MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Bayan Fitanshi ma Malika kuka tasha saboda ganin haryauma din bai ce mata komai,gashi joda ta kirata jiya tace mata bata samu tahowa ajiyan ba,ammh insha Allahu yau tana bisa hanya,ammh ta lura Mallam so yake Ta nunamai haryanzu malika malik din da bata Tafi ba,aiko sauranta kawai Ruwa ne ya daki babban Zakara Shiyasa ya ganta haka..

Har yatafi office da bacin Ran malika Shiyasa ko achan din Fuskarshi ba’a sake ba yana mamakin yaushe malika tadaina tsoronshi..? Yaushe kuma ta Rainashi haka..? ita kuwa tana kwance kiran Ummi ya Shigo wayarta bayan ta Dauka sun gaisa take tambayanta tana katsinan ne,Takaichi ne ya ciko malika ta sakama Ummi kuka tana Fadamata Abunda ya Faru,ran Ummi ya baci ta yanke kiran Ta kira Saleem yana dauka ta Rufeshi da Fada,Ta inda take Shiga batanan take Fita ba,daga karshe tace maza ya kira malika ya bata izinin tafiya bataso  iskanci,Saleem yaji zuciyarsa na Tafasa da zafi cikin bacin rai ya furta.”Haba Ummi biki sai kace hauka Yaufa saura kwana 6 in ta tattara tatafi ni kuma na zauna dawa..”Ummi taji Haushi ta kunduma mai zagi da cewa”Ka zauna da Uwarka mana,koda kafin ka Auri malikan da ita kake kwana..,.? Kai bani son Dogon zence kayi Abunda nace kawai mallam in kuma bazaka iya bane ka Sanar dani..”

Ranshi bace yace”Toh Ummi…”Daga haka ta yanke kiran tana Sababi ita kadai Abbi dake zaune gefe yana karanta Jarida ya dago yana Fadin”Aisha..”Aisha Shugaban matan Duniya,Kinga na haneki da Shiga lamarin yaran zamani kada Watarana kiji kunya atoh..”Tana kokarin Ficewa daga daki tacemai”Ba wani jin kunya Abbin Marwan,saleem din ne da ban Haushi wai kada ta barshi Shikadai,toh da dawa yake kwana..? Kaji wani iskanci..”Dariya Abbi kafin yace”Jiki da wata mgana nifa banga laifinshi ba,Ciwon Da Namiji ai na Da namiji ne so kona yi miki bayani bazaki gane ba..”Dariya Ummi tayi tana Fadin”Au hakane,toh shikenan Muma Ciwon ya mace na ya mace so ko nayi maka bayani bazaka gane ba..”Tafada tana tikar Dariya ta Fice daga bedroom din Abbi na tayata.

Bai kirata ba kamar yadda Ummi ta umarcesa sai dai ya Turamata sako kamar haka Kin kyauta Tunda ni ban isa nace Abu ba kiyi,shine kikeje kika Hadani da Ummi ko? bakomai Allah kiyaye hanya Bawan Allah bazai Wulakanta ba insha Allah.. ya Rubuta mata ya Tura mata koda taga sakon duk kuma sai taji bata kyauta ba Nombarsa ta laluba ta kira,ammh har ta gama Ringing bai daga ba,ta sake kira ma Still bai daga ba,daga karshema latse kiran nata yayi ya kashe wayar gabadaya,Sai gashi Duk dokin Tafiyar ta Fita aranta taji da badon ta kira Hajiya tace ta turo mata Direba ba data hakura wlh,haka ta dinga gwada kiransa ammh wayarsa akashe har Direban yazo,dama aleady tun dazu ta soyamai miya da farar Shunkafa ta sakamai cikin fridge ta kuma soyamai Nama Shima ta ijiyemai kozai wahala kadan ne,Duk da tasan Mallam din nata akwai son jiki karshenta sai dai ya rinka Siyan abinci.

Bata Wuce ba sai da ta Shiga gidan Maman Abba ta karbi sakonta na kayan matan data bata kudi ta Hadama Joda sukayi sallama bayan sun Rabu akan Ranar biki insha Allah zata biyo Baban Abba Tunda zashi Daurin Aure,Malika tayi murna sosai suka rabu akan sai tazo,Merry ita ke Rike da Ayda Wacce tasha wata hadaddiyar Bulawus mai kyau da tsari ga gashin kanta an tajeshi har merry ta daure mata shi da band dayake Ta biyo gashin uwar tata.

Megadi shi ya taimakama Peter ya saka musu akwatunsu aboth din mota malika ta mai sallama kafin Su Fada mota su Fice daga gidan megadi na Daga musu hannu,sai da suka dau hanya kana Malika ta yanke shawarar Turama Saleem text sai ta Shiga wajen Rubuta sako acikin wayarta ta Rubutamai.

   Am so srry mallam Bani da laifi wajen Sanar da Ummi komai,Banso mu Rabu ta haka ba buh Allah ya huci Zuciyarka we are in our way,In ka koma gida nayi maka miya,da abinci ka Duba cikin fridge,harda Nama soyayye,Sai mun hadu achan..I love u..

Tagama Rutamai ta Turamai suka Cigaba da Tafiya bata ga Reply dinsa ba sai da suka Shiga katsina kana taga ya Rubuto mata Banso ban kuma gode ba,I swear zaki dawo ki tarar da Abunki.. Daga haka bai kara komai ba,ita saima sakonshi yabata dariya ta Shareshi bata kara bi ta kanshi Ba.

Mommyn ladingo..

MALIKA MALIK…!
(Sai na rama..)

Mallakar:Janafty????

KUDUBI GIRMAN ALLAH KUREMIN AMANATA,NAYI MUKU ADALCI NIMA INA BUKATAR KIYIMA KANKU KUYIMIN ADALCI KADA KU FITARMIN DA BUK WAJE DON ALLAH????

Kada ki karanta inda baki biya ba,inda kina so kiyi karatu cikin salama ki biya kudin karatu akan 200kachal???? ta wannan account Nombar 0552179550 JAMILA UMAR Gtb ,ko kuma katin Mtn ta wannan Nombar 09069067488,Aturo hoton kai tsaye,ta Nombar dana bada

32

…………”Hajiya Binta tayi matukar Murna da ganinsu sosai haka ta Shiga Dawainiya dasu Ayda ko Ram ta goyeta bisa bayanta tana jijjigata saboda yau tatashi da Rigima ne.

Koda suka iso katsina Malika ta nemi Saleem awaya ammh bai Daga kiranta ba,sai tamai Uzuri ko yana Wani Abu ne,ammh Abunda ya bata mamaki har Washegari bata ga kiransa ba,kuma harda zasu Wuce malumfashi da Hajiya ,ta kirashi taji yayi hanging din kiranta A Number Busy kuma daya gama bai kirata ba,Abun sai ya bata mata rai Taga toh metamai Ammh ya Dau Wannan Fushin da ita,Tunda ga lokacin itama Tayi alqawarin Fita batunshi.

    Duka gidan suka Tafi,sai aka bar Dose da Wata yar aiki da Hajiya ta Dauka sai sauran ma’aikatan Haraban gidan da megadi,Koda suka isa malumfashi a family House din Su Daddy Su ka yada zango wanda dama Tun Daddy na Raye ya gyarashi Sosai Adakin Hajiya Innaro suke sauka in sukazo wanda Shima yake gyare tsaf Duk da Wacce ta Haifi Hajiya Binta tana nan da Ranta acikin gidan.

Malika bata Tafi gidan Baffan Joda ba sai da yamma Direba ya karisa da ita,koda tajema joda batanan tana makotansu inda ake mata Dilka da Halawa,sai da taje chan suka hadu,nan Suka Rumgume juna suna murna ganin juna cike da doki kafin su Zauna suna bayan sun gama gaisawa da Sauran yanmtan Wasu suna ta kallonta cike da mamakin anya wanna ce malika malik din da Suka sani..? Lalle Rayuwa juyi juyi na gaba yakoma baya Inda ada ne ko da kudi suka saka baza suga malika ido da ido ba balle har Su ganta akusa dasu haka.

Malika nan ta tare Wajen Joda suna cigaba da Shiryen Shiryen,Ayda kuma tana Wajen Hajiya ita da Merry,sai inda ta Fara Rigima ne zata kawota ta bata nono Tunda babu Nisa da Family House din Su Daddy,An tsara komai cikin Tsari sai wanda ya gani bangaren ango ma ba karya domin Duka iyayan nasa sun baza Kudi sosai bayan Tarin gayyatan dasukayi Hardashi Marwan ya gayyaci abokan aikinsa Sosai.

Saleema ma ta iso ana gobe Daurin Aure tazo ta tarar da gida cike da yan’uwa anata harkan arziki da Murnan Auren ya marwan,sai dare ne ta tambayan Ummi ashe Auren Zahra da Ya Saleem ya kare..? Nan Ummi ke Warwaremata Abunda ya Faru Tabe baki Saleema tayi tana Shaidama Ummi Nadira ce ke Sanar da ita Abunda Ke Faruwa tace Zahra ta zama Abun Tsausayi kuma tayi Nadama,Jinjina kai Ummi tayi kafin tace’Ko tayi Nadama bashi da amfani Saleema,dama ko addini ba’a son irin wannan Nadamar Saboda kana yinta ne,sanda Ruwa ya karema Dan gada,Kinga ko,ko kayita bata da Wani amfani agareka,shiyasa Amfison ka Tuba Tun kana da Sauran Damarka yanzu kuma babu Abunda mukayi iya Don Aure ya kare atsakaninsu..”Gyada kai Saleema tayi kafin tace”Wlh hakane Ummi,Allah ka tsarkakemana Zuciyarmu da imani..”Ummi ta amsa da”Ameen Ameen Saleema.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button