MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL
MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Shi kuma ya Fito daga motan ya nufi haraban gidan inda su Abbi ke tsaye shida sauran yan”uwan Daddy na Malumfashi,gaisawa sukayi yana kara musu gaisuwa,kafin shima ya koma gefe yasamu buta yafara daura alwala domin har an kammallah yima Daddy Sutura ana jiran lokaci ne ya cika a sallaceshi zuwa gidansa na gaskiya,kowa ka kallah awajen Fuska babu Annuri kowa yayi tagumi yana alhinin wannan Rasuwa ta Alhaji Abdulmalik Dankasuwa….
Itako Malika na Shiga Falon gidan ta tsaya cak tana bin kowa da kallo,gabadaya dangin Daddyn natane yan malumfashi suka cika Falon suna koke kokensu,wanda ada sune in ta gansu sun zo gidansu tayi ta fadan cewa sun zo maula sun cika musu gida,sai gashi yau sune suka zo su taru suyi kukan rashin da kuma Faduwar bango garesu gabadaya.
Nan idanuwanta suka kai kan Hajiya binta dake zaune gefe da dogon Hijabi ta carbi tana ja,Fuskarta ta kumbura saboda kuka,gefenta kuma Joda ce itama sanye da hijabi tana Sharan kwallah,Shigowar Malika shiya sa Falon ya dau Shuru kowa ya juyo yana kallonta cike da tsausaya domin ansa babu wanda akama mutuwa kamar ita.
Hajiya ta kalleta idanuwanta da suka sukayi jawur cike da kuka tace”Malika..”Takira sunanta cikin raunin da karayan zuciya,ai da gudu malika tatafi gareta ta Fada jikinta tana Fashewa da kuka,Rumgumeta hajiya tayi itama kukan take tana Fadin”Mun rasa Alhaji malika,mun rasashi lokacin da da ni dake muka fi kowa bukatarshi,wayyo Allah mutuwa tamana yankan kauna ta daukemana Alhaji lokacin da muke tsakar bukatarshi..”Take Fada tana kuka,Malika dake jikinta ta kara fashewa da kuka,cikin muryan kuka wacce ta Dishe take Fadin.
“Dama da gaske mallam yake Daddylove ya tafi ya barni..? Why..? meyasa zai min haka ? zai tafi ya barni cikin wannan Duniya mai cike da kunci ni kadai,ya rayuwata zata kare,wayyo ni Malika dama Allah ya dauki raina,nima na mutu abinne gawata kusa data Daddyna,domin babu Abunda zan tsinta aduniyar indan na zauna ba ni da kowa sai shi,gashi yanzu Babu shiii..”Tafada tana kara kife kanta akasa tana kuka harda jijjiga.
Wata wacce take kanwa ga Daddy tataso daga inda take ta riko Malika itama tana hawayen tace”Ashh malika bar Fadin irin wannan kalaman basu dace ba sam,ki na zaton Allah daya bamu shi bai Fimu sonshi bane? karki Manta gawan Mahaifinki na cikin gidanan kuma sai ki sakamai da mganganun banza da koke koke,yanzu ne fa zamu nuna mai mu masoyanshi ne ta hanyar neman masa gafaran Allah,gashi kema baki da lafiya ko so kike kijama kanki mtsala muna alhinin rashin Mahaifinki mukoma alhinin shiganki wani hali..? Girgizamata kai Malika tayi tana toshe bakinta da hannun kada kukanta ya Fito,Zaunar da ita tayi tana zama kusa da ita carbin hannunta ta mika tana Fadin”,Yita salati acikin ranki,Kibar kukan nan hakannan kada kijama kanki wata mtsalan Abdulmalik tashi ta kare ,sai dai mune muke cikin kila wa kalan Yaushe zamu mutu? yau ne gobe ne? bamu sani ba..”Take Fada tana Share kwallah.
Gabadayan Falon sai da kalamanta yasasu ta kwallah,itako Malika batayi gaddama ta karbin chasbawan tana karanta innalillahi bakinta na motsi ammh hawaye sun gaza daina gudu bisa kuncinta,haka Hajiya binta ma ana ta bata baki,ana mata Fadan tadaina kuka ita da zata Tallafin Raunin malika,ammh itama ta koma tana biye mata suna kukan da bashi da amfani,dole suka hadiye kukansu ammh fa zukata sun Raunana,gabba sun yi rauni suma.
Tashin hankali bai kara ziyartansu ba sai da akace Hajiya da Malika su fito su zo Falon waje inda aka shirya Daddy,domin sumai addu”a da ganin karshe,lokacin da Malika taci karo da gawan Daddynta kasa control din kanta tayi haka ta fada kanshi ta kamkameshi tana kuka mai taba zuciya kamar zata Shide,hajiya ce kadai ta samu daurewar yimai addu”an Fatan dacewa da kyakyawan mtsayi.
Malika kin sakin Gawan Daddy tayi Fadi take ita, Daddynta bai mutu kada su Fitar dashi,gashi ta rike makaran dakyau taki saki,sai da Abbi ya fita waje ya kira saleem yazo da karfi gaske ya bambareta jikin makaran yana lallashinta,ammh ita hankalinta ya bar jikinta,ganin tana Fizge fizge ne yasa ya Kara tsaurara rikon dayayi mata,har sukayi baya suna neman Faduwa,neman kwatan kanta take ita sai taje ta riko daddynta kada su Fita dashi,ammh Saleem bai barta ba sai da ya tabbatar da sun Fita da gawan waje kana ya Sausauta rikon nata yana Fadin”Haka mukayi dake..? Haba Malika stop don Allah baki ganin halin da kike ciki ne?”…Yafada yana kallonta cike da tsausayinta.
Kuri tayimai kafin kawai yaga tayi luu zata Fadi ya tarota yana Salati,ashe suma tayi sai da wadanda ke kusa suka taimako da Ruwa ya Shafamata kana ta Farfado,wannan karon babu kuka da baki sai dai kukan zucci da Fitowar hawaye,kamar an bude fanfo ammh ba mgana,Gashi ta makaleshi gam taki sakinshi,dakyar ta yarda ta koma jikin Joda,ammh sai da ya ce mata zashi jana’iza ne da an kai Daddy gidanshi na gaskiya zai dawo gareta,kana ta sakeshi ya Fice kamar ya mata kwallah.
Amsallacin jumma’an dake anguwan aka Sallaci Daddy,wanda ya tara dimbin jama”a iya kallanka mallam,agaskiya Daddy ya dace kama daga yadda Annabi ya kwatanta mana Dacen musulmi na kwarai,uwa uba ga Shedan mutane daya samu Abun sai wanda yagani,Amgakabarta ko ba”a matsaka tsinke wasu ma har aka binneshi basu hango ba,saboda tsabar jama”a,Saleem yana daya daga cikin shakikan Daddy wadanda suka sanya kanshi cikin kabari suka turbene da kasa,saboda imanin da Tunanin shima watarana nan za”a kawoshi yan”uwanshi na jini na gani zasu Rufe kanshi da kasa,kai Allah ka Shirya damu kasa mu dace Duniya da lahira.
Bayan an kaishi gidansa na gaskiya aka dawo ana cigaba da karban gaisuwa bayan an saka Rufunan manya manya cikin haraban gidan da waje saboda mutane,Su Abbi sune gaba gaba wajen karban gaisuwa,Saleem ko yana tare da Sadiq dayazo bayan angama jana”izar Daddy,da wasu yan’uwansu matasa irinsu yan malumfashi,Ba dadewa sai ga su Ummi sun iso,har cikin gida suka shiga inda suka iske malika zaune inda Saleem ya barta tana kwallah ammh ba”a mgana,Ummi ta zauna kusa da ita ta Rumgumota tana ta lallashinta da mata nasiha masu ratsa jiki,hakama Hajiya itama ta dora danata hadda hajiya binta basu kyale ba,suna ta bata baki,don babu shakka mutuwar Alhaji itama ta daketa.
Sai yammah kana su Ummi suka koma Abuja,haka akacigaba da amsan gaisuwa daga bangarori dadama,ciki harda manajojin gidajen man Alhaji Abdulmalik dankasuwa,tare dana kamfafonimshi,Malika kuwa tunda aka Fita da gawan Daddy bata kara ma kowa mgana ba,sai dai kawai aga hawaye suna zubomata,sallah kadai ke tada ita daga inda take,Abinci ma In Joda ta matsa mata taci sai kawai tarashi ta Shige tiolet ta kulle kanta tana kuka,data gaji da halin data ke ciki ne ta Fita waje taje ta sanar da Saleem,shima Hankalinshi tashe yazo yana magiyan Ta bude,ammh malika taki,yayi yayi,sai ya koma daga ban baki zuwa yimata Fada cikin zafi,ammh kememe Malika taki budewa kuma yanajin kara sesshekan kukanta,wanda ke tafasa mai rai.
Kada kai kawai yayi ya Fita daga dakin bayan ya Umarci Joda data rabu da ita ta samu natsuwa zata bude da kanta,haka ko akayi sai da tagaji da zaman bayin kana ta Fito tana goge kwallah,ganin ban tsausayi ga cikinta ya girma Tunda ya Shiga watanshi na bakwai kenan,sai daddare kana Malika ta iya shan madaran hollandian da kaza,shima Saleem ne ya ritsata kuma ya matseta ya dinga Turamata abaki,bayan ya gama yakoma aikin lallashi,tana Rumgume ajikinsa,Joda dake kula da Malika in ta gansu awannan yanayin sai ta dinga mamakin yadda aurensu ya kasance,ammh kalli yadda Saleem yake kafa kafa da malika Bayason ya barta tana kuka,Baya barinta sai ya tabbatar da ko bata bar kuka ba toh hankalinta ya kwanta,ta bar koken koken takoma tana ajiyar Zuciya.