MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty


Washegari Tun bayan Angabatar musu da Abun kari suka karya sukayi wanka kowa ya Shirya saboda su isa da Wuri don bazasu kwana a zamfara ba dagachan zasu juya kano ne,Itako zahra an cakare cikin wata Shadda Ash colour dinkin Riga da Sikat,kayan Sun fita da ita ba laifi,Ummi ce ta Shigo gaida amarya da baki,Allah ya kyauta lokacin tana Sanye da mayafi da anyi Abun kunya,ammh fa ita kanta Ummi tayi mamaki ganin amarya tana gaisheta zaune kan kujera ta mike kafa idonta kyar akanta babu alamun kunyar nan ta Surukai,Abun ya daure mata kai sai dai batayi mgana ba ta Share,ammh aranta tana Fadin”Wannan wata amaryace Saleem ya kwaso kuma..?

Magana tayi akan Zata tafi da zahra chan wajen Abbi zai hadasu ita da Saleem yayi musu Nasiha ko gama Rufe baki Ummi batayi ba Zahra ta mike zumbur tana gyara mayafi tace”Yauwa Ummi muje..”Tafada tana yin gaba,ba Ummi kadai ba duk mutanen dakin sai da sukaji kunya,Tun ballatana Nadira taji kamar ta dora hannu aka ta yanka ihu,Saleema ko Wani iri taji don bataso ace wacce take goyon baya tana irin wannan Ba,duk zata bata musu Shirinsu Malikar ma ta Fita samun Fada wajensu Ummi.

Ummi ko Yaken Dole tayi tabi bayan Zahra tana kallonta cike da mamakinta,gefe daya kuma tana Tur da wayewa irinta yan matan zamani,don yanzu sai ace wannan ba komai bane wayewar zamani ce,ganin Sun Fita kuma batasan hanyar ba,shiyasa tabama Ummi dama ta Shiga gaba suka hau sama har Falon Abbi inda yake zaune bisa kujera Saleem wanda ke sanye da Farar Shadda dinki Muhammed,Aikin jikinta baki ne hakama hulan kanshi baka ce,yana zaune akasa kusa da kafafuwan Abbi kansa akasa alamun biyayyah da ladabi.
  
  Suna Shiga Falon Tunda zahra ta hangi Masoyinta ta fara washe baki,sai kawai tatafi kusa dashi zata zauna,kanshi na kasa ya dago yana hararanta cike da takaichi,ganin haka yasa Abbi fadin”Kyaleshi diyata dawo nan..”Ya fada yana nuna mata dayan gefen,Ranta baiso ba takoma nan ta zauna tana kallon Saleem cikin so da kauna kamar ta jawoshi ta Rumgume haka takeji,balle yadda yayi mata kyau yau sosai..

   Ummi dake tsaye gefe ta rike haba tana Fadin Cikin ranta”Allah mai zamani…”Zahra saboda shagala da kallon Saleem bata iya gaida Abbi ba,sai Shine yake gaisheta yana tambayanta ya kwanan bakunta,sai lokacin ta danji kunya ta sunkuyar dakai tana ansawa,ammh kuma ta gefen ido tana kallon Saleem,shiko kunyar Duniyace ta isheshi gaban Ummi da Abbi,kan Abunda zahra tayi gabadaya sai yaji auren ma ya Fitarmai aka yarinya kamar mai tabuwar junnu.

  Nasiha sosai Abbi yayi musu,Yayima Saleem nasihan adalci a tsakanin matansa,Tunda Nauyi ya hau kanshi sai ya dage,banda nuna bambamci kowani wariya ga daya daga cikinsu duka matanshi ne,daga karshe  yajamasa kunnen sai ya jajirce dole yazama na Namiji don zama da mata biyu babu sauki,don ko Shi da yake ubanshi daya gareshi,Yayima zahra Fadan tabi mijinta tamai biyayyah Shine Ribanta da Tsiranta aduniyama Har zuwa ranar Gobe kiyama.

Kuma yayi mata nasihan ta zauna da abokiyar zamanta Lafiya ta kuma bata girmanta,wanda ko Ummi ma da Abbi yabata damar mgana Abunda tayi ta jadaddamata kenan,Sakale tayi kawai tana jinsu ammh azahirin batu hankalinta baya tare dasu yana chan tana Tunanin yarda zata ci uban Malika ne hankali kwance,Duk Nasihan da suke mata bata jiba,Domin tace duk suyi su gama miji dai natane ita take da ikon Sarrafashi yadda taga dama basai wasu sun tsara mata ba.

  Bayan su Abbi su sallamesu Saleem ya Dukar dakai yana godiya kafin su tashi su Fita,suna Fita zahra tayi zaraf ta riko hannunshi tana sakin mai mirmishi cike da salon makirci,Fizge hannunshi yayi yana kallonta kai tsaye yace”Zahra..Wai mike kanki ne? nan fa gidan iyayena,haba kidinga Abu kamar wata kilakin karuwa,dubi abunda kikayi dazu agaban su Abbi,yanzu Fisabillahi haka h amare masu kunya keyi tsakani fa ga Allah..”Ya fada cikin bacinrai.

Tura baki tayi kafin tace”To menayi kuma? ai ba Rashin kunya bane,suma su ummi murna zasuyi Ina son dansu sosai..”Kuramata ido yayi kafin yajamata wani dogon tsaki ya Kama hanya yana saukowa daga Steps da hanzari ta biyoshi har suka sauko hanyar dakinshi ya nufa,tako biyoshi jin tana biye dashi ne yasa ya waigo yana kallonta ganin ya tsaya ne,yasa itama ta tsaya tana kallonshi,Fuskarshi ba fara”a yace”Lafiya ina zaki naga kina bina ne…?

Rausayar dakai tayi kafin tace”Ina kuwa..? inda zaka mana..”Turbene Fuska yayi kafin ya nuna mata hannu yana Fadin”Kinga malama Wuce ki koma daki yanzu zamu tafi gidanmu sai kije chan kiyi ta rashin kunyarki,ammh wlh bazan bari ki barmin Abun Fada gaban dangi da iyaye na ba,karki sake ki Biyoni wlh..”Yafada yana Jadadda bayaninsa,Kafin ya juya ya Shige dakinsa ya banko kofa yana Ma kanshi jajen ya auro ma kansa jaraba da kudinsa.

  Ganin ya Shige ya barta yasa taja kafafunta takoma cikin dakin tana wani bata rai,ba wanda ya kalleta sai Saleema,wacce ke mata kirari cike da Iya Shege,nan da nan ta Shiga washe baki kamar wata sakarya,Yadda suka zo haka suka dauki hanyar Zamfara,ammh wannan karon babu  Saleema,wacce har ta Shiga mota Saleem yamata jan ido yace ta Fito,Tana tura baki ta Fita yayi mata kaca kaca,lokacin da Tajema Ummi tana kukan yahanata zuwa gidanshi,Shiko yace sai dai ta mutu Tunda ba uwar wani Zatamai ba intaje,dole ta hakura tanaji tana gani suka Fice daga haraban gidansu.

Sadiq shi ya sake daukan amarya sai motar gidansu Abbi da direba guda daya,Sai motar haya guda daya,wacce Saleem yayi tashanta,daganan Zamfara Kano zata Wuce dasu,Sun riga Saleem yin gaba,don shi kadai yataho amorarshi ammh bayan ya kira Malika ya sanar da ita suna bisa hanya,Ummi ko bata barsu haka ba,ta basu Turamen zani guda goma,da Turaren Wuta,dana daki,sai kudi ta ba masu kawo amayar aka rabu cikin girma da arziki.

  ****
Lokacin da Saleem ya kira Malika Tuni har an gama mata kunshinta ja da baki da kitsonta 2Steps????,wanda yayi mata kyau over sai wanda yagani kunsan Farin fata yana karban Jan abu da baki atare,sai kitsonta wanda ya kasance yiri yiri ne,dama akwai gashi sai ta fito ras da ita,Abu daya yayimata cika katon Tulalen cikinta,wanda tayi wanka ta Shirya cikin leshinta riga da zani ta kashe daure bakace Malika malik din nan bace mai sanya kananun kaya masu Fitar da tsiraici.

Tun jiya su goggo hadiza suka iso ita Zulai tare da suka taru dasu Maman Abba suka sha bikinsu ajiya,suna kuma kokarin Debemata kewa sosai,wanda yayi nasaran ragemata damuwa,da kuma kishi,duk da taji abun,mussaman da lokacin daura aure ya kusanto har yazo ya Wuce,taji Abun aranta,ammh basu barta Tashiga halin damuwa ba,Hatta Hajiya binta dake gida tana takaba sai da ta kira Malika tana kara tausanta,Mirmushi kawai malika take aranta tana Fadin”To in batayi hakuri ba, ina zata da wannan cikin,ko tabar gidan Saleem bamai kwasanta ya zauna da ita don Allah,saboda haka hakuri yazama dole gareta.

  Yana sanar da ita tasowarsu ta sanar dasu Joda,suka fara shiryen Shiryen taransu,duk da dama chan ashirye suke,gidan suka kara gyarashi sosai kafin su shiga kichen su dukufa wajen shiryama yan kawo amarya delious mai dadi cikin mutumci da kima.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button