MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL
MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Katsina Suka Fara Zuwa wajen Hajiya inda Taji dadin karan da’aka yi mata amtsayinta na Uwar diya,sai da suka ci abinci sukayi sallar azahar kana suka Damki hanyar Malumfashi,koda suka isa ba laifi sunga kara,dayake Ba Joda kadai za”a Aurar ba aiko yayanshi mata su uku joda ce cikon ta Hudunsu Tun Tarar da an kawo kayan Auren mutum biyu Aranar,suka Hada dana Joda cikon na ukun kenan,kuma Alhamdulillah Ciki duk Joda ce Tayi Zarrah,toh Pilot guda Wasa ne Dole akaga barin Naira,kunsan ance dama yanayin kayanku yanayin Tarbanku ne????Toh su Ummi sunga karammawa sosai,sun kai suma kuma sun taho da Niki nikin Abun Arziki harda kudin Tukwaicinsu 40k aka basu Wanda Ummi ta nuna bazasu amsa ba ammh suka matsa musu suka karba ammh bayan Sun Nuna basu ji dadi ba.
****
Malika ko tagama Fushinta na kwana Biyu Dole Ta Hakura,Ammh tayi damarar Cewa Tun ana Saura Sati daya biki zata biyama Hajiya su Wuce Malumfashi biki,saboda Joda bata da Wata kawa kuma yar’uwa abokiyar Shawararta irinta so tana bukatarta akusa da ita,Da Farkon mganarta Saleem bai dauka da Gaske take ba,shiyasa bai dau Abun Serious ba ya Fita batunta don bayajin zai iya Rabin Malika tayi Nesa dashi Domin ya riga daya saba Rayuwa da ita,ko kwana daya Sukayi Batare da juna ba ya Fita jin jiki
Malika ita tama Joda waya kan Ta samu Wacce zata mata Dilka da Halawa da kuma kunshi,in tazo zata biyamata,mganar mgungunar mata kuwa Maman Abba ta Hada ma Joda masu kyau da inganci dama ta iya Su gumba ne,su Tsimi ne,su garin aya,Hadin Bawon kankana,daidai Sauransu harda kaza da yan Shila mai mgani Malika ta Sanya akama joda,yan Uwanta ma na Dangin babanta basu barsu haka ba,suna basu Wata gumba da’a ka hadota daga sokkoto suna Damata kamar Fura da Madarar Yoghourt ko Madaran gari,Hajiya na gefe ta barma Malika komai Tunda itace Uwar Diya,shi kanshi Marwan din Da ita yake waya,shiyasa Saleem yace Ana nuna masa Wariyar Launin Fata,sai da yaga Ya marwan ya kira Malika,chan anjima kuma yaga Ummi ta kirata ayi ta kuskus shiko bamai kiranshi,daya gayama Ummi haka Dariya tayimai batace komai ba Itako Malika gwalo ta Dingamai Tana Dariya,shiko yana girgiza yake Fadin lallema Yarinyarnan zaki Shigo hannu ne…”
Biki na ragewa Saura Sati daya Tun Daren Jiya Malika ta Shirya kayanta tsab acikin akwatunanta guda biyu Wanda natane dana Ayda ta kuma Umarci Merry data Hada nata,don da ita Zata Tafi saboda kula da Ayda,shiko Saleem Sai da ya dawo da Daddare ne yaga kayan Malika tsab ashirye Abun ya bashi mamaki ganin har Washegari da Safe batamai mgana ba yasa shima ya Shareta yana so yaga iya gudun Ruwanta.
Yana cikin dakinsa yana kokarin Daura Tek tie dinsa Malika ta Shigo hannunta Rike da Waya,gefen Gado ta Zauna tana Fadin”Mallam yau zamu tafi harma na kira Direba daga gida nace yazo ya kwashemu..”ido kawai ya sakamata yana Daura Tek Tie dinshi bai mata mgana ba Sai da ya gama yana kokarin Saka coat dinshi ne yace mata”Zuwa ina..?Kuma da izinin wa..? Ya fada Fuskarsa ba Fara’a.
Jagale tayi tana kallonshi kafin tace”Bangane Zuwa ina ba Mallam..? Ka manta nayi maka mgana zan tafi katsina yau gobe mu Wuce malumfashi da Hajiya saboda Shiryen Shiryen biki..? Wayarsa yadaga yana Fadin”kuma sai nace miki toh na amince ko..? Ni azatona kawai kina mganarki ne..”Malika taji kwallar Sun Fara cikamata ido cikin Raunin murya tace”Mekaka nufi mallam..? Jakar brief case dinsa ya dauka yana Fadin”Kinfi sani ,so u better call d Driver ki sanar dashi kada yazo don inda kinga kinga bar gidan nan Toh ana gobe biki ne,bandama rashin Tunaniku na mata kitafi Tun yau nikuma sai kibarni na Zauna dawa,biki ba gobe ba ba kuma jibi Ba..”Yafada kanshi Tsaye yana nufar Wajen jerin Takalmansa bayason kallonta kada Hawayen datakeyi ya bashi Tsausauyi
Malika dataji Abun yayimata Wani iri mikewa tayi tana Share kwallar data subomata tana Fadin”Ammh mallam kada kamin haka Don Allah,daga hajiya har Joda suna bukatata,kuma in kayi la’akari ina nataba Zuwa nayi kwanaki banda lokacin dana gama wankan Jego,don Allah kada ka hanani zuwa…”Bai kalleta ba ya Zura takalminsa baki Sawu ciki ya mike yana Fadin”Meyasa kikeso ki Fara Abunda ba halinki bane malika..? Na riga na gama mgana bafa zaki Tafi yau ba fakat bani son yawan gaddama..”Daga haka ya Fice adakin yana daga wayarsa dake Neman agaji Tun dazu.
Wani kukan Takaichi ne ya kama Malika batasan sadda ta Fada bisa gado tana kuka ba,babu mai Rarrashinta Abunda yafi mata bakinciki meyasa Ranar datamai mgana bai ce bazata ba,sai da ya bari ta gama Shirya kayanta kuma ta saka rai atafiyar bayan ta kira Har Hajiya ta Sanar da ita yau tana Tafe,shine kuma zai hanata Zuwa kuka tayi sosai kafin ta dauki wayarta ta kira Hajiya muryanta a cunkushe tace kada Direba yazo bazata samu Zuwa ba yau..”Hajiya Binta yadda Taji muryan Malika tasan kila Saleem ne ya hanata sai bata damu ba,sai ma ta fara lallashin Malikan tana bata hakuri,Nuna mata tayi bakomai ammh kasan Ranta takaichin Abun yaki barinta.
Ranar Wuni Tayi kwance,banda salla babu Abunda ke Tada ita ko girki bata Dora ba Ranar Tea kadai tasha merry kuma complex tace ta Hada tasha,ita kanta Ayda yau tayi Rigima saboda bata,bata nono yadda yakamata ba,Sai wajen bayan mangariba kana Saleem ya Shigo gidan da merry ya cikaro Afalo tana jijjiga Ayda dake kuka,Amsarta yayi yana tambayan ina mamanta take..? Merry tace tana daki yau kamar batajin dadi ne,Tunda yaji haka yasan Dalili koda ya Shiga dakin nata tana kwance,da alamun yau kazanta ne tataahi don ko wanka bata sake ba,Tunda da kayan daya Fita ya barta daso yazo ya sameta,cike da mamaki yayi tsaye kanta yana Fadin”Malika…”Yakirata cikin muryan Amo dagowa tayi tana kallonshi batayi mgana ba,mamaki tabashi mamaki ammh sai ya shanye mamaki ta hanyar kara Rumgume Ayda wacce ke Saman kafadanshi yana lallashinta yace”Meye haka..? Kina ji Ayda Na kuka ammh bazaki Fito ki amsheta ki bata nono ba,mekike nufi da yin hakan..? Mai da kanta tayi ta kife bisa Filo bata tanka mishi ba,ganin haka yasa Ranshi ya baci sai kawai ya kada kai ya Fice Zuwa Falo bai kara Tankata ba.
Merry ya umarta ta kawomai madarar Ayda ta Sakamata Ruwan zafi ajikin Fidanta yana bata ta karba da Sauri tana ta Sha,daga gani tasha Yunwa,sai da koshi kana ta saki kan Fidan tana Wani maida Numfashi Tsausayinta yakamashi,Allah sarki yaro kenan,Rumgumeta yayi yana jin Bacin Rai game da Abunda Malika zata koya na wani banzan Hali,bata jima ba barci ya kwasheta nan ya mika merry ita shi kuma ya koma daki ya wanka ya Sauya kaya Zuwa jallabiya daganan ya Dauki mota ya Fice,sai da yayi sallar isha’i kana yaje yayo musu takeaway ya kawo musu,da kanshi yakaima Malika har daki bayan yabama merry nata Ya karbo Ayda Tunda yau matar gidan Tana Fushi dashi.
Babu Abunda ya kara batamai Rai da lamarin Malika illah rashin cin abinci uwa uba kuma taki bama Ayda nono,ko da Daddare bai raba makwanci da ita ba,ammh ita ta juyamai baya kuma bayan ta maida kanta ta wajen kafafunshi,babu Abunda ya tsana irin mace ta juyamai baya,shiyasa shima ya Futa batunta Shi yayi ta bama Ayda madara cikin Dare har ya samu ta yi barci koda Safe Shi yayi mata wanka ya Shiryata Shima yayi wanka ya Shirya,ko kallon barayin da Malika take baiyi ba kuma Fuskarshi tana Daure babu alamun Fara’a itako Malika haushinta daya Don me yasan ya bazata ba,ammh bai sanar da ita ba sai bayan ta Shirya..? Koda zai Fice ko tak bai ce mata ba ya sakai ya Fice bayan ya mikama Merry Ayda yace ta kula da ita ko kuka take kada ta kaima Malika ta dama madaranta ta bata tasha ta goyata karban ta tayi tana amsa da toh Sir.