MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL
MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Ummi ko datayimai mganar yasa baki Saleem ya maida Zahra dakinta,kiyawa Abbi yayi yace mata dama Tun mganar Auren Zahra ya yayi alqawarin bazai kara shiga Sha”anin gidan Saleem,ta barshi shima magidancine,kuma hukunci da yayanke Shine Daidai gareta,ganin haka yasa Ummi ta nemi izininshi gobe in ta dawo daga court don tana da wata Shari’a zata saka Zahra agaba ta maidata Zamfara,Tunda ta nuna tayi Nadama,Bai damu ba yace adawo lafiya.
Saleem bai saki Fuskarshi ba sai da gari ya waye kana ya fara warwarewa,ammh itama malikan tasha Fada,Akan meyasa in Zahra tayimata wani Abun bata sanar dashi,toh meye amfanin ta amtsayinta na Uwargida,kuma yayimata Fushin yadda ta nemi ta yarda da kalaman Zahra na cewa zai saketa,ya sanar da ita in har zai saketa ai ba Tsoronta yakeji ba dabai Fadamata ba,Ita dai Malika nata ban hakuri da kuma mai alqawarin insha Allahu haka bazata kara Faruwa ba,bai saki ba Fuska Sosai don Ranar ko breafast baiyi ba ya Fice zuwa wajen aiki,Ranta duk ba Dadi don bata son wannan Saleem din nata tafison Abu Ayda na yanzu yafi dadin zama da Dadin Sha’ani.
Dukkansu basu san da Zuwan Ummi ba,sai gashi wajen karfe 1 sai ga Ummi da Direba tazo tare Da Zahra,haka Malika ke rawan jikin Tarban Ummi,ita kuma tana Fadin tazo ta zauna jego take,Sai bayan su gaggaisa ne da Malika da goggo Hadiza da Joda,Tunda tazo Ayda na rike a hannunta Zahra na gefe ta rabe kamar wata mutuniyar kirki da akwatunta agabanta,Ummi ce ta tambayi Saleem,Malika tace yana wajen aiki,waya Ummi ta Fito dashi ta kirashi tace yazo gata agidanshi tana jiransa yanzu zata Tafi ne,bai jima ba sai gashi yazo Fuskarshi ta kara Dinkewane lokacin daya cikaro da Zahra,cogewa yayi yaki zama yana Fadin”Ummi dama wannan munafukar gida taje,ke Abuja nan ne gidanku da zaki tafka hauka miji ya sakeki kuma kije chan.? ya Fada yana kallon Zahra cike da Tsana.
Ummi ce ta dakatar dashi Da Fadin”Saleem zo ka zauna bani son Shanshancin naka..”Jin haka yasa yazo yazauna akasa akusa da ita yana gaisheta,ganin haka sai Malika tatashi zata Shiga ciki,sai Ummi ta kirata ta dawo ta Umarceta data zauna domin mganar ta Shafesu dukkansu ne,dama Joda da goggo Hadiza tunda suka gaisa da Ummi suka koma daki,Kafin Ummi tafara mgana sai data fara Rokon malika gafara bisa Abunda Salema da Zahra suka aikata gareta,Kusan Malikar Taku da Sanyin Hali nan da nan ta yafe musu dama bata Rikesu ba,Ummi taji dadin haka harsai da Ta nuna afuskarta,Bangaren Saleem kuwa sai da Ummi ta Fitomai a uwa sak kana ya yarda ya yafema Zahra har ya maidata dakinta,ammh ya gayama Ummi da Sharadi wlh tallahi last chance ya bata in takara duka Sakin biyu zai cikasa mata,Nan Ummi ta yarda bayan ta sa Zahra ta duka tabama Saleem hakuri,shi kuma yace bazai hakura sai inda Ta Roki malika ta yafemata tukunnah,don ita suka batamawa,Dole Zahra tabama Malika hakuri ba don Ranta yaso ba,sai don Tsira da Aurenta datake matukar So,malika batayi gaddama ba tace ita bata taba kallonta da wani Abu ba,taje ta Yafemata,Ummi taji dadi sosai nan ta tarasu tana ta yi musu Nasihan zama lafiya da Hakuri da juna,kafin daga karshe tayi ta sakama Malika da Saleem albarka tana bayyana yadda suke alfahari dasu.
Ummi bata tafi ba sai datayi la’asar ammh kafin tatafi sai da takara jan kunnam Zahra sosai,ta nuna mata taji kuma insha Allahu itama zata zama mace tagari kamar Malika,Ummi kuma dazata tafi ta Shiga har dakin Malika ta damkama wani Abu abakar leda tace zata kirata awaya ta mata bayani karba Malika tayi tana ma Ummi godiya,Dole Ummi ta ijye Ayda wacce take nanike da ita Tunda tazo ammh tadaukan ma Abbi sabuwar Amayarshi hotuna,don ta kara Nunamai yadda Ayda takara girma,har bakin mota suka rakata ita da malika suna dagamata hannu har motarsu ta Fice Daga get din gidan.
Suna tsaye Saleem ya juya zai koma cikin gida Malika ta riko hannunshi tana kallonshi bai kalleta ba,sai ma wani hade rai dayakeyi,Matse hannunshi tayi tana Fadin”Maraba da Uwa ta gari gaakiya Ummi tayi Abunda kowacce uwa ta dace tayi,naji dadin yadda ta dawo da Zahra dama harga Allah banji dadin Hukuncin daka yanke ba..”Wani kallo yayi mata kafin ya Rike hannun data Rike shi dashi yana Fadin”Uhm ke murna ma kikeyi ko? kinsa me,ma Umarni zan baki ba Shawara ba,ni nasan zahra ba Tuban gaskiya tayi ba,duk Randa ta sake Miki gori ko wata mganar banza ki daki bakinta sai yayi jini kafin ni nazo nayi mata mai dalili..”Baki ta rike tana yar dariya tace”Wane ni? Ka Rufamin Asiri ,Insha Allahuma bazata kara ba.”Jinjina kai yayi kafin sufara Taku zuwa cikin gida,.
Mirmishi Malika keyi kafin tace”Mallam yaushe zamu dora daga karatunmu..”Bai kalleta ba yace”Duk Ranar da Ummi Ayda ta Shirya toh Abu Ayda Shima ashirye yake..”Dariya tayi tana kallonshi kafin tace”Na tambayeka…? Yana kallonta ya dagamata kai,Idanuwanta na cikin nashi tace”Da gaske ne,Abunda ka Fadama Saleema da Zahra..? Gira ya dagamata kafin yace”Me…? bata Dauke idanuwanta akanshi ba tace”Kana SONA….? Sun dade suna kallon Juna cike da wani yanayi kafin shi ya lumshe ido ya bude yana Fadin”Nan ba wajen da zamuyi wannan mganar bane kibari kigama wannan jegon Tukunnah..”Yafada yana jan karan hancinta,batayi mgana ba,illah kanta data aza bisa kafadanshi,shikuma ya sako da hannunshi guda daya ya Rumgumeta yana Sakin Ajiyar Zuciya,ji yake kamar ya maidata cikinshi saboda yadda Zuciyarsa ke bugawa Saboda ita.
Saleema ko kwana biyu takara Abbi ya Tarkatata ta koma Kano cikin Asibiti inda zatayi Housemanship dinta,Saleema taji kunya Sosai saboda harda ya marwan Sai da ya kirata ya mata Fatata,ya zageta kamar ya fito ta wayar yaci ubanta haka yakeji,Kuka ta sakaimai tana bashi hakuri,yace bashi zata ba Hakuri ba,Malika da Saleem zata bama hakuri,haka ko akayi Ummi ta Turamata Nombar Malika ta kirata ta bata Hakuri malika tace ta yafemata wlh.
Shiko Uban gayyar sai da ta kwana2 tana kiranshi bai dauka ba,sai ana uku kana ya dauka,Saleema na kuka tana bashi hakuri tare da alqawarin tayi Nadama kuma bazata kara ba,Bai hakura ba sai da ta sanar dashi takira Malika ta bata hakuri kana ya hakura har sukayi mgana tace tana kano,Nasiha yayi mata na ta maida hankali kan karatu kafin suyi sallama,shiko Sadiq dayaji lbri wajen Ya marwan Takakkiya yayima Saleema har kano ya nuna mata tayi Wauta,Saleema dai Tashiga uku kowa ganin laifinta yake,Nadama ko tayishi ba adadin Tayi Nadamar Abunda ta aikata,daga karshe Goge Nombar Zahran tayi acikin wayarta ma gabadaya ta maida hankalinta kan Abunda ya kawota.
AFTER SOME DAYS
Zahra ta chanza kamar ba ita ba,yanzu babu Rawan kan nan ko kadan,domin shikanshi Saleem din bai Fara kulata da cin abincinta ba,sai da ya tabbatar da Nadamarta kana,kuma ya saka mata Dokan dole da Safe ta rinka zuwa tana gaida Malika don Tana gaba da ita.
Toh Babu laifi Duk batasaki jikinta ba,ammh zata bita har daki ta gaisheta ta dauki Ayda ta mata wasa,ta gaida Goggo Hadiza tayi Fito,joda ma sukan gaisa in suka hadu,ammh ba sosai ba don ita Joda har yanzu gani take Zahra nada Sauran wani Abu Ranta,domin ko Fuskarta ka kallah zaka ga bata Fara’a Sosai.