MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Saleem baida masaniyar Abunda ke Faruwa,don baya zama agidan in yafita Tun safe sai dare yake dawowa,kuma babu wanda ya Sanar dashi ga Abunda ke Faruwa,wanda Wuni suke suna zaune afalo suna Hiransu suna dariya,ko ajikinsu kuma adafa abasu suci suna wulakanci,Malika ko tana cikin damuwa bata cikin natsuwarta saboda ita harga Allah Ta yarda da mganar Zahra tana cikin Fargaban in Mallam ya saketa ya zata kare da rayuwarta,ammh ta gagara fadama kowa ta bar Abun acikin ranta.


Ranar bakwai din na zagayowa Ranar akayi suna jaririya taci sunan Ummi Aisha suna kiranta AYDA,Anyi sha’anin cikin Farinciki da murna,yan malumfashi sunzo harda yan Kumo ma sunzo ansha suna,wanda Su joda sukayi abinci kala kala agidan maman Abba,sun dafa white rice da Miyar nama,sai friede rice da Kuma jallof mai Cosslow,sai Soyayyan Naman kaji dana rago,Sunyi kunun aya,Sai alale na leda,wanda yaji kwai,kuma bayan lemukan da Saleem yasa aka sauke musu domin baki,Kuma su kadai sukayi duka aikinsu agidan Maman Abba,sai dai suka kwaso su cikin manyan kololi suka dawo dashi nan gidan

Malika ta Shiga ta Fita cikin kayan alfarma ita da Ayda,musamman maman Abba ta sake kiran Ummi mai lalle da kitso ta sake cakareta,bayan nan mai kwalliya tazo itama ta tsantsaramata kwalliya Abun sai wanda yagani,dayake simple make up ne tayi mata,sai ta Fito ras da ita,Abunka ga farar fata,dama gata da kyau ai sai kawai tashiga kyalli,Zahra ko da Saleema kamar su mutu saboda bakinciki domin ko sun sani wlh karfin hali kawai suke,ammh Malika tafi karfinsu dukkansu,domin ta Wuce da saninsu ta bangarori dama,Ranar sai ga Hajiya saratu momi da Nadira sun diro sunan wanda suka zo suna ta ma zahra Fadan bata sanar dasu malika ta haihu ba,nan tayi ta borin kunya tana Fadin wai ta kira wayarsu bata samesu ba,Nadira ce tace sunyi waya da Saleem yake sanar da ita jiya,yace kuma yau ne Suna,shine ta Fadama momi suka taho,duk da basu wani dade ba,ammh ko malika da basa shiri da zahra taji dadin zuwansu da zasu tafi momi ta bata 10k da kuma Atamfa guda biyu da kayan babys,ko Saleem basu gani ba,don Tun safe ya Fice sakon gaisuwa kadai sukabari agaya mishi.

Taron sunan baiyi wasu jama’a sosai ba,daga yan malumfashi ne sai yan kumo,wadanda suma suna gama cin suna suka koma,dama sunzo da motar gidane,sai yan group din MALIKA MALIK PAID Da yan HAFNAN AND JANAF PAID GROUP Da sukayi mata kara mota guda suka zo ma malika sunan Ayda wanda ta dinga mamakin daga ina suka samu lbrinta,nan Dotata Ladingo tayi dariya kafin tace”Karki damu da sanin ina muka samu lbrinki,domin mommyna Janafty ita take sanar damu lbrinki,kuma dukkanmu nan masoyanki ne,duk dabamu taba ganinki ba,muna kaunarki..”Jin haka yasa malika tayi murna sosai da Farinciki nan aka zubo musu abinci suka baje suna ci suna hira,su Sisina Aisha alto da Sahiba sai ci ake hannu baka hannu kwarya????su mommyn Abdul me,su Rafi’atu,Fati sadi,mommyna khadija tame gari,momyna khadija bashir,Dijah Abdul,Dija muhd,Zuwaira Andijat,My besty halima,Fatima zahra,haleema,Ummi imran, Mmn useey,Ummi bilal,Fatima garba,mom sadiq,Suwaiba,shafa yola,Murja bagudu,Deejart,Mmn baraka,Mmn Amira,mm siyama,Ummu bilal2,Rouky niger,Azeeza,hadiza,Durling Rukayyah, Masoyiya takwarar malika,khadija Aliyu,khadee Noor,mmn Haneef,Mmn mama,yar Fulani,Nazeeha Ahmed,Saleema Hamza,Ayshert usman,Maman khairat,Bbyj,Asma’u Shehu,Ummah sabo,Zainab jega,Hafsart Umar,Fatima musa mamn Nabila,Mmn ummulos,Nafeesa Fee,jikar hajiya,Mrs Umar Faruk,Sardiya,Suna da dayawa wanda bakina bazai ya ambatonsu duka ba.

Sunsha Ankonsu cikin red din materila sunyi head da blue,abun sai wanda ya gani,malika tayi Farinciki ganinsu sosai haka sukayi ta daukan Hotuna suda malika da bby Ayda,Fatima zahra ko ana riketa tana abarta ta Shiga dakin Zahra taci ubanta????????Dakyar Su Nazeeha da Ummi imran suka rirriketa suna bata baki kana ta hakura,Har sukayima Malika sallama bayan sun bata sha tara na arzikin da suka kawomata ,basu saka Zahra da Saleema a ido ba,ammh d Yawansu sun so su gansu koda tsaraban Harara ne su basu koda bazasu dake su ba,Saboda murna da godiya har bakin mota joda da Malika suka rakosu suna musu godiya suna dagama musu hannu har suka Fice daga gidan.????

Anyi taro lafiya an watse taro,Ayda da mamanta sunyi goshi matuka domin Abbi 50k ya aikomata dashi Ummi ko akwati tayi Sir da kayan Babby da mamanta balle dataji ita akama takwara,Ya marwan ko Shima kayan yara ya turo dashi daga lagos,da kudi 30k akabama malika,haka shima Sadiq kudi yabata 20k Malika saboda Farinciki sai da tayi kwallah ta kira Abbi da Ummi tana musu godiya tana kuka,harta da Sadiq din da Marwan Saleem ya kirasu yabata tayi musu godiya sukace ai babu komai suma yarsu ce,Su Zahra da Saleema ba karamin mamaki sukayi ba da sukaji uban Dukiya da kayan da malika tatara,nan da nan hassada da haushi ya kamasu,nan Zahra taji itama tana son ta samu ciki itama ta haihu ataramata kudi,Niko nace banza abanza,ke keta Dukiya indai kudi ne Malika ta mallakeshi da wanda zai siyeki keda Mai zugakin gabadaya.

Shiko Uban gayyar bai siyan mata komai ba,illah wata sarkan gold mai kyau Sarka da Dankunne,Ranar daya kirata ya damkamata sarkan adakinshi ne,yana rike da Ayda ita kuma malika na Faman gwada sarkan gaban madubi tana washe baki murna ta cikata Fadi take”Wayyo Mallam wht a special gift,gaskiya am so hppy wlh Allah ya saka da alheri ya kuma rayamana Ayda cikin tafarkin islama..”Da Ameen ya amsa yana mata dariya Abun yayimai dadi yadda ta nuna murnanta afili,domin yasan cewa Malika ta mallki dubunsu kafin yanzu kuma ko ayanzu tana da Dubunsu ammh kalli yadda take murna akan kyautan da yayimata wacce bata Wuce yarwa abola ba indai awajentane..

Kwantar da Ayda yayi bisa gado ya taso yazo ta bayanta ya Rumgumeta duka kyakyaawan Fuskokinsu suka bayyana acikin madubi,mirmishi take sakin mai bayan ta dora hannuwanta kan nashi,cikin wani salo yayi mata Rada akunne yana Fadin”Ummi Ayda..”yafada yana Shinshinar Wuyanta Cikin kasalar daya saukarmata tace”Umhmm Abbu Ayda..”Mirmishi yayi har Hakoransa farare suka bayyana,Cikinta ya mtsana tayi yar ihu tana Fadin”Kai mallam wajen operation din nefa ka tabamin..”Tafada cike da Shagwaba Saurin juyo da ita yayi yana Fadin”Ayyh am srry..”Ya fada yana shafa kumatunta,Kafin yace”Tambayarki zanyi,kuma ina so ki sanar dani gaskiyan al’amarin..”

Hannayenta ta harde bisa kirji tana Fadin”yes ina jinka,Allah yasa na sani..”Gyara Tsayuwa yayi yana kallon cikin kwayan idanunta Yace”Mganar dakikamin a asibiti kince kada na sakeki sai mun dawo gida? waya sanar dake cewa nace zan sake ki bayan kin haihu..? Shuru tayi tana dukar dakai taki mgana,Ganin tayi Shuru taki mgana yasa yace”Kinga ki sanar dani waya gaya miki wannan mganar da bata da Tushe ballatana makama,in baki gayamin ba,zan kira goggo Hadiza yanzu,kila ita in ta tambayeki ki sanar da ita..”

Jin haka yasa ta riko hannunshi da Sauri wanda yake Shirin Fita,bisa gefen gado suka zauna kafin tace”Basai ka sanar da kowa ba,Bani son Tun bayan daidaitan al’amarinmu babu wanda ya sakejin kanmu kai baka alfahari da hakan..? kai ya gyada mata bai yi mgana ba,Sai tacigaba da cewa”Toh meyasa zaka kai karata? dama zan sanar dakai Wacce ta Fadamin ammh sai kamin alqawarin bazaka dau wani mataki ba,kowani hukunci ba..”zuru yayi mata da ido yana kallonta kafin yace’Banyi alqawarin ba,ammh ki fara sanar dani Abunda ya Faru..”,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button