MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Basu iso ba sai wajen 2 na rana suka iso,wanda Malika najin Sautin hon dinsu da kuma karar bude get,gabanta ya amsa ta tashi da Sauri Ta shige daki tana kokarin danne Abunda ya tasomata,Su joda da Maman Abba ne da Su zulai suka Fita suka tarbesu,Zahra dake cikin mayafi hankalinta na kan karema gidan da kallo,Haka take bin ko’ina da kallo har suka Shiga falon gidan suka zazzauna ana gaisawa ana tambayan gajiyan hanya,Joda ce kan gaba ta nuna musu dakin Zahra wanda ke kusa dana Malikan suka tashi suka Shiga da Zahra ciki,wacce dama ta kagu akaita dakinta taga wani iri ne.

Dakinta yana da girma,Shimfide da wani cafet mai taushi,wanda ya mamaye dakin gabadaya sai makeken rolay bed dinta da kuma Wardrope mai girma da Fadi,sai dressing mirror,sai kofar Tiolet,zahra a wulakance take bin dakin da kallo,Bawai dakin bai mata bane a”a so take taga na ita malikan ya yake? don ita zatonta Saleem ya raina mata wayau Ne Shiyasata ya sanya  awannan dakin wanda da kadan yafi na gidansu inda take kwana.

Joda da Maman Abba da Zulai su suka dinga kwaso musu kololin abinci zuwa cikin dakin Zahra inda suka ga Abun mamaki amarya ta zaune kan tsakiyar gado ta cire dankwali shigen gashinta mai kama da Hammatan dan iska awaje,duk ya mike Kallo kowa daya daya take tana wani girgiza kafa,Maman Abba da joda suka kalli juna suna mamakin wannan al’amarin daga zuwa har za”a nuna hali,sai da suka Fita zahra ta kalli Nadira take cemata”Wai yan biki kenan,? hala bata da wasu dangi ne ita Malikar,koda yake sai dai in taron arna..,”

Tafada tana yar karamar dariya,Tsaki Nadira taja tana Fadin”kedai kike kidanki da rawanki,in banda Shiga Abunda bai shafi mutum ba,ina Ruwanki da danginta,kedai tafi wajen Shigen rawan kanki da Shisshiginki miji ya ram miiki,kinga ko kya ga karshen Rawan kai..”Goggo Shatu tace”Kwarai da ma gaske,ai tama baras,Nadira tunda ta yada hali gaban Uwar miji,mai ya rage kuma,ai babu Shi Nadira,Allah dai kawai ya sauwake…”

Zahra ta tura baki ta kauda kai tana dauko wayarta tacigaba da Laluban Nombar, Saleem ammh har yanzu bata Shiga kuma,sadiq yace batare suka taho ba shi yana baya gajiya tayi da kira ta hakura takoma gefe tana kallonsu Nadira na cin abinci,Farar Shinkafa,da miyan nama,sai Fride rice,sai kunun aya mai sanyi,da ferfesun Naman kaji,kallonsu take don ita babu abinci agabanta so take ma suyi su tafi abarta daga ita sai angonta.

   Sadiq kuwa Joda tayi ta dawainiya dashi,bayan tabashi na Direban da zai maida Su Nadira ya kaimai,ya dawo yazauna falo yana cin abinci yana ma Joda hira har yana tambayanta Shi bai santa ba? tace mai ita kanwar Malika ce gidansu daya,Sai alokacin Malika ta Fito tana taku dakyar suka gaisa Da Sadiq yana kara kallonta kamar ba ita, ba kamar wata zara acikin wata,shi baima san cikinta ya tsufa ba haka don Saleem baya yarda yayi mganan Malika dashi,koshi ya jawo hirar Kauceta yake,ya basar.

  Suna cikin gaisawa da Sadiq din sai ga Saleem ya Shigo gidan yana waya,yana sagale da yar jakan kayansa,Sai da ya katse wayar ya kariso garesu yana bama Sadiq hannu suka tafa yana Fadin”Kai mutumina kayi Wuta ahanya fa..”Yar dariya Saleem yayi kafin yace”Ah to mezan jira,ai ban saka lerna ba,balle na dinga na lallaba Titi..”Yafada yana kallon Malika dake tsaye tana gyara zaman mayafin kanta,Kwabemata Fuska yayi kafin yace”Ba sannu da zuwa Yar Amanata..”Batayi mgana ba,illah karisawa datayi gareshi tana saka hannu ta karbi jakan hannunsa tana Fadin”Yanzu fa ka shigo..”Sannu da zuwa..”Kin sakin mata jakan yayi saima Rumgumota dayayi ta gefe yana Shafa fuskarta yace”Bar jakanan kawai kinyi Nauyi dayawa kada na zama mara tsausayi..”

Ya fada yana shafa cikinta lokaci daya yake Fadin”Kai cikin nan yayi kasa sosai,koda yau zai Fito Duniya..? Sadiq ne yace”hhh karma kayi Fatan haka don zaka tashi daga angon amarya ka koma angon karni,wlh baka ba kwanan dakin Amarya sai dai kwanan Asibiti..”Dariya joda ta saka,shiko murmusaa kawai yayi Malika bata hakura ba jakar ta sake karba ya sakarmata yana kallonta Mirmishi tayimai tana Fadin”Kada kahanani samun lada awajen Allah…”Hannunsa ya daga yana Fadin”Wane ni? ai ban isa ba,Allah yabamu ladan dukkanmu..”

Batayi mgana ba. ta Wuce zuwa dakinshi,shi kuma ya tsaya suna gaisawa  da joda da maman Abba data Fito yanzu sai Zulai wanda dama Malika ta sanar dashi zuwansu,har dakin Malika ya shiga suka gaisa da Goggo hadiza yana mata godiya,Yana Fitowa dakinsa na yawuce yabar Sadiq zaune yana mai tsiya,koda ya Shiga dakinsa nasa,ya tarar da har Malika ta hadamai Ruwan wanka,Mamaki ta bashi yadda yaga cikinta ya tsufa dayayi mata mgana sai tace zai hanata neman lada,sai ya kyaleta bai samu lokacin yaba lalliinta da kitson ta ba,sai da yayi wanka yayi sallah yaci abinci kana,haka yadinga Sumbatar hannu yana Shafa kanta,nan take ya bata 5k yace tabama wacce tamata lalli da kitso,domin zahirin batu yagani kuma ya yaba.

   Sai wajen biyar na yammah yan kano sukayi Shirin tafiya,bayan sun gama jerama Zahra akwatunta sun mata yan nasihu duk da sun san baji zatayi ba,Nadira tayi kwaba tayi kwaban kamar bakinta zai Cire,ammh Zahra sai ta nuna taji,ammh kuma nan ko bata jin zata dauki mganarta,da zasu tafi sukace Zahra ta Fito su mika amanarta ga Malika,ammh sai zahra tace Allah ya kyauta tabi kishiya,sai dai in Malikar ta matsu ta shigo dakinta ayi mganar,ganin haka yasa babu wanda yakara bi ta kanta,da zasu tafi har dakin malika suka shiga don su gaisa lokacin tana dakin Saleem,sai da joda ta Fita taje ta kwankwansa musu ta kirata tazo suka gaisa cikin mutumci,daga karshe sukace ga Zahra nan kanwata take gareta,don Allah tayi hakuri da ita,su zauna lafiya da juna,don su samar ma mijinsu zaman da kwanciyar Hankali,sunji dadin yadda Malika ta karbesu sai sukaji ta burgesu sosai,domin ba haka suka samu lbrinta ba,domin ance bata da dabi”a sam,sai suka ga sabanin Tunaninsa,dazasu tafi haka sukayi ta sakamata Albarka da fatan Allah ya sauwaketa lafiya.

Sai da suka Fita haraban gidan kana Saleem ya Fito sukayi sallama ya basu kudi 3k sukuma Su joda suka Fito da Musu da kaji da meatpie da donout,din da sukayi musu wanda sukayi raping dinsu,suka basu suna ta godiya,Nadira dai mamakin ganin Malika take da ciki,don batajin ko Zahra tasan da cikin nan,don data sani da ta sanar da ita,Abun mamaki sai ga amarya acikin yan rakiya tana Rumgumesu tana daga musu hannu ammh Fuskarta babu alamun Rashin jin dadi ko Kuka ko damuwa,a’a fuskarta cike da Annuri.

Suna tsaye motarsu tatashi suka Fice daga  haraban gidan Zahra na daga musu hannu,sai alokacin taga Malika wacce datake bayan Saleem,sai yanzu ta Fito ta gefenshi gabanta ne ya Fadi ganinta da turtsetsen ciki,wani karin Abun takaichin ma hannayensu sarke dana juna suna mgana kasa,kasa malika ke sakin mirmishi Daga ganin Wata mgana mai dadi yake gayamata.

Duk da ahoto tataba ganin Malika bata zata afili tafi kyau ba,koda ita da datake amarya bazata Nuna ma malika kyau ba,duk da ko cikin jikinta wanda yake hanata kwalliya,Babu karya kyanta ya daki zahra sosai balle ma cikin dake jikinta wanda ko Saleem bata sanar da ita ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button