MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL
MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Malika bata tsaya wasa ba tacigaba da karatunta wajen Malaminta ,gefe daya ga kuma girkin datakoyo domin Tunkafin ta haihu dama ta iya wasu,saboda Shiga kichen din datakeyi tana ganin yadda Joda keyi,Shiyasa ta zage Damtse kafin Joda tatafi ta samu ta koyi wanin Abu,kuma ba laifi tana da kwalkwala komai daukeshi takeyi,Ga kuma Shirin Akushi da Rufi na Arewa baya Wuceta shima tana karuwa dashi sosai,Maman Abba bata son da wannan kalmar zata gode mata ba,domin taba Rayuwarta dukkan wata gudummuwa,shiyasa ta hadamata Turamen Atamfa masu kyau da Tsada guda biyar da Kuma kudi gefe daya ga Naman suna data dibanta da yawa wanda dama su sukayi wahalanshi harta mutanen Kumo da Malumfashi sai da aka aika musu dashi,harda yan group din Malika malik paid da kuma Hafnan and Janaf paid group suma kowa ya samu kasonshi????,Maman Abba kin karba tayi Sai da goggo Hadiza ta saka baki kana ta karba tana godiya sosai.
Ana Saura kwana biyu Malika tayi arba’in Sai ga wayar Hajiya binta ta kira Saleem da kanta inda take sanar dashi Ranar Asabar mai zuwa alkalin alkalai mai ci ayanzu zai raba gadon Dukiyar Daddy so duka Manajojin kamfanoninsa dana gidajen mansa anyi musu waya zasu tararra komai suzo dashi harda Mrs suzan wanda suke Da Rubutattacen komai na hannayen Jarin Da daddy ke dashi akasashen ketare so za’a hadu Ranar asabar din domin saukema Daddy Nauyi kuma malika ita kadaice yar’shi kwara daya daya mallaka,shine zasu zo shi da ita,da sauran yan’uwanshi da suka rage daga Malumfashi domin gani da ido..
Da Saleem ya gayama Malika ranar Mutuwar Daddy takara tasoma Malika tayi ta kuka Yana lallashinta,Dakyar ya samu tayi Shuru,dama kuma Abun yazo adaidai domin goggo Hadiza zata koma malunfashi itama Joda zata tafi,shiyasa suka Shirya Tafiya alokaci daya Malika da Joda da goggo Hadiza Tun Ranar Jumma’a Tasaka Direba yazo daga gida ya daukesu ya kaisu katsina Shikuma Saleem sai gobe zai zo Saboda Ranar yana da meeting,Ammh yama joda da goggo Hadiza sha tara na arziki suka karba suna godiya.
Rabon Malika da gidansu Tun bayan Tafiyarta lokacin Rasuwar Daddy,lokacin data Shiga gidan sai da tayi kuka domin tana ganin kamar Daddy zai Fito yace”Bbyna…”Ammh kuma Daddy yatafi Tafiya ta har Abada,Hajiya ta dauke Ayda tana cillata sama tana Bangala mata Dariya,ita mamakin girma Ayda take kamar wata diyar Turawa,Goggo Hadiza tace ta samu Nono mai kyau ne Shiyasa,Malika ko tazo da kayanta dayawa Tunda Mallam yace zata kwana biyu har Abuja zata gidansu ta kwana biyu kafin takoma Zamfara,shiyasa harda guzurin mganin matan da Ummi ta kawomata tazo dashi domin tafara amfani dashi,don Ummi ta kirata ta mata bayanin gumba ce,da kuma garin aya wanda zata dinga damashi da madara,sai wata hadin zuma wacce zata dinga shanta ita kadai,Ranar Malika sai da tayi hawaye taji aduniya ai batayi maraici ba,balle goggo Hadiza ma bata barta haka ba,kayan Fruit din duk matsa mata sha,take tana da kuma Shan Abu mai Romo romo,ita kanta goggo da Hajiya Sunji dadin yadda Saleem ya yarda zai bar Malika ta kwana biyu in yazo gobe saboda su samu lokacin yimata gyaran da basu yi mata ba lokacin Aurenta.
Dose da mery ko nanan Gidansu Malika suna taya hajiya aikace aikace,Suma sunyi murna da ganin Malika,haka suke rigen rigen daukan Ayda har suna Fada,malika ko na musu Dariya cike da Nishadi
Zahra ko tana ganin Su Malika sun Tafi ta Fito Falo ta Fada kan kujera tana Fadin”Gida yazama nawa ni kadai,hakama miji yazama nawa nikadai,ammh da wannan matar ta gaje komai,wlh bantaba kaunar Malika ba,kuma bazan taba kaunarta ba..,Kawai nayi lambo ne abubuwa su yi sauki kafin na Fito da wani sabon salon..”
Akwai wan lbri dake Tsungulina,Lbrin ba irin Salon da kuka sani bane,Salo ne da zai karkata kan wani al’amari dake cimin Tuwo akwarya na Yadda Mata take mallake Miji ta rabashi da kowa nashi ciki harda Uwar data Haifeshi..? Bayan ta rabashi da kowa nashi,sai yakoma nata da ita yan’uwanta..? Shin yaya Abun zai kasance..,..? Sai kun yi jimarin bina sannu a hankali mun gama malika da aminci in Allah yaso,sai mu Dora cikin wannan Lbrin nawa wanda zai zo da Sabon salo…
Mommyn ladingo..
MALIKA MALIK…!
(Sai na rama..)
ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى ASSɷ????
Mallakar:Janafty????
28
“”Saleem sai washegari da Safe yazo,inda aka hadu aka Raba gadon Tarin Dukiyar Daddy,wanda Malika ta samu kaso mafi rinjaye da tsoka domin kusan rabi da kwatan Dukiyar natane,Hajiya ma ta samu nata kason,Sakamakon Dady bashi da uwa ba Uba,kuma ba wani dan’uwa da suke Daki daya ko kuma yan Uba duka Babu wanda zai iya gadanshi bayan Malika da hajiya,sai kuma cikin kawunan Daddy akwai wadanda suka Shigo cikin magada.
Anan Hajiya take Sanar da Malika cewa Zata koma Malumfashi ita Joda,tunda gidan da suke ciki malika ta gajeshi,ai nan da nan Malika tace batasan wannan Zencen ba,Tace Har Abada hajiya bazata bar gidan ba,zata cigaba da zama tare dasu merry ita zata cigaba da biyansu,kana manajojin Kamfanonin Malika tayi mgana dasu Tace su Cigaba da gudanar da komai sai lokaci bayan lokaci zasu dinga mgana ta waya,hannayen Jarin Daddy na kasashen ketare kuwa an Dawo dasu ne an rabasu,tsabar kudin da Malika ta mallaka banda kamfanoni bata san iyaka ba,shiyasa kuma bada cigiyar Filaye inda tace tana so agina islamiya,da masallaci,domin sadakatul jariya zuwa ga Daddy.
Hakika wannan bayanin nata ta saka Farinciki azuciyar kowa,mussaman Mijinta Saleem wanda Farincikinsa yakasa boyuwa har sai da ya bayyana mata,bai koma Zamfara ba aranar sai awashegari ammh yammah nayi yace Malika ta Shirya tazo suje yawon bude ido????Tako cakare ita da Ayda Suna Fita bai su zame ko’ina ba sai gidansu wanda Daddy ya basu,Allah sarki megadi na nan da wani wanda yake kula da gidan,komai yana nan amuhallinsa babu Abunda ya chanza.
Malika tasha mamakin ganin hatta cikin dakunan tsaf tsaf,ashe Hajiya ta kansa merry da Dose suzo su gyara lokaci bayan lokaci,basuyi masauki ako’ina ba,sai akan gadon Da Saleem ya karbi budurcin Malika haka ya Rumgumeta kam idanuwansa alumshe yake Tambayanta..”Kin Tuna wannan gadon Ummu Ayda..”Cikin kasala ta dagamai kai bai bata zarafin mgana yace”Toh wannan gadon shi yakafa miki tarihin zama azuciyata wanda baki Fita ba,kuma bazaki Fita ba har Duniya ta tashi..”Kuramai ido tayi cike da mamaki tana kallonshi bai bata xarafin mgana ba,sai da ya tsotse lebunanta kafin ya hada dogayen hamcinsu waje daya yana Fadin’Tun Ranar dana aikata miki wannan Abun,ban kara Sukuni ba,tunda lokacin Ashe sonki ya Shigeni sai nake dauka Tsausayinki nakeji sai daga baya na Fahimci na Fada acikin kogin sonki wanda baida iyaka,Wlh Malika zuciyata tanayin Xafi matukar na ganki cikin damuwa,kukanki tamkar zubowar dalma daga zuciyata,Bata miki rai kuwa tamkar Nima an batamin ne,Bana samun sukunin zuciyata sai naji gangar jikina ta hadu danaki..Yau na Na sanar dake Abunda na boye miki I SO MUCH LOVE U MALIKA…”Ya Fadamata idanuwansa na chanza launi.
Kamkameshi Malika tayi tana hawaye Da dariya lokaci daya,Kanta takara tusawa bisa kirjinsa tana Fadin”Bani da bakin mika godiyata gareka,domin asanadin Abun ka min akan gadon nan,ya chanza rayuwata na dawo malika datace na dawo mace kamar kowa,har Abada kai Abun alfahari na ne,Duk Abunda kamin bai hana zuciyata ta Fada tarkon sonka,Ina Sonka Abbu Ayda fiye da Yadda nakeson kaina..”Tafada tana dago kanshi bakinta takai kan nashi Tafara tsotsan lebenshi cike da kwarewa shima kan nata ya rike da hannu bibbiyu ya mikamata harshensshi tana cigaba da Kissing dinshi kamar Allah ya aikota shiko gabadaya jikinsa da hannuwanshi rawa suke saboda yadda Malika ke Tafiyarshi dashi cikin Kwarewa.