya hannu ya sharemata yana lallashinta,shi ya shafamata mai yana yaba kyau da tsari na jikin malika daga cikinta har wajen babu abun yarwa,yadda yakeji kamar yakara kafin su tafi,buh halin datake ciki kadai ya dakatar dashi,Kallon dan cikinta kawai yake wanda keta motsi yana gani,shafa cikin yake yana kallonta cike da tsausaya,itako idanuwanta na Rufe tana rike hannunshi tana sakin nishi lokaci daya da hawaye.
Da kanshi ya Shiryata cikin doguwar riga cikin kayan daya dinkamata ne,ya sanya mata dankwali da hijabi,Agurguje yakoma dakinsa yayi wanka ya Shiryo cikin wata shadda ash colour,yana sanya hulansa zanna bukar ya Shigo dakin yace tatashi suyi sallah,ganin kamar jiri take gani yasa yace tabishi sallar daga zaune,haka akayi Azaune tayi sallar tana sharan kwallah gwanin ban tsausayi,suna idarwa da kanshi ya kimkimin akwatunta da yar jakan kayansa zuwa mota bayan ya dawo ne yazo ya kamata ganin tana tafiya dakyar ne yasa ya kuramata ido yana fadin”Are u okey…?
Kan kirjinsa ta lafe tana gyadamai kai,cak ya dauketa har cikin mota ya ijiyeta kafin yakoma cikin gidan ya kakakkashe duka na”uran wutan gidan bayan ya kulle kofar babban Falon gidan kafin ya Fito,wajen megadinsa ya nufa bayan sun gaisa yabashi key din yana sanar dashi rasuwar baban Malika,maigadi nata kwararo addu”a yana sanar da Saleem yanzu yaji sanarwan aradion.
Komawa motar yayi ya shiga yana Daura set belt,itako ta sanya kanta tsakanin cinyoyointa tana kuka bai mata mgana ba,ya shiga karanta addu’ar da Annabi muhammed (SAW) ya koyar damu in zamuyi tafiya bisa wani abin hawa,kai tsaye yatada motar yana zubama megadi hon wanda ya wangalemai get da hanzari ya sulala waje yana musu fatan Allah ya kiyaye hanya yakuma bada hakurin rashi Ameen.
Momyn ladingo ce
MALIKA MALIK…!
(Sai na rama..)
ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى ASSɷ????
Mallakar:Janafty????
Dis page is For u MY BEST????Endless of love Besty
21
Karfe 10 da wani abu suka isa anguwan su Malika,wanda Tundaga farkon layin har karshe jerin gwanon motoci ne na gani na Fada,anguwan tacika makil,Malika ko Tunda suka baro Zamfara take kuka har zuka iso katsina,Tun Saleem na bata baki har ya gaji ya kyaLeta.
Bai samu damar Shiga da motar ciikin haraban gidan ba,sakamakon yadda aka wangale get din Mutane sunyi Dafifi kowa nata daura alwala saboda lokacin Jana’iza ya kusa,Malika dataji kanta na sarawa ta dago kanta tana bin ko”ina da kallo,Zuruf tayi zata bude Murfin motan sai taji hannun Saleem bisa nata ya damke,waigowa tayi tana kallonshi wasu hawaye suna zubomata Kara damke hannunta yayi yana kallonta kai tsaye kafin yace.
“Kiyi min wata alfarma plz..? Girgiza kai tayi tana Kokarin kwace hannunta,shiko yaki sakinta ganin haka yasa ya Bude baki yana Fadin”kada ki yi kuka sosai,kinga fa Tundaga Zamfara kike kuka,har muka iso nan,don Allah in kika Shiga ciki ki tararro juriyanki kada kiyima Daddy kuka,ayanzu haka yafi bukatar addu’anki Fiye da na kowama..”Runtse ido tayi hawaye suna kwaranyomata kai ta gyada mai alamun taji,mirmishin yake ya saki kafin ya Kai hannun nata bakinshi ya sakarma wani light kiss,kafin ya saketa ta bude murfin motan da hanzari Ta fice tana Rufe Fuskarta da Gefen hijabinta kuka na kwace mata.