MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL
MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Yana huci da Numfarfashi yake Fadin”Saleema,Zahra dukkanku Babu Abunda zence muku sai nagode da sakayyar ku gareni,kunyi ikirarin zaku kori Malika daga gidan daku kukazo kuka tarar da ita,to Alhamdulilah kafin ku koreta ku bari ku Farayin gaba,Zahra wlh nayi nadamar Aurenki saboda haka kije na SAKEKI SAKI DAYA,…”Malika ta kwalalo ido,goggo Hadiza ko Fadi take”Assha Ashha..Saleem hukunci yayi Tsauri..”
Hannu ya daga yana Fadin”goggo kibarni,wlh aurenta ya Fice daga kaina,dama kuma kadarrace ta sani aurenta bawai don ina jinta acikin zuciyata ba..”Yafada yana huci Zahra ko hannun ta daura bisa kai tana Fadin”Wayyo Allah na Shiga uku ni Zahra Fatima,don Allah honey kamin rai kada ka rabu dani..”Take Fada tana kuka,tsaki yaja kafin yace”Dallah Rufema mutane baki sakarya Wawiya kawai,ke har kina da bakin yima malika gori akan bana Sonta,kin ma san miye so,Toh bari na gayamuku Abunda banta gayama kowa ba,ko gabanki kike wankewa kibani wlh bazaki kamo mtsayin malika acikin Raina ba,in kince zaki kishi da ita,sai dai ki mutu wlh don bazaki taba samun mtsayin data samu ba,saboda haka ki tararra ina inaki kibarmin gida ki koma gidanku ki kuma Sanar da iyayenki wajen Gudirin koran kishiyane Reshe ya juye da mujiya,ke kuma…”Yace yana nuna Saleema da hannu.
“Kin kyauta in kuma nuna min Cewa kedin kin Fita Dabam acikin ya’yan Ummi da Abbi,shegiya mai Fuskar alade ki rasa inda zaki zo kiyi munafuncinko da gulma sai gidan Dan”uwanki harkina bada goyon bayan ayima matar dan”uwanki wulakanci Saboda mugun Halinki,baki Tunanin kema wata rana gidan wani zaki,ko don kina ganin Sadiq bai da kanwa baki Tunanin yana da ya’yan yan’uwa..? kema za’ayi miki haka? ya zakiji? ko kuma ayima yar da zaki Haifa zaki so..? Amsan ita ce A’a ammh kuma kike kokarin cima wata Zarafi agidan Mijinta,wlh Saleema Tir da munanan Halinki kema ki tararra kayanki ki barmin gida yanzu ba sai anjuma,kuma yanzu zan kira Ummi da Abbi na sanar dasu Abunda kika aikata,in kin koma chan ma kikara amsan hukuncinki,Dabba kawai wacce batasan nata ba..”Yafada yana Shureta da kafa kafin ya juya afusace ya Shige dakin yana banko kofa Ranshi bace kamar Zuciyarsa zata Fito waje.
Malika ce tabi bayanshi Da Sauri tana zuwa jikin kofa tajita akulle gam,baya ta dawo tana Dafe kai,Joda ko dake Rike da Ayda cikin Towel,ta fara Dariya kamar cikinta zai kulle,Zahra da Saleema da suka ji jiki,suka bita da kallo idanuwansu jajir,kowacce Fuskarta ta chanza Saboda Wuya,Saleema ta fara Ture Zahra wacce ke kan Kafadanta tana kuka,dagowa Zahra tayi tana kallonta cikin bacin Rai take Fadin”Allah ya isa tsakani na dake Saleema,gashinan wajen zugani na Raba Malika da honey ni kin kashemin Aure..”Tsaki Saleema taja Tana mikewa dakyar take Fadin”Allah ya isa ta biki munafuka,daman chan da ra”ayinki na ganki da baki da mugun Nufi akanta dana kawo Shawaran ai ba Dole nayi miki ba ko? Tafada tana mata wani Wulakantattacen kallo,ganin haka yasa Zahra dingisawa ta mike tana cakumo wuyan Zahra tana kuka take Fadin”kece ai munafuka Komin mugun Nufina inda ban samu goyin bayanki ba,da bazan iya yi ni kadai ba,Ammh saboda rainin wayau bayan kin kashemin aure,shine kike Fadamin mgaanar banza,Ran Saleema ya baci ta kalli Zahra tana Fadin”Sakarni don uwarki…”Baki Zahra ta rike tana Fadin”Lalala..Har da zagin Uwata,to anki asakeki din don uwarki kema,Tunda uwa batafi uwa ba..”Jin haka yasa Saleema ta Fizge riganta daga hannun Zahra tana Fadin”Andai ji kunya wlh,Ni sai yanzu nake nadamar biyemiki Domin Tun Farko na gane ke Shashashace..”Tafada tana hararanta kafin ta Shige dakin Zahra tana Sosa bayanta inda belt din ya Shigeta dakyau
Kukan kura Zahra tayi tabi bayanta tana Fadin”Kutumar ubanchan To Fitomin daga daki..”Daga cikin dakin Saleema ke bata amsa da Cewa “Dakin ki ko dakin Yaya Saleem,don ko banza ni ina da gado agidan ko yau ya Saleem ya Fadi ya mutu,ke fa.? Saki ne fa akanki kinga ko baki da wani iko da dakin nan..”Nan suka Shiga suna zagin junansu da cin mutumci,Malika ta rike bakwai aranta tana Fadin”Lalle Zamanta zamafara yasa ta Fara karatun Duniya,Joda ko goggo Hadiza daki suka koma suna fadin Allah Shi kyauta,dama Ramin karya kurarrene,kuma dama haduwar abota indai ta munafunce bata karfo,kuma indai tatashi Rabewa bata rabewar arziki.
Haka kowacce ta Fito dauke da katon akwatinta da mayafinta bisa kai,har suka Fice daga gidan suna tsiya taku da tona ma juna asiri suna zage zage kamar zasu daki juna,koda suka isa tasha suna tare,kuma da Saleema ta hau motar Abuja,itama Zahra nan ta Shigo nan Saleema ta kalleta tana Fadin”Ke mara Mutumci ina zaki danaga kin Shiga motar Abuja..”?
Zahra bata tankata ba Sai da taja mata wani dogon Tsaki kafin tace”Kina da son bata bakikin,aikwai inda zani wanda ya Wuce gidan iyayen Mijina,chan zani muje kowa ya maimata Abunda ya aikata nabama Ummi hakuri na Roketa ta Roki Honey ya maidani dakina,don ni dai ko giyan wake nasha bazan koma gida ba..”Baki Saleema ta bude kafin tace”Bazan taba bari ki koma gidan Ya Saleem ba Zahra,domin dama chan baki dace da yayana ba Malikar dai itace ajinsa…”Baki Zahra ta mele kafin tace”Daga baya kenan,wai anyi Sadaka da karuwa,kanki kuma akeji yanzu..”Tafada tana juyama mata keya,har mota tatashi suna Tsiya har sai da wata mata dake ciki ta musu mgana kana suka Saurara.
Shiko Saleem dama yana Shiga dakinsa Bayan ya kulle kansa,bai kira Ummi ba sai da fushinsa ya Fara sauka kana ya kira Ummi yana gayamata Abunda ke Faruwa kamar yayi kwallah,Ummi da Ranta ya gama baci da jin Abunda Zahra ta aikata kuma Abun haushi harda Diyarta Saleema cikin Fushi da takaichi tace”Ina Fatan kaci uban Shegiya ka barta kwance ko,…?”Yace”Nadai mata hukunci Ummi buh ita Zahran na Saketa gaskiya Ummi,bazan iya zama da ita ba wlh..”tsaki Ummi taja kafin tace”To waya kwasota ai ni dama Tun ranar dana Fara ganin idon yarinyarnan nasan akwai zence,Allah ya kyauta in ta yi hankali sai kadawo da Matarka..”Shuru kawai yayima Sukaci gaba da mgana,nan yake Tambayanta Abbi don yace ya kira Nombarshi bata,nan take sanar dashi yana meeting da Shugaban kasa,sun dade suna mgana da Ummi kafin kowanne ya yanke kiran.
Da Ummi take Fadama Hajiya Abunda ya Faru mamaki da Haushin Saleema ya kamata,tayi ta sababi ita kadai,harta Fadin bari kabirun ya dawo azo ayi mganar aurenta kawai Da Yaron nan Sadiq,tun bata da mutumci,Zuwa yammah kuwa sai ga Zahra da Saleema sun Diro,Ummi takaichi kamar ya kasheta,ganin yadda Zahran ke kukan munafunci,ko dayake bata ga laifin Zahra ba,babu babban mai laifin irin Saleema,Ummi tayi Fada kamar ta daketa,haka Hajiya babba Ta nuna mata abunda tayi Rashin kishin kanta ne,domin har Abada Saleem dan”uwanta ne,Dakin dai Saleeman Zahra ta sauka,ammh ko mgana basu ma juna,Ummi tace ta jirata zuwa gobe suyi mgana da Abbi,Abbi koda yadawo Ummi ta sanar Shuru yayi yana maimaita Sunan Saleema,Ummi ya sa ta kira masa Saleeman yayi mata Fafata yaci Mutumcinta sosai kuma yace maza ta Shirya kayanta a Asibitin Mallam Aminu kano zatayi Housemanship dinta,Saleema tayi kuka da Nadamar dama bata aikata Abunda ta aikata ba hakuri tayi tabama Abbi,ammh yace wlh chan zata,kuma mganar aurensu da Sadiq kwananan zata tashi,bazai zura mata ido tana bin gidan Dan”uwanta tana Assasa rashin zaman lafiya atsakanin matanshi ba.