MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL
MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Tun bayan haihuwan Saleem da tasowarshi mutum ne mai kulafuncin iyayansa,mussaman ma Abbansa,wanda suke kira Abbi,duk inda zashi yana makale dashi shiyasa dayawan abokan mahaifinsu sunfi sanin Saleem akan Marwan saboda shi nanike yake da mahaifinsa,shiyasa ko affice zashi dashi yake zuwa tun yana karami saleem yake jinjinama masu sanya kaki kowani iri,lura da ganin yadda mahafinsa ke kokari da fadi tashin kare hakkin al”ummah,Tun Abun na bashi sha”awa haryazo yana burgesa,ammh baitaba jin zai iya zama kamar mahaifinsa ba,shi arayinsa yafison zama ENGINEARING
Lokacin dayayi Candy lokacin ne mahafinsa yazama Commissioner of police na jahar katsina,shikuma ashekaran ne yasamu addmission a ABU ZARIA inda yake karanta Chemical engenearing,Ammh duk sanda suka samu hutu yana dawowa gida ko kuma ya Wuce kauye kumo wajen Kakarsa wacce suke kira da Hajiya babba,ko yaje da niyyar yin sati,to dakyar zaiyi kwana biyu,ya wuce katsina saboda yadda basa shan inuwa daya da Hajiya babban,saboda sa idonta,shikuma tsokana da neman Fada itakuma ba hakuri sai suyita bugawa har sai ta gaji ta kira mahaifinsa awaya tana kuka tana Fadin ya kira dansa yasanar dashi ya barmata gida ko wlh ta fita ta kira samari majiya karfi awatsamatashi zuwa waje,Cp kabir sai ya hau bata hakuri nan da nan sai yakira saleem ya Rufeshi da fadan Maza yatattara kayansa yakoma mkranta,haka zai tatattara ya wuce katsina in ko taga yadade baizo ba ta dinga mita kenan tana cigiyarsa wai duk yafi iyayansa son zumumci.
In yakoma katsina hutu duk inda mahafinsa zai sanya kafa,shima zai sanya,Hardai Abbansa ya bude baki ya tambayeshi koyana Sha”awar zama kamar shi ne”Girgiza kai yayi kafin yace”Ko daya Abbi,kawai kuna burgeni ne kona ce kuna bani sha”awa bama kuba,duk wasu masu kaki dake kokarin kare hakkin mutane da kuma martaba kasarsu,suna burgeni Abbi..”Tundayaji haka daga bakin dansa ya tabbatar da cewa Allah yabashi da mai hikima da kwazo,kuma yasa aranshi ko bajima ko ba dade,sai Saleem yazo yana sanar dashi ya sanyashi aikin dan sanda,saboda yadda yasan komai na mahaifinsa ya sanya ya saba da yawa daga cikin sargent da Inspectors din,wata rana ma in zasu pertrole yakan bisu,suje tare koda bazai yi komai ba,ya zauna amota yana charting Ko Vidion call shida ya marwan,wanda yake tsokananshi sa INSPECTOR
Yana Final year dinshi Ajami”a Incident dinshi da MALIKA MALIK.. yafaru,Wanda Ranar ana partrole ne atsakanin Titin shiga katsina zuwa Dutsenma,wanda ake binciken mota zuwa mota saboda masu Fitar da makamai ta bodar katsina,shine fa Saleem ya bisu lokacin yana da Shekara 24 Ne Aduniya,yazama saurayi sosai,duk da kana kallonsa zaka Fahimci alokacin yanada kurciya,Tunda ga lokacin da Abun yafaru Saleem yaji bakincikin da baita shiga ba,ya shigeshi dalilin mganganun Malika,wanda sune suka sauyasa daga yunkurin zama injiniya zuwa yunkurin zama DA’N SANDA
Ko barci yake Abun na Fadomai arai,saboda yadda yasanya Abun ranshi,ko abinci kirki bayaci koda yakoma mkranta ga karatu ga Damuwa,duk sai kafin su kare Final exams,dinsu sai yayi rama daya koma gida haka iyayansa suka tasashi da tambayan meke Faruwa dashi ammh yaki sanar dasu komai,Lokacin daya je yasamu Abbi da mganar Shiganshi aikin yan Sanda,yayi Farinciki ya Rumgumesa yana murna da hakan bai tafi Police staff collage ba sai da yadawo service kan lokacin kuma ya sanya wani Dan sanda mai suna inspector sale,wanda yakasance ya yarda dashi sosai shiya sanya amtsayin wanda zai binciko masa lbrin malika malik,Tunda farko har karshe bayan nan,kuma yasakashi amtsayin wanda zai dinga bibiyan duk wani motsinta.
Tafiyarsa police staff collage Jos,cike yake da jarumta da kuma buri,in akace buri toh ana nufin RAMUWA domin yayi alqawari sai yasaka malika kuka da idanuwanta,sai ya azabtar da ita,sai tayi kukan zuciya Fiye da wanda yayi sai ya nunamata cewa ba kudi bane kadai martaba Aduniya ba,Dan adam ma kanshi Abun darajawa ne,Saleem bai da aboki ko Amini,saboda shikanshi bai yarda dakowa bane,Duk duniya bayan iyayansa sai yan”uwansa bai iya zama yayi dariya dakowa ba.
yana da taka tsantsan da Duniya,miskili ne sosai mara mgana da Fara”a,ammh kuma yana da barkwaci in yaso,musasaman shida sakonsa saleema,wanda in yadawo hutu,itama tazo andinga kwamawa kenan,har hutun ya kare kowa yakoma inda ya Fito Ummi kuwa har saita gaji da raba Fada kamar mayaka,ammh bai hana anjuma ka gansu tare,Ya marwan Ya dawo Nagaria,shekara biyu kenan,yana Lagos yana aiki saboda yanayin aikinsu ashekara baifi yazo gida sau uku ba.
Shekara Biyu Saleem yayi yafito amtsayin ASP Lokacin kuma aka zana sunan mahaifinsa amtsayin ASSISTANT INSPECTOR GENERAL OF POLICE Shikuma Saleem akayi posting dinshi zuwa kankara dake garin katsina saboda yadda yake da kwazo baima shekara ba yasamu karin girma zuwa *DSP bai Rufe wata Shidda ba yasamu karin girma zuwa *SP* Wanda lokacin ne mahaifinsa shima yasamu karin girma zuwa * DUPUTY INSPECTOR GENERAL OF POLICE*,Suka tattara suka koma Abuja,duka iyalanshi harda Hajiya babba wanda dakyar ta yarda takoma don tace tafi sabawa da kumo.
Yana da Shekara 28 Aduniya yasamu karin girma zuwa ACP akayi posting dinsa zuwa babban headquater yan sanda ta jahar ZAMFARA,wanda ko wata baiyi da samun karin girman ba,Allah yayima IGP rasuwa alokacin, nan da nan aka zama sunan mahaifinsa wato KABIR KUMO amtsayin INSPECTOR GENERAL OF POLICE* na kasa baki daya,inda suka tararra suka koma cikin katon gidansu mai kama da aljannar Duniya dake garki Abuja.
lokacin ne kuma dukkan zati da haiba ta cikakken Namiji ta bayyana ga Saleem,wanda ya girma da buri da kuma Ramuwa ga Malika,shekaru biyar din nan duk yayi su ne cikin Shirye Shiryen Ramuwa ga Malika,kuma daman yanzu Ne lokacin daya dace ya aiwatar da kudirinsa,yasanar da kudirinsa gaban kowa da kowa ne,mussaman Hajiya babba,saboda Abbi yadauki Abun da muhimmanci,duk da shi Abbi yataba sanar dashi mahaifin malika tsohon abokinshi ne,zununci ne yayi Rauni tare kuma haduwa datayi Wuya.
Ayanzu haka Saleema na aji uku a jami”ar Bayero University kano,tana karantar medicine tazama budurwa itama sosai,kuma Tana da Saurayinta ABUBAKAR SADEEQWanda ake cemai Sadiq dana ne ga wanda suke ya”ya maza da IG Kabir kumo,ammh mahaifinshi yadade da rasuwa kusan ma rikonsa Duk hajiya babba ce tayishi kuma duka wahalan karatunsa Abbi ne yayishi harzuwa yau dayake Matakin Controller,domin ma”aikacin costumer ne,yana Abia yana aiki shima bai cika zuwa gida sosai ba.
Dashi ne kadai nasan Saleem nada kayakyawan alaka,sosai domim ko Hutu yazo daki daya suke kwana,ammh koda wasa Saleem baitaba sanar dashi Abunda ke ransa ba ko damuwarsa,duk sun shaku da juna sosai,sai dama Sadeeq din ya Furta soyayyarsa ga saleema ne ma yasa yadaina shigemai saboda gudun raini,dayake kuma shi Abun shi zuwa ne,Ranar dayake jin barkwamci kaf,gidan nan sai sunji ya gunduresu musssaman ma sufara tsiyarsu Shida hajiya wanda baya mutuwa kamar cin kwan makauniya.
Tuni Sadeeq ya Fahimci Saleem nada damuwa,yayi tambayan Duniyan nan,ammh Saleem yacemai babu komai,domin yayi alqawarin babu wanda zaisan Abunda ke ransa sai ya aiwatar da Abunda ya kudirta Shekara da Shekaru,Saleem yana da zuciya sosai da kuma tsantsane ya tsani mutum wanda baisan darajan manya ba balle kuma wanda baisan darajan mutane ba,Yana da tsanani a kan ra”ayinsa in yakafe kan Abu mawuyaci ne kikaga ya dawo ga Abun nan,Kallon daya zakamai ka Fahimci ko yana cikin kunci ne,saboda baya gayyatoma kanshi Fuskar dariya ko Rahama akallon farko,sai ka zauna dashi ,yana da Kawaici da hakuri,ammh baya kaunar mutum mai cin zarafi mutum dan”uwansa,Lokaci daya Malika tasamu girbin tsana mafi girma aransa,wanda ko barci yake yana mafarkinta sai kaga ya farka yana Fadin MALIKA MALIK..Sai na rama..”Sai daga baya sai ya Fahimci tsabar yadda yasa ka Abun ranshi ne,kuma ya fahimci Abun bazai taba gushewa ba,sai ya nunama malika iyakarta,bai gama jin ya tsani rayuwar kudi da wayewa ba,sai da yaji duka Tarihin rayuwar malika yaji yakara tsanarta da kuma kyamatanta,da duk wasu hallayanta,kana yayi tir da Mahaifinta domin bai bi Turba mai kyau b wajen samar da ita kanta Malikn ba,,kwata kwata ba macen aure bane,ba macen mutumci bane,Aranar dayasamu lbrinta yakwana yana Tunanin mafita