MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL
MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Itako Malika Tana kallon Zahra ne cikin ilimi da wayewa,daga sama har kasa,tabe baki kawai tayi cikin ranta batace komai ba,Ganin yadda ta kura musu ido ne yasa Malika tayi kokarin Fizge hannunta tana nuna mai Zahra da baki,dagowa yayi yana kallon Zahra wacce ta harde hannu akirji tana kallonsu Fuskarta babu Fara’a ko kadan.
Da Sauri Malika ta isa ga Zahra tana mata Fara’a tace”Sannu da zuwa amaryarmu…”Tafada tana bata hannu su gaisa,baya zahra tayi da hannunta tana ma malika wani kaskastancen kallo na Wucin gadi kafin ta mele baki tana Fadin”,Yauwa sannu dai buh found of correction Hajiya malika amarya Saleem kabir kumo kidaina saka min jaye..”
Tafada tana wani yamutsa Fuska kamar taga kashi,wani nauyi da kunya suka kama Malika ta sauke hannunta asanyaye tana mirmishin yake kafin ta kada kai kawai ta Wuce cikin tanajin yau fa kenan,? lalle akwai aiki ja agabanta game da amaryan mallam,Shiko Saleem waya ya tsaya yanayi wanda Sadiq ne ya kirashi yana sanar dashi har ya kusa isa garin Abuja motarshi ta samu mtsala,ammh zaiyi ma bakanikensa waya,shiko yanzu zai bi motar haya zuwa Abuja,so duk Abunda yafaru baida masaniya,yana kokarin yanke kiran ne yaga Malika ta wuce cikin gida,itakuma ta zahra ta matso inda yake tana mai wani kallo kamar ta lasheshi danye bai gasu ba
Tana karisowa kusa dashi ya yanke wayar yana binta da kallo,riko gefen hannunshi takama Tana Fadin”,Haba Honey Shikenan kuma tun jiya bankara ganinka ba…”Tafada tana saka kanta bisa kafadanshi,ganin megadi awajen karya dizgata yasa yadan riketa suna tafiya zuwa cikin gida yace”Ai yanzu ina tsammanin korafi ya kare ko? Tunda gaki gani,naga Yar Amanata taje kun gaisa,hop kin gaisheta da kyau Antynki kenan Malika Abdulmalik dankasuwa matata ta farko kuma uwar ya’yana..’
mganar ta zafeta Shiyasa ta tabe baki batace komai,shima ganin haka sai yaja bakinshi yayi Shuru,suna shiga falon suka iske Joda da Maman Abba,sunsaka hijabai zasu Fita da alama zataje gidan Maman Abba gabadayansu ganin Zahra rike da angonta Abun yabasu matukar mamaki sudai a al’adan bahaushe amarya tana kunshe adaki tana fargaban zuwan angonta,wasu ma saboda kunya ko siyan bakin akayi basu iya budeshi suyi mgana,ammh yau agidan Saleem suke ganin wani sabon salo,ai Tusa da lasifika????
Irin kallon da suke binsu dashi ne,yasa Saleem dan jin kunya yana kokarin raba rikon da Zahra tamai ammh taki sakinshi saima kara kwantar da kanta take bisa kafadanta,Girgiza kai kawai yayi yana basarwa nan sukayi sallama da Maman Abba,wai ashe Zulai da joda ta dauke zasuje gidanta su tayata kwana Abba da babanshi suna zaria wajen maman mijinta,Goggo Hadiza kadai aka bari,wacce duk kunya saleem ya takuramata tana cikin dakin Malika bata ko Fitowa falo,takuma gayama malika gobe da Safe zasu koma malumfashi insha Allah.
Har su joda suka Fice bata sakeshi ba bai sake mata mgana ba,illah hanyar dakinta daya nufa,sai da yabari sun Shiga kana ya Saketa yana kallonta kafin yace'”Wai miye haka…? Sakarni alwala zanje nayi na samu jam’i kema ki gagggauta yin naki sallar..”Tura baki tayi tace”Toh ina zaka? baga tiolet anan ba,ka shiga muyi alwalan tare..”Tafada tana kokarin kwantomai bisa kirji,ganin haka yasa yayi Saurin Fadawa tiolet ta biyo bayanshi sukayi alwala yana Fitowa yayi hanyar Fita tayi zaraf zata biyoshi ya waigo cikin haushi yana Fadin”Ina kuma zaki bini..Ehe..?
Diddira kafa tahauyi kafin tace”Inda zaka mana,don naga baka da niyyar sauken alqawarin dakama iyayena wajen kula dani da rike amanata…”,Tafada harda matso kwallar Karya,kansa ya dafe kafin ya karisa gareta ya riko hannunta yana Fadin”Injiwa… ? wayaga miki bazan kula dake,kinga ana kiran sallar mangariba,sauri nake naje na samu sallar cikin jam’i ko baki son ace mijinki yana kokarin yin sallar cikin jam’i..”Kallonsa tayi kafin tace”Ina so mana..”Da hanzari yace”Toh kibarni naje nayi na dawo,saurin mekike,yau ba tare zamu kwana ba..”,Da hanzari ta gyadamai tana Mai wani kallo,Sakin hannunta yayi yana gyara hulan dake kanshi yake Fadin”To kingani,oya Kema kiyi sallah asakemin wata sabuwar kwalliyan wannan ban Amince inci amarci da ita ba.,Sai na dawo..”Ya fada yana karisa Ficewa daga dakin,Sufa tayi ta haye kan gado tana Rumgume Filo cike da murna,cikin rawan jiki tatashi tayi sallar ta Tube kaya ta Fada tiolet tayo wanka akazo aka shafama lotion kafin abi kowani lungu da sako na jikinta da Turare,Wai saboda rashin hankalin zahra wai Tunda Saleem yace ta sake kwalliya to kwalliyan kayan barci yake Nufi batayi sanya ba ta bude akwatunta na inners ta zabo wata arniyar riga wacce tsawonta bazai gaza cinyarta ba,gata da budadden gaba,gata kuma raga raga,pant kawai ta sanya babu bara,sai ko gabadaya halittan kirjinta suka bayyana waje,tana kallon kanta amadubi tana jujjuyawa take fadin”Haba dole ya raina kansa in yaga wannan kayan,yasan nawa ba irin nata bane…”
Shiko Saleem bai dawo gida ba,sai da yayi sallar issha’i kana ya dawo,kuma koda ya dawo bai Shiga dakin kowa ba sai yawuce dakinsa yayi wanka ya sanya jallabiyansa Mai Ruwan toka kafin ya dauki wayarsa ya kira Malika yace tazo dakinsa ta sameshi yanzu,bayan ita sai ya kira Zahra yace itama tazo dakinshi ta sameshi yanzu,Jin kiran dayake mata sai bata kawo cewa harda Malika ya kira ba,ita atunaninta kila chan ne zasu first nigt dinsu????ai bata tsaya sauyawa kaya ba sai ta kara gyara fuskarta gyalen kawai ta yafama kanta,bata kuma Fito ba,sai da ta kada wani garin mgani tasha da madara kana tafito tana rarraba ido,ganin dakin daya ke hari dazu sai ta sa aranta nan ne dakin saleem din.
Da confident dinta ta Shiga,Cikin Siririyar Sallamarta,Turus tayi ganin Malika zaune akasa ta mike kafafunta,Shikuma Saleem yana rawan jikin jeramata Filulluka,bayan yagama yakoma mtsamata kafa,yana mata mgana kasa kasa,cikin ran zahra tace durun uwa Salatin Arna????????ita za”a torzata,tsaye kawai tayi hannunta bisa kugunta tana jifansu Da wani mugun kallo,Malika ce ta ankare da ita sai ta tabo Saleem ta nunamai Zahra,ganinta ahaka kafafu duk awaje yasa ya zaro ido????????Lokaci daya yana Fadin”,Zahra lafiyanki kalau kuwa..? Kinga yadda kika Fito marabanki da tsirara kadan ne..”
,Hhhhhh…Kuna bani dariya masu cewa kila Zahra ba budurwa bane,? waya sanar daku haka,? ai bance Zahra na bin maza ba,Nadai ce Tana da rawan kai da Iyayi da Feleki,Sai kuma rashin wayau dake damunta,in kun lura akwai irinsu Zahra sangartattu marasa wayau da badon ta samu jajircewan Uwa da uba ba,ga kuma Nadira dake kwabamata ba,da yanzu tafi haka Wauta itafa duk Abunda take yi gani take Shine zai sa Saleem yasota fiye da malika ya haukace mata,ita bata Tunanin tana kashe kanta ne,irin sune inda a kauye aka Haifesu da yanzu sun Fara Shiga Daji????????
Momyn ladingo..????
MALIKA MALIK…!
(Sai na rama..)
ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى ASSɷ????
Mallakar:Janafty????
25
“”Kwabe Fuska tayi tana wani kif-kifta ido tace”Kamar ya marabana da tsirara kadan ne? Yo inace bakai ka kirani ba,kuma laifi ne don mace tazo Turakar mijinta tana kama da Tsirara kamar yadda kace..”,Tafada tana jifan Malika da wani matsiyan kallo na zakiji ubanki ne,ke kikafi bani haushi.