MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL
MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Kafin Satin ta rame ta lalace kamar ba Zahra ba Saboda wahala,daka ganta duk tayi Zuru zuru kamar wacce take amai da guduwa,Gashi kullum cikin gashin kanta take,saboda yadda Saleem ya maidata,kuka ko da Nadama tayishi kamar ba gobe,ammh Saleem bai ragamata ba,sai ranar daya gama bakwai dinshi ya koma dakin Malika,kuma Abun mamaki dasukayi Making love da Malika bai Wuce akidarsa ba,lafiya lau komai ya Gudana,Shiyasa gwara ka tsaya inda Allah ya ijiyeka da kaje kana ma kanka jaye jayen banza wanda baida amfani,daya gama kwana biyunshi yakoma dakin Zahra da kanshi ya iza keyarta ta Fito da duka sauran magungunar matan datazo dashi,abun yakusa bashi tsoro ganin irin Abunda Zahra ke dirkama kanta,shi ya Fita da mgungunar ya jefar abola yana tir da masu hali irin na Zahra,bai sauraramata ba,sai da ya tabbatar da Nadamarta kuma tayi mai alkawarin bazata kara shan wani mgani ba,wanda ya Wuce ka’ida,to lokacin ya dagamata kafa,kuma ya taimakamata ta kula da kanta,don ba laifi ta zazzagu har sai da ya kaita wani priver hopt aka bata mganunguna tazo tana sha tana kara Shiga ruwan zafi,sai ga Zahra duk Rawan kafanta,kan Saleem yanzu ta dainashi,ada batajin tsoronshi ammh yanzu dataji muryanshi sai gabanta ya Fadi,domin ba laifi taji maza,ballatana yayi mata mgana jikinta na Rawa zaki ga ta mike duk bai kara waiwaryata ba sai da ta warke ammh tsoron Abun ya darsu aranta,kuma Abunda da zai baka mamaki,duk surutun Zahra ko Nadira bata gayama Abunda ya Faru ba,taja bakinta tayi shuru kada ayi mata dariya.
Kwana bibbiyu sukeyi atsakaninsu Ranar da Malika keda girki joda ce keyi,Ranar da Zahra keda miji kuma ita ke girkinta da kanta,don daga malika har joda ko kallo basu isheta ba,wani lokacin sai dai in sun hadu afalo ita malika ta gaisheta,ammh zahra sai kiga ta amsa a wulakance,Wani abu mamaki in tana da miji Malika bata isa ta zauna afalo ba,don Shige da Ficen zahra cike da gayyah da kuma nuna isa,Ba laifi ta iya girki Tunda momi bata barsu sun zauna a sangarce ba,shiko yanzu Saleem aiki yayi mai yawa baya Wuni agida Sai dare yake dawowa kuma daya dawo ya gaji sai barci gari na wayewa 7 ya fita daga gida,wani lokacin in bai dakin Malika sai dai ya Tuntubeta ta waya su gaisa yaji kodawani damuwa
Abunda Zahra kema Malika ya Wuce misali,domin in zahra na Falo tana kallo babu wanda ya isa yazo yadau Remot din ya chanza tasha yanzu zai ga hayaniya da bala’i,shiyasa malika in taga zahra na Falon batama Fitowa Joda ce ke Fitowa tace bamai hanata Fitowa Falo ta gaji da zaman daki,kai ko kichen take tana aikin da zarar Joda ta Shigo zata ce Ta fita,ta bari in ranar girkin uwargijiyanta ta Shigo,Malika ke kwaban joda ammh da yanzu Sun raba hali saboda Abun na Zahra yafara batama Joda rai gaskiya.
Hardai wata rana data bangaje Malika har sai ta kusa Fadi,Allah ya taimaketa ta dafe kujera gabanta na Fadi take bin zahra da kallo,takan kawai ta Fito daga dakinta ita kuma ta Fito daga kichen zata Shiga dakinta,ita Malika bata ganta ba,ita kuma Zahra ta ganta ammh saboda mugunta da Iskanci ta bangajeta,wanda yakusa joda ta mareta don datayi mata mgana cewa tayi ita malikar bata da ido,da bata ganta ba,Ran joda ya Fadi suka Shiga sa’insa har zahra na mata gorin tana agolanci agidansu Malika kuma tazonan tana cin arziki ita da gidan mijin,wlh ba macen data isa ta hana ta yin yadda taga dama,Ko ita Malikar ma atafin hannunta take,tana jiran Ranar zata Shiga sabgartane wlh sai tayi Nadama.
Malika bata bari Joda tayi mgana ba tattarata suka koma daki,tana ba Joda hakuri tare da Nuna mata kada ta biyema Zahra don abokin mutuwa take nema,so take wani Abu ya faru tsakaninsu in Mallam ya dawo tace kece baki da gaskiya,kinga kuma ba dadi ace baraka yafara bullowa daga Barayinmu ki kyaleta mu hayaniya ba aikinmu bane,shiyasa kikaga bana son zama ako’ina sai adakina gudun Fitina.
Koda Saleem yadawo Zahra takasa kunne taji ko zata wata mgana bataji ba,duk ranar ko ita kedashi,jin shuru bai mata wani mgana yasa tayi kyafci aranta tana Fadin”Gaskiyan Saleema ce datace ni na kyalesu,da sannu duk zakuji ubanku daga ke har wacce kike zaune don ita..”itako Malika koda Saleem ya shigo da Safe Cikin uniform dinsa yana Sauri zai Fita koda ya tambayeta koda wani damuwa ne,cemai tayi babu,gaisuwan safe sukayi kafin ya sumbaceta abakinta yafice yana Fadin”Sai ya dawo,addu”ar dawowa lafiya tayimai koda ta rakoshi har kofar dakinta sai taga Uwar gayyah zahra ta cakare rike da jakarsa Ta brief case tana wani Mele baki kamar wata mai jiran cas,tana ganinta ta juya takoma ciki tana Dafe cikinta dataji ya juya mata,tana cije baki don ita ko abaya batayi hayaniya ba,balle yanzu datake kan Siradin rayuwa da mutuwa.
Tunda Saleem ya Fita Malika bata Fito ba,sai bayan datayi sallar Azahar,ta Fito tadan mike kafa,saboda sun kara kumbura,kuma tun Safe maranta ke ciwo tana dannewa,Ko joda bata bari ta Fahimci haka ba,bata zata haihuwa bane,don saura kwana 2 EDD ta yacika toh bata kawo haihuwa bace,falon babu kowa,shiyasa ta zauna akasa bayan ta saka Filon kujera ta dafe bayanta dashi Rimot ta dauka ta chanza tasha zuwa Arewa,ta iske sun saka wani Film din hausa,mirmishi tayi domin ba laifin zuwanta zamfara yasa tafara kalle kalle wanda ada ba Halinta bane.
Zahra ce ta Fito daga daki tana waya har tazo ta takama Malika yatsar kafa ta kuma tsalleta ta zauna bisa kujera tana cigaba da wayarta,jaye kafarta Malika tayi tana sosa inda ta takata cikin wani yanayi ta kalleta,kamar zatayi mgana sai kuma ta Fasa,ta kada kai ta maida hankalinta wajen kallonta,chan taji zahra ta Sheke da dariya tana Fadin”Wane ita,ai ina gayamiki ita da banza duk daya ,darajan cikinta jikinta kadai takeji Honey yasanar dani da zarar ta haihu zai kalata gidansu taje chan sucigaba da zaman Kunci ita da matar ubanta..”Tafada tana watsamata harara ta gefen ido.
Gaban Malika ya Fadi tabi zahra da kallo tana mamakin kalamanta,Kanta ya sara tayi jagale tana kallonta,da gaske ne Abunda take fada ko karya ne,bata gama mamaki ba kawai taji an Fizge Filon kujeran data jingina dashi,Tayi Baya ta dafa kujera tana bin zahra da kallon mamaki,itako kallonta batayi ba,sai ma ta dora kafarta kan Filon tana cigaba da lasta Wayarta bayan ta katse kiran.
Wani Fushi ya ziyarce Malika cikin kakkausan murya tace”Lafiyanki kuwa..? Me Filon yayi miki dana tare bayana dashi zaki Fizge,naga dai kina da iko dashi nima ina dashi ko..? Wani kallon Uku Saura kwata kafin ta yatsina Fuska tana Fadin”Nafiki iko dashi Tunda duk inda matar so take itace yar gaban koshin megida..”Tafada tana daga zaune,Wani iri Malika datayi nan da nan hawaye suka ciko mata ido,ta dade tana kallon Zahra kafin kawai ta kada kai ta dafa kujera ta mike dakyar tana Share hanci,Ganin haka yasa zahra ta saka dariya tana Fadin”Ikon Allah jimin mace toh ke in banda Abunki meye Abun damuwa,keda kika ga rashin so zahiri,ai ba babban Tozarci sai mijinka ya sakeka adaren Da’aka Daura maka aure bayan yayimaka fatafata,meyafi wannan Wulakanci,kuma wai mutum saboda dakikanci yana zaton haryanzu ana Sonshi ne..”Tafada tana kara saka dariya.
Cak malika ta tsaya tana jin wani kuka na taso mata daga kasan rai,juyowa tayi tana kallon Zahra kafin tace”Duk wa yagaya miki wannnan mganaganun dakike jifani dashi..?”Bude Zahra tayi kafin ta mike tana Rike kugu tace”jiki da wata mgana,wazai gayamin banda honey,Tunda shi aka cuta aka tilastama sai ya maidake dakinki,ke in ma zaki daina rawan kafa ki daina wai ke gaki uwargida bayan da bakinshi ya Fadamin tsausayinki yake babu Uwa asali mai kyau Tunda dangin Arna ne,uba kuma anyi Sanadiyar Shekawarsa da bakinciki,kinga ko ai inda imani ke abun atsausayane ga kuma ciki kinga sai ajira ki haife kafin kiyi gaba..”Tafada kai tsaye tana kallonta.