MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

  Dangin mamanta biyu sai na babanta daya,sai kawayenta biyu sai Nadira da Saleema sai zahra su kenan,Suka kamo hanyar Abuja,Zahra tana ji kamar ta bude ido taga sun isa,don ma Nadira ta kwabeta da farko tafara gaddama bazata Shiga motar kowa ba,sai ta angonta wanda tuni yakara gaba,kujimin Amaryar zamani gaakiya Zahra zamanki cikin gidan Saleem akwai shan kallo…”!.


Sai bayan mangariba suka iso gidansu Saleem,nan fa kallo yakoma sama domin ganin tsaruwa na gidansu Saleem,zahra tana cikin mayafi ammh tana kokarin Fito da kai,sai da Nadira ta damketa dakyau tana mata Fada,Ummi da kanta ita da kawayenta suka Fito suka tarbi amarya da yan’uwanta cike da Farinciki da murna,suka dumguma zuwa cikin gidan inda akayi musu masauki adakin na mussaman da’a gyara domin su.

Nan da nan Aka fara jera musu abincin da ababan Sha da’aka tanadar domin su,wasun su ne suka fara gudanar da sallar kafin sufara cin abinci,ammh irinsu Saleema da Nadira sai da sukaci suyi nat,Abunda zai baka mamaki sai ganin Zahra ta cire dankwali ta Cire sikat tana zaune daga ita sai rigan Leshin jikinta da Underwears,ta Iyayen ciki suka mata mgana sai tace,zafi takeji bazata iya zama da Sikat din ba,Ai nan gidan iyayen mijinta ne,So kamar gidan Mijinta ne,Rike baki kadai sukayi suna mamakinta,basu gama mamaki ba sai gashi ta Fito da wani hadin gumbar mata tanaji,Duk kyafta mata idon Nadira keyi saboda Saleema awajen bata gane ba,Da wata kanwar Babanta ta mata mgana sai takara narke Fuska tace’Yo ni goggo Shatu,in bantashi tsaye na taimaki kaina ba,kawai sai na zauna tunda dai kun kasa,ai ni sai nayi Tunda gidan kishiya zan Shiga abun sai da tanadi..”

Tafada hankalinta kwance,daganan ba wacce ta sake mata mgana,Kowacce ta kama kanta,tunda sunsanta bata da kunya ko kadan,Itako zahra harda tafawa da Saleema tana kara zugata,Nadira dai Shuru tayi tana tsoron kada Zahra ta tafka kuskure,koda wani abu ya bullo Saleema yar”uwanshi ce, bazai taba rabuwa da ita,itafa Yana da ikon da zai yarda kwallan mangwaro ya Huta da guda…”

.

Yan gidan MALIKA MALIK PAID GROUP Kuna sha’aninku kucigaba da gashi Suya sai ranar da Saleem ango zai Shiga dakin Zahra’u Amarya????????????????????…

Momyn ladingo..

MALIKA MALIK…!
(Sai na rama..)

ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى ASSɷ????

Mallakar:Janafty????

Kada ki karantamin lbri matukar baki biya ba,In kika ka karanta batare da sani na ba na barki da Allah,in kina bukatar yin karatu cikin Salama ki nemi ta wannan Nombar wayar 09069067488

24

  “”””Har Dare Zahra bataga Angonta ya leko ba,sai tafara damuwa,Saleema ce tace mata tayi hakuri zasu Shigo Shida da Sadiq kila idon mutane, ne yahansu shigowa tun dazu,Da farko tabar damuwa ammh data ga har pass 9 ai sai ta dau wayarta ta laluboshi sai taji ya sakata a call waiting.,lokacin yana waya da Malika ne,yana gani ya Shareta saboda yasan ko ya katse kiran, ba wata mgana bace mai muhimmanci ba,Shirme ne kawai da Shiririta.

Zahra ko kamar ta Fashe saboda takaichi da bakinciki gefe guda,kuma wani Tarnakakin kishi ke dawainiya da ita gashi taki hakura da kira sai kira take yana sata a call waiting,ranta ko ya kara baci kamar ta Fashe ita kadai,kuma bai kirata ba,sai da yagama waya Da malika kana ya kirata,lokacin har kwalla sun Fara taruwa a idanuwanta.

Tana Dauka Sai ta Fashemai da kuka,Shuru yayi yana Sauraranta cike da mamaki yace”Topha…Lafiyanki kuwa..? Tana Shesshekan kuka tace”Shine..Shine ina ta kiranka kaki dauka kana chan kana waya da wata ko..? Mele baki yayi kafin yace”Da wata kuma..? Ni bada wata nake mgana ba da yayarki ne,kuma bisa adalci duk wunin yau ban kirata ba,Kinga ko takirani ai na dauka na bata hakuri ko..?

Wani bacin rai ya Shiga zahra sai ta danne kafin tace”Ok..Shine najika Shuru baka Shigo waje na ba..”,Mamakin kalamanta yayi kafin yace”Haba don Allah Zahra mena ke ci na baka na zuba,akwai saboda rashin kunya sai na Wuce gaban Ummi da Abbi zuwa inda kike,tsayama su bakin dake dakin in na Shigo ina zasu..? Yafada cike da Dattako,Tura baki tayi kai tsaye tace”Toh su Fita mana..”Baki yakama kafin yace”Toh badani za’ayi haka ba,duk Abunda kikema Rawan kafa in inkinyi hakuri zaki sameshi zuwa gobe,sai kin barmin Abun Fada ba..”

Ko ajikinta sai ma kara narkemai datayi tana Fadin”Toh Tunda kasan Abunda nakema rawan kafa mai zai hana ka min kwatantancen dakin sai nazo kabani ka Huta da Rawan kafan..”,Tafada tana wani shafa Bakinta,Zaro ido yayi bai mata mgana ba kawai ya yanke kiran gabadaya yana kiran Sunan Allah,har Sadiq dake gefenshi yana waya da Saleema ya dago yana kallonsa,bai mai mgana ba,ganin ya dauki wayarsa ya Shige Tiolet,shiko wayar ya dauka saboda kada zahra takara kira,sai ya sanya Nombarta cikin blacklist ya dauro alwala ya Fito..

Jin ya kashe wayarsa,bai sa tagane tabargazan datayi ba,saima kara kokarin kiranshi datake,ammh ta gaza samunshi,tayi tayi taki Shiga kwata kwata,cikin damuwa ta Fito Falo ta Samu Saleema kan kujera tana waya ta daga mata duka tana Fadin”Ke kanwar Miji tashi ki rakani dakin yayanki yanzu..”Ba Saleema kadai hatta Nadira dake gefe tana charting sai da ta dago tana kallon Zahra cikin wani yanayi mai kama da kinyi hauka..

Saleema tayi Saurin yanke kiran tana kallon Zahra tace”Dakin yaya Saleem,lafiya kuwa..? Yamutsa Fuska tayi kafin tace”Kawai ina son ganinshi ne,ko laifi ne don nace kirakani dakinsa,ai naga dai an daura aure yazama mijina..”Tafada tana kallon Nadira,wacce ke kallonta cike da takaichi.

Saleema tayi dariya tana kallon Zahra kafin tace”A”a ko daya,sai dai ni bazan iya wucewa dake zuwa dakin yaya Saleem ba,Su Ummi fa na falo,kuma bama haka ba wlh Yaya Saleem zai iya marina in na rakaki gwara kiyi hakuri ki kirashi ta waya..”Tafada tana sakin hamma,Jagale Zahra tayi kafin tace”Ina ta kiransa ban samesa ba…Tafada kamar zatayi kuka.

Batama bama Saleema damar mgana ba,ta mike tana Fadin”Tunda bazaki rakani ba,ni bari naje da kaina,nasan bazan bata ba..”Tafada ta na kama hanyar Fita daga dakin,Nadira ta mike data ga rashin hankalin na Zahra ba karami bane,itako Saleema Abun ne ya bata mamaki,domin bata zata Zahran takai haka Wauta ba,Nadira ta sha gabanta tana Fadin”Wlh in kika Fita daga dakin nan,sai na kira Momi na sanar da ita,haba kidinga Abu kamar Wata mara Tunani da ilimi,in kin fasa Fita kin zama shegiya…”Tafada cike da masifa.,tana gama Fadin haka ta juya ta koma ta zauna tana sakin huci,

Jin Abunda Nadira tace ne,yasa Zahra takasa Fita,sai ta joyu afusace tajuya koma ciki tana kunkuni,Sauran iyayenta kuwa kanzil ba wanda tace musu,sun so ne sai ta Fita wlh gari na wayewa su tatarra su koma Kano suce amarya ta Hutar dasu takai kanta daki,Saleema tabi zahra da kallo tana wani Tunani aranta na indai zahra ahaka take Tunanin Sace zuciyar Saleem,to da sake domin Yaya Saleem ba irin sauran sakarkarun mazan data sani bane,Mutum ne mai aji da takama,da Wuya su Shirya matukar bata gyara takunta ba,ganin haka yasa ta mike tabi bayanta,koda taje ta isketa ta kumbura kamar ta Fashe,saboda Fushi ita ta zauna tana ta bata hakuri tana kara nuna mata sai fa ta rage wani abu saboda tsaro,ammh suk zahra bataji tana ganin Abunda takeyi Shine Daidai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button