MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Gabadayansu suka razana da jin zencensa saleema data tura chips abaki sai da ta Furzoshi waje,Shiko Ya marwan,yakafa kai yana kurban coffoe,sai da ya kware yafara Tari sama sama,Ummi dake zaune sai da ta mike hannunta dafe da kirji shiko Abbi kasake yayi yana Bin Saleem da kallo,wanda yayi saurin boye razanar daya ga sunyi Afuskarsa.

Saleema ce cikin Rudani tace”Ya saleem Wai wakake Nufi..? Kai tsaye yace mata..” MALIKA MALIK..”…Da ita da Ya marwan sai gasu tsaye suna zaro ido atare suka Furta..”,Bura uban chan…”

Suka Fada suna kallon Saleem kamar wani tababbe,Hajiya datake nazartansu tace”Kai wai miye haka daga Fadar suna,kun shiga Rudi lafiya meyake Faruwa ne..? Ya marwan ne yace”Komai ma yafaru Hajiya bakiji sunan daya Fada bane..?Tabe baki Hajiya tayi tana Fadin”Wannan bai dameni ba,indai yar gidan mutumci ne,Amemasa aurenta Tunda yana Sonta..”

Wani kallo Ya marwan,ya ke Wurgama Saleem,wanda yaki bada damar Ya kalleshi balle ya Fahimci wani Abu,To waima yaushe Saleem yataba haduwa da Malika,yarinya da Da Namiji ma baya gabanta? Bai gama mamaki ba yaji saleem na Fadin”Nidai hajiya gashi na kawo wacce nake so don Allah ki matsawa Abbi yaje gun mahaifinta ya neman min Aurenta,kuma one anoder thing,don Allah Abbi karka sanar dasu Aikina,ka sanar dasu ina aiki da hukumar costome ne,in komai ya daidaita zan sanar da ita dakaina plz Abbi..”Yafada yana hada hannuwansa kafin ya Ture hannu Hajiya dake Rike dashi ya Nufi hanyar dakinsa da sassarfa Saleema da ya marwan suka bishi da kallo baki sake.

Hajiya ce ta kalli Abbi,wanda yacigaba da karya wasan tana Fadin”Kabiru maza ka hanzarta,Tunda daga jima kasan mahaifinta Tunda kaima babba ne agwannatin,Tunda har ya nuna yanaso to gwara agaggauta yimai kaji ni ko bakaji ni ba..?”Batare dawani Tunani ba Abbi yace”Insha Allahu hajiya zan kira mahaifinta awaya mufara mgana dashi abokina ne,tare mukayi Dan Fodiyo dashi ammh bayan mungama Zumunci yayi Rauni..”

washe baki Hajiya tayi tana Fadin”Kajima ko,to maza kabar zencen kira zuwa zakayi don wannan mganar bata waya bace..”Gyada kai yayi yana Fadin”karki damu hajiya komai zai daidaita..”Hajiya na murna tana ta sakama Abbi albarka,Ta mike tana kallon Ya marwan tace”Andai ji kunya babban banza,har kaninka yafika sanin ciwon kansa,kadai je,kayita yawo a iska haka zaka zo ka koma,wlh in ka mutu,ana sadakan uku zan saka asallami kowa,daganan kowa ya manta dakai,Tunda ba wani mgaji gareka ba,balle akalleka Atuna ka”Tafada tana Wucewa rai bace.

Ummi dake zaune takalli Abbi tace”Yallabai kako gane wata yarinya Saleem yake mgana..? Hannu yadagamata yana Fadin”mubar wannan mganar Aisha zamu tattaunata letter..”yafada hankalinsa kwance.

Ajiyar zuciya Ummi ta sauke kafin ta mike tahaye sama ranta bace,Saleema tabi bayanta aranta tana Fadin”Lallema ya saleem,ya daukoma kansa dala ba gammo,inma ta yarda zata aureshi don ita ko Qur”ani aka bata zata dafa ta karyata Cewa Ya saleem da malika malik suna soyayyah macen da bata san Darajan kanta bama balle hartasan da wani..”Saleema tace afili”kilama ta girmeshi wlh, yarinya kamar arniya wacce bataga Ruwan musulunci ba”Tafada tana bin bayan Ummi da Sauri taje tasanar da ita kamar ta wahalar da kanta bazai samu damar Auren wannan yarinyar ba,.

Shiko ya marwan bayan Saleem yabi koda yazo dakinsa sai ya tarar da ya rufe da key,jinjina kai yayi yana fadi Cikin Ransa”Ka Rufe kan ka mana,Tunda karasa wacce zaka Furta zaka aura ko wasa ne,sai wannan watsatsiyar yarinyar..”Yafada yanajan tsaki ya wuce dakinsa,yana ayyana tabbas akwai yarinya haryanzu Atare da saleem….

Ammh ta hanyar nuna min kauna da soyayyarku wajen Siyan MALIKA MALIK Akan Naira 200 kachal????,ta wannan account Nombar, *0552179550 JAMILA UMAR GTB,sai ki Turo Shaidan biya ta wannan nombar *09069067488* ko kuma katin waya na MTN,shima sai ki Dauki hoton katin aturo kai tsaye ta wannan Nombar 09069067488 Sai kun zo ina maraba daku masoyana..

Karku manta da garabasanmu mai son Siyan Biyu KISHIN MATA,na HAFNAN,300 ne kachal????shima zai iya Turo ta nombar bankin dana bada ko katin waya na MTN ta nombar saman dana bada, ko kuma kai tsaye ku Tuntubemu ta wadannan Nombobin domin karin bayani

07065481260..Ko kuma 09069067488

Janafty..

????MALIKA MALIK????..!
(Sai na rama..)

ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى ASSɷ????

Mallakar:Janafty????

Free Page

4

FLASH BACK

  
  “”IGP KABIR KUMO Shine asalin sunan mahaifin Saleem,wanda ya kasance haifaffan garin gombe ne, a KUMO babbar hukumar AKKO LOCAL GOVERMENT Kabir ya fito daga gidan mutumci da tsatso mai kyau da Asali,family dinsu basu dawani yawa sosai,ammh suna da kudi dayake suna da manyan yan boko sosai kama daga Doctoci zuwa sama.

   Sunan mahaifinsa BASHIR,Wanda ya kasance Lacra ne,a babban jami”ar gombe kafin Allah yamai Rasuwa ya rasu yabar matarsa HAJIYA HAFSAT da Da’nsa kabir,wanda yake aji uku ababbar jami”ar Usmam DanFodiyo Universtiy Sokoto inda yake karantan Sciology Sanin Hallayyar dan Adam kenan.

Mutuwar mahaifinsa ta girgiza sa ammh haka ya fauwalama Allah komai ya maida hankalinsa akaratunsa,Shigansa jami”ar ne suka hadu da *ABDULMALIK SA”AD wanda shi yake karanta Business Admistration,ammh dayake hostel dinsu daya yasanya sukayi abota sosai Duk da shi Abdulmalik din dan jahar katsina ne akaramar hukumar MALUMFASHI.

  Kammallah karatunsu shiyayi sanadiyar raba zumuncinsu domin Shi kabir daganan Burinsa dama Aduniya ya ganshi yana sanye da kakin YA’N SANDA,nan da nan yasamu nasarar Tafiya POLICE STAFF COLLAGE JOS PLEATUE makarantace dake horar da manyan ya”n sanda mussaman wadanda aka dauka daga matakin Degree,shekara daya yayi ya Fito amtsayin ASP

  lokacin ne,kuma yayi Aure da yar”uwansa AISHA,Wacce ta kasance diyar wan babanshi ne uwa daya uba daya aka hadasu zumunci lokacin itakuma tayi candy,sai ya taho da ita nan ZARIA inda akayi posting dinshi,har yayimata cuku cuku ya sanyata a ABU Kongo,tana karantar Sharia Low,Shekaranta biyu tagama lokacin kabir yasamu chanji wajen aiki,zuwa kano suka tararra suka koma inda tadora daga Karatunta a low sch kano,Shekararta ta Farko Allah ya azurtata da ciki,inda ta Haifi danta na Fari  Wato MARWAN Shekaran Marwan biyar Aduniya ta sake haihuwan Danta na Biyu Wato SALEEM Lokacin kuma Kabir yana matsayin DEPUTY COMMISSIONER OF POLICE Na jahar katsina.

Sai da Saleem ya shekara Hudu Aduniya kana aka haifi SALEEMA wanda daga ita Allah bai kara bata haihuwa ba,kuma bawai don ta tsayar ba,Allah ne ya tsaidamata,Tunda daga ita har kabiru,suna bukatar ya”ya sosai atare dasu lokacin ta kamallah karatunta na low school ta Fito da sakamako mai kyau sai Kabir ya nema mata aiki ababban kotun jaha dake katsina nan da nan tafara aikinta amtsayin Lauyan gwannati.

Tun Marwan na dan karami yake da sha”awan Zama matukin jirgin sama wato pilot,shiyasa yana gama secondry sch dinsa Iyayansa suka Turasa Kasar Russia,domin karantan Abunda yashafi Tukin jirgin sama,wanda zai dauki kimanin shekaru biyar achan,lokacin Saleem da Saleema,duk suna Nagerian Turkish Acadamy Abuja,Saleem na jss2 ne,Saleema na primary 4,ko lokacin tafiya Marwan Hajiya hafsat mahaifiyar Kabir taso ta nuna gaddama ammh iyayan suka lallasheta suka nuna,kamar yadda suka gini da boko to suna Fatan suma iyalansu sun san ilimin Addini hade dana boko,wanda malami na mussaman garesu,mai koyar dasu karatun Addini,Saleem dai ya sauke alqur”ani Tuni,Sauran littafai yake bita yayinda Marwan yasa wasa har kaninshi yazo yawucesa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button