MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Daga bangarenshi babu Shirye shiryen dayake gudanarwa ko kudin kayan aure ma Ummi ya tura kudi a banki ta bada oder kayan akwatuna,tsarin Shirye shiryen bangaren amarya kuwa sai da ya bude musu Wuta ita da Nadira,Abun takaichi aure kamar wani auren Mawaki,Evets wajen goma suka lissafomai baki ya sake yana kallonsu daga karshe ya Rufe bakinsu da Fadin Shidai banda daurin aure babu Abunda zai hallata,so in ma sun Shirya bidi’o’insu toh shi dai bandashi ayi lafiya 3hundered thausand ya tura musu yace suyi Abunda ya zama dole,sai kuma yahadasu da Sadiq tunda yaga yamatsamai Shiyasa ya hadasu don yaga shima dan Rawan kan ne kamar su.

Baita yarda yayi ma malika mganar ba,itama batayimai ba,sai ranar Suna kwance bayan sungama Samun Natsuwa tana kwance bisa kirjinsa,wayar Saleem tayi ta daukan daukin kira,wanda lokacin after 11 na dare ne,yana ji ammh sai ya dauki wayar ya kashe,ganin haka yasa Malika cewa”Ka daga kiran ka Mallaam..”Tafada cikin karfin hali.

Yana jinta yayi mata Shuru ammh kuma yana Rumgume da ita yana Shafa gashin kanta zuwa bayanta,Cikin kasalattaciyar murya yace”In dauka fa kikace?kinsan waye ke kiran ne..?Kai tsaye tace”Na sani ba amaryanka bane..”Abazata yaji mganar nata,duk ya ji wani iri ammh sai ya dake cikin karfi hali yace”Waya fadamiki zan kara aure..”Kai tsaye tace”Ummi ta sanar dani tun lokacin da aka sanya ranar..”

Shuru yayi bai kara mgana ba,itama sai taja bakinta ta tsuke,still kuma Zahran bata hakura ta daina kira ba,afusace ya dauki wayar ya kasheta gabadaya yana tsaki cikin ranshi,har ta Fidda rai da zai mata mgana taji yace”Ammh meyasa baki taba Nuna min Ummi ta sanar dake ba..”Tana kwance bisa kirjinsa bata dago ba tace”Saboda baka bani damar haka ba,bansani ba ko kana Tunanin cewa zan hanaka kara aure ne,nikuma ko daya babu yarda zan ce ka zauna dani ni daya mallam,Allah yabada zaman lafiya yasa ayi sha’ani lafiya agama..”takarishe Fada tana Sharan kwallah.

Tsausayinta ya kamashi,Fuskarta ya dago yana Share mata hawaye yake Fadin”will tok later,juz sleep now kinji..”,Gyada mai kai kawai tayi takoma bisa kirjinsa ta lafe,shikuma yana ta lallashinta ta hanyar Shafa bayanta zuwa kugunta cike da salon lallashi,har barci ya kwasheta shiko idanuwansa biyu yana Tunanin yadda yanayin zamansu zai kasance irin zahra ta Shigo rayuwarsu.


Bai kara tada mata da mganar ba,shiyasa itama tayi mai Shuru,bata karamai mganar ba sai da taga yafara gyaran gidan,gabadaya dakunansu zuwa falon duk an chanza komai da komai anyi sabon Fenti,kuma daga yammah daga Falon ya Fitar da dakinsa,aka gyara aka zuba komai da Malika taga haka sai tamai mganan cewa badai anan zai saka amarya ba,sai ya bata amsa da cewa eh anan gidan zata zauna,ammh adakinsa,shi kuma Zai koma sabon dakin daya gyara,sai Malika tace Me zai hana su koma gidan da Daddy ya bashi su zauna dukkansu,sai ya dinga zuwa musu Weeked.

Ya dade yana kallonta cike da mamaki kafin ya girgiza yace mata”Bazai yuyu ba,bai zauna da ita acikin gidan da akabashi saboda ita ba,cin Fuska ne wannan kawai ta barshi tazo nan su zauna,kuma Shi baya ra”ayin zama shi kadai yafison ya hadashi matanshi waje daya ta bari in tana so ta zauna agidan ta bari sai ta haihu sai su rinka zuwa suna hutunsu achan,data mtsamai sai ya bata Fuska yace tadaina ma Damunshi Dole Abunda ya tsara shi za”ayi.


Biki saura Sati biyu Aka kai akwatunan aure kano,wanda Ummi da ita da wata kawarta da wasu goggonin Saleem yan kumo suka kai kayan,akwati takwas,shake da kayan arziki wanda aka karbesu hannun bibbiyu Abunda sai wanda yagani,Suma achan din anyi musu kara sosai sunci sun sha,kuma sunyi guzurin Abun soye soyen da’akayi musu basu ci ba,Takwaichin Turaman atamfafi ashirin Hajiya Saratu momi ta basu da kudi 50k,Daga kano zamfara suka Wuce suka kaima Malika kayanta wanda aka hadamata dana Haihuwa,Dayake tayi scanning ance mace zata haifa,akwati hudu nata uku kuma kayan bbys ne Abun sai wanda yagani,Malika taji dadin zuwansu ba kadan,ita da ada take jin haushin baki suzo gidansu,ammh sai gashi yau Malika tana neman ma bako yazo wajenta koda daga kauye ne..

Ba Aranar suka koma ba,sai washegari suka koma Abuja,wanda kafin tafiyarsu sai da suka tara Saleem da Malika suka yi musu nasihan da fatan su xauna lafiya da junansu,Amarya kuma Ummi tace ranar da za’a dauko ta daga kano Abuja za”a kawota sai ta kwana kana washegari su wuto zamfara da ita.

momyn ladingo..

MALIKA MALIK…!
(Sai na rama..)

ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى ASSɷ????

Mallakar:Janafty????

23

  Abangaren gidansu Zahra ne Shirye Shiryen yafi yawa saboda itace uwar gayyah,Tun ana saura sati daya biki Hajiya Saratu momi ta dauko hayar wata Falmata mai gyara amare daga maiduguri,wacce zata gyara Zahra ciki da bai kafin ranar bikin yazo,Hakika bakaramin burgeta momi tayi ba,haka takasa boye murnata afili dama ita burinta taje ta rikita Saleem wanda zai manta da kowa da komai sai ita shalele Fatimatul zahra’u.

Bangaren gidansu Saleem kuwa Abbi shima ya saki aljihu ana ta Shiryen shiryen biki,Tunda daga kano Abuja za’a kawo zahra sai ta kwana washegari su Wuto zamfara da ita,wannan Auren na musamman ne,domin yazoma Saleema akan gaba,sun gama Final Exams dinsu ta tararro ta dawo gida aka Shiga shagali da ita tayi alqawari sai ta chusama Malika haushi Sosai da sosai,Balle ma Da Sadiq ya sanar da ita itama Zahran ba baya ba akwai kyau ga iya kwalliya da Iya tsara kalamai,Kawai sai taji lokaci ta burgeta saboda neman suna harda karban nombarta ta kirata suka gaisa.

Itako Zahra an samu nayi ai sai aka zare an samu kanwar miji abagas,abun takaichi ma Saleema bataji kunya sanar da Zahra duka sirranka auren Saleem da Malika wanda batasan dasu ba,yazamana Family issues ne,itako zahra kanta ya fashe harda daukan ma Saleema alqawarin sai inda karfinta yakare game da mallakan Saleem,harda ikirarin sai malika ta barmata gidan????.,Saboda munafuncinsu yazo daya,sai ga Saleema ta Shirya kayanta tsab tatafi kano gidansu zahra tace chan biki zai fi dadi,Allah barshi in Za”a kawota sai ta biyosu su dawo tare,Ummi da Abbi basu zargi komai ba sun zata dama kila chan kawayene suna da kyakyawan alaqa duba da itama Saleema zamanta yafi yawa akano,basu san ko kullewan ta munafunci bane.

Duk wannan Abun Saleem bai san dashi ba don babu wanda ya sanar dashi,Dayake ma Saleema yanzu bata gabanshi Tunda sukayi karon nan da ita agida yadaina mata dariya,gabda bikin yaga kiranta ammh sai ya Shareta bai daga kiran ba kuma bai calling dinta back,sai ana gobe biki yana Shirin tahowa Abuja inda zasu hadu anan gidan Abbi su Tafi daurin Aure,Zahra ta kirashi tana rokonshi don Allah ya iso kano yau ya hallarci Dinner dasuka Shirya,kawai sai yaji kamar muryan Saleema cike da mamaki yake tambayan Zahra murya wa yakeji kamarta kanwarsa Saleema..?Zahra na mirmishi ta sanar dashi itace,gabansa ya fadi hannunsa bisa bakinsa,yana jinjina al”amarin na Saleema tsoro ya darsu ranshi rai bace yace zahra tabata waya nan akaba Saleema waya ta karba tana gaisheshi bai iya amsa gaisuwanta ba ya kira sunanta a kakkaushe..

   “Saleema,Don ubanki uban me kikazo yi gidan su Zahra..? Tana tabe baki tace”Yo laifi ne don nazo gidansu matar da zaka aura,Don mutaru muyi shagalin biki tare..? yana Numfarfashi ya tare ta yana Fadin”Ke rufemin baki munafuka,kinsan Allah Saleema kinsan dai nasan halinki wlh tallahi in naji wata mgana ta Fito to nasan daga bakinki ne,Kuma sai naci ubanki na kakakkrya ki shegiya Mai dogon baki kawai..”Yafada yana huci ya yanke kiran,Tabe baki Saleema tayi kafin tace acikin ranta”Ni ba munafuka bace..”Tafada tana murguda baki kamar tana gabanshi,Nadira ce ke tambayanta ko lafiya,sai ta barsa tace bakomai..,”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button