MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL
MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Abangaren Malika ma,Joda da Maman Abba suna ta gudanar da Shiryen Shiryen zuwa amarya ta ango,Maman Abba da kanta ta karbi kayan Malika wajen kala biyar taba telanta ya tsaro mata dinkuna na gani na fada,kuma saleem yabada kudin da kanshi,kuma zahirin batu dinki sun Fita sosai,Gashi yayi mata masu yalwar saboda cikin jikinta.
Duk da Malika na boye kishinta bata bayyanashi ammh yau kam takasa control din kanta,balle dataga Saleem ya Shirya kayansa Zai Wuce Abuja bazai dawo ba sai jibi in sun taho da amarya,tana zaune agefen gado sanye da doguwar rigar Atamfa cikin dunkunan da Maman Abba ta dinkomata,tayi mata kyau sosai balle da cikinta yakara tsufa,sai ta dan kumbura kadan fuskarta ta cika sai takara kyau,tagumi ta zabga hannu biyu tana kallonshi yana kokarin saka botir din gaban wani yadinsa Fari ammh Shara shara ne,domin hatta Farar vest dinsa ana gani,Hulansa ya dauko xanna bukar,mai adon baki ajiki domin aikin jikin rigar baki ne,Yadorata akai agogonsa baki na fatar damisa yake daurawa kafin hankalinsa ya koma kan Malika wacce idanuwanta suka fara cika da kwallah.
Yadade yana kallonta kafin ya saki ajiyar zuciya ya karisa kusa da ita,har ya durkusa gabanta bata Sani ba,sai da sanya hannu ya ciremata hannuwan datayi tagumin dasu,kana ta dago tana kallonshi ido cikin ido, Kwabe Fuska yayi yana kallonta yace”Why…? Haba Amanata meyesa kikeson Allah ya kamani ne? ehe kina tagumi abunda kikasan babu kyau meyasa kikeyi..? Ajiyar zuciya ta sauke tana kallonshi dukar da kai tayi saboda bazata jure kallon kwayan idonshi saboda suna dauke da wasu sirranka wanda suke haddasamata wasu irin yanayi atare da ita.
Kanta na kasa tace”Na daina..”Ta fada tana sosa hanci dan mirmishi yayi kafin ya saka hannu ya dago habarta yana Fadin”Mejego..Uhmmm..Menene fadamin naji..? Yafada yana shafa lebenta da hannunshi guda daya,rikemai hannu tayi tana kokarin maida kwailarta tace”Katashi katafi kada kayi dare a hanya..”,Kwayan idonta yake son gani,ammh sai taki ta rinka kauda kai,shikuma yana binta da ido,ganin haka yasa yatashi tsaye yasa hannu ya dagata tsaye yana Kallonta cike da kulawa,bai bata zarafin mgana ba, ya budemata hannuwanta tafada,lokaci daya ta saki kukan data ke rikewa Tun dazu..”matseta yayi yana shinshinar Wuyarta cike da salo,lokaci daya yana Shafa cikin jikinta,Tunda dama ta gefe ya Rumgumeta,saboda cikin daya yi mishi shamaki.
Sai da tayi kukanta ya isheta kana tayi Shuru tana Ajiyar Zuciya,tare da sauke Numfashi,Mirmishi yayi yana Kara gyara mata daurin dankwalinta bayan ya bata Sumbata asaman tsakar kanta yake fadin”Kamar kada natafi Amanata,inaji ajikina zanyi kewarki sosai..”Da sauri ta dago kanta tana kallonshi kafin tace cikin sauri”are u Sure zaka yi kewata mallam..? Yana kallon cikin kwayan idanuwanta yace”Very Sure..Kefa zaki kewata..?Bata iya bashi amsa ba,sai kawai tayi dage ta kama lebenshi tana tsotsa da sauri rike kanta da hannu daya yayi,hannu daya kuma yakara mtseta cikin maranshi cike da salo Malika take sumbatarshi har sai da suka gaji kama suka saki juna suna maida numfashi,bisa kirjinsa ta lafe tana Fadin”Zanyi kewarka sau ba adadi mallam,kariga ka zama jinin jikina,rayuwata bazata iya tafiya ba sai da kai,ina nace maka bani son zama dakai akoda yaushe wlh nayi karya mallam,i so much luv u,don Allah karka bani ko bayan kayi aure..”Tafada hawaye na wanke mata Fuska.
Wani sanyi yaji ya Shiga cikin ransa,cike da farinciki ya damki Fuskarta da hannu biyu yana kallonta yace”Da gaske kina sona malika..”?Gyada mai kai tayi hawaye suna kwaranyomata,Bakinta ya sumbata kafin yace”Duk da yadda na lalata rayuwarki na toxartaki keda mahaifinki..? Hannayenshi ta damke tana Fadin”Da shine ma nakejin ka mamaye duka raina,kayi sanadiyar Chanza malika zuwa wata malikar dabam,in ko hakane ka taka muhimman rawa arayuwata mallam,ka koyar dani abubuwa dama,wanda ni banda bakin godemaka sai dai nayita maka addu”an Allah ya saka maka da gidan aljannah Firdausi..”
Bai samu zarafin mgana ba,illah matseta dayayi ajikinsa yana shakan kamshin Turarenta,cikin wata murya yake fadin”kinsa me? bai bata zarafin mgana ba ya cigaba da cewa”Nima sai daga baya nadinga jin Abunda na aikata gareki ban kyauta ba,mussama ranar danaje daukanki agidanku naji matukar kunyar yadda Daddy ya karbeni batare da yayi Duba da irin Tozarcin dana miki ba ya karbeni hannu bibbiyu kuma wani karin nadamar tawa yadda yabani ke batare da Gaddama ba,ranar naji kunya sosai..”Mirmishi tayi kafin tace”Ni kuma abu daya ke ban haushi a abunda kayi min in na tuna..?
Dago kanta yayi yana Fadin”Menene shi..? Gira ta matse tana Fadin”Har ka manta..”Tafada tana hararanshi,ware ido yayi kafin yace”Srry gayamin don Allah..”Yafada yana Shafa dogon hancinta zuwa karamin bakinta,Shagwabe Fuska tayi kafin tace”Yadda ka karbi Virginity na da karfin Tsiya mana..”Tafada tana Wulkamai ido cike da salo,Mirmishi ne ya Subucemai wanda sai da duka fararen hakoransa suka bayyana awaje,hannunta ya riko yana Shafawa har zuwa saman kirjinta yana mirmishi kafin ya gangaro zuwa katon cikinta,cikin husky voice yace”Ni kinga wannan daren D Unforgtable Night and moment kenan bazan taba manta wannan Daren ba..”Yafada yana Shafa cikinta yana wani munafikin dariya.
Fuska ta kwabe tana kallonshi kafin tace”Saboda mene…? Hannunsa ya dora bisa lebenta yana zagaya babban yatsanshi dashi yace”Baki sani ba..? ta gyada kai tana kallonshi Yar dariya yayi kafin yace”Dare ne mai cike da Tarihi ,dare ne da kika Shayar dani wata zuma mai dadi wanda banta zaton akwaita ba,Wlh tallahi i can Explain buh abu daya na sani ke ta dabamce domin Haryanzu kina kan Shayar dani wannan zumar,sai dai na ranar is so Sweet and special..”Yafada yana kanne mata ido daya,Dariya da kunya suka kamata,sai takaimai duka Kirji tana mai kukan Shagwaba dariya yake yana Fadin”Allah am Serious,ko zaki karamin ne,sai na kara tabbatarwa..”Wata uwar harara ta makamai kafin ta warci hannunta tana kallonshi,Juyawa tayi ta dauki yar jakarsa wacce ya sanya kaya ta rataya tana Fadin”Ni..? ai yanzu mun tsufa abari amarya tazo sai tabaka sabuwar zumar,muje na takamaka kaga dare nayi kuma,sadiq karya ga kamar ni na tsaidaka..”
Yana dariyanshi na Nishadi yabiyo bayanta tana tafe da kyar yace”Ai wlh kece kika tsaidani ko ya tambayeni haka zancemai,mganar zumar amarya kuma nidai Taki nasani ki bari in tazo na dandani tata,sai na tantance..”Yafada yana shafa gemunsa na rashin kunya cike da Nishadi tana jinsa tayimai banza ta Fito daga dakin tana mirmishi cikin ranta.
Har cikin kichen din yabi Su maman Abba yayi musu sallama,sukai mai fatan isa lafiya,da kuma Fatan Allah yasa adaura aure lafiya,Tare suka Fito da malika har haraban gidan ita da kanta budemai mota ta turashi,saboda taga bai da niyyar Tafiya sai kwakwumarta yake jakar kayansa ta sakamai akujera mai zaman banza kafin Tarufe mai kofar mota taja gefe tana dagamai hannu,Jagale yayi yana kallonta kafin ya bude murfin motan ya Fito,kawai sai ji tayi ya Rumgumeta kam kam,yana Sumbatar wuyanta,itama matseshi tayi tana kokarin maida kwallarta Sai da suka dau tsawon lokaci kafin ya saketa yana Riko hannunta yace”Ki saka ashafa miki wannan jan Abun na mata,zai yi kyau da hannunki..”Bata kalleshi ba tace”Toh..”Yana kallon Fuskarta yace”Kinji..Don Allah kiyi ko don ni kinji Amanata..”Muryanta cikin sanyi tace”Zanyi insha Allahu..”Mirmishi ya saki kafin ya duka ya Sumbaci bakinta,yana dagamata hannu ya fada mota,ya daura Set belt ya tada motan yana kallonta tana dagamai hannu,shima dagamata yayi kafin yayi Riverse da motar yazuba hon megadi yataso da sauri ya wangalemai get ya sulala waje Malika ta dagamai hannu,sai da ya karisa Ficewa megadi ya maida get ya Rufe kana ta juya zuwa cikin gidan tana Share kwallar data zubo mata.