MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL
MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

ZAMFARA
Cikin Wannan Halin kara’in Soyewar Da Saleem da malika ke tsakar kwasa laulayin ciki yayi ma Malika salamu alaikum,wanda Ranar data Fahimci tana da shigar ciki Wuni tayi amai da zazzabi mai zafi,koda Saleem ya Dawo daga office yaga Halin datake ciki bai jira cewar datakeyi ya kyaleta basai sunje asibiti ba,ya Tada ita Zaune ya saka mata hijabi,ya kama hannunta Zuwa mota.
Private hopital ya kaita nan da nan aka Dibi jinita aka gwada sai ga sakamakon ya Fito Malika na Dauke da 2 month preganant,Murna wajen Saleem ba’a mgana bakin nan har kunne,ko kafin su koma gida sai da ya biya yayi musu takeaway Tunda bata da lafiya bata yi girki ba.
Malika dai wannan karon Cikin yafi Wahalar da ita Fiye da Cikin Ayda Wacce keda Shekara daya kenan,tafara Tatatan Tafiya Tuni,har mikewa tanayi ita kadai,Kullum cikin laulayi take,ga amai komai taci baya zama,ga Zazzabi dashi take Wuni ta kwana,har asibiti ta kwanta har sau biyu Ammh Abunda sai Addu”a,Duk sai ta rame kamar ba Malika ba,yadda cikin ke Wahalar da ita yasa Ummi tasata Ta yaye Ayda ita kuma tatafi da ita Abuja saboda Wahalan na Malika ya ragu Tunda yanzu Ayda Tunda tayi yawo kuma sai Shigen Rigima ba.
Cikin yasa Malika tayi muni duk tayi baki,ga Wasu manyan Pimples da suka Fitomata bula bula afuska,gashi yasata kazanta don in ba Saleem bane ya matsamata ya Shiga da ita tiolet yamata wanka ba,sai Malika tayi kwana Uku batayi wanka ba????gashi kuma ya saka mata wata irin Masifa Abu kadan sai tataso tana jijiyar Wuya gashi yanzu Duk yadda take Bashi kulawa abangaren Shimfida yanzu ko kusa da ita ya matso,yanzu zata bata rai,balle yace zai Shiga majalisar dinkin Duniya,yanzu zata hau kuka,,Saleem yanzu lallaba malika yake,Saboda ta zama alallaba Auren zamani,saboda yadda take Wahala harta da Abbi yazo Dubata Saleema tazo daga kano tamusu kwana biyu takoma Tunda sun kusa gamawa ana ma mganar Aurenta da Ya Sadiq ne,Su joda dai sai dai suka kira ta waya suka mata sannu,ko fa awayar ne Malika in Masifarta tatashi yi take,merry kam na Hakuri don da ita da Saleem sun Fi kowa ganin Masifar Hajiya malika,mai Cikin yan gayu,shi Acp dayayi mgana tafara Zumbura baki tana kunkuni Duk shi yajamata wahala,????Toh ya zaiyi Tunda Shi ya kumsa Abunda ke saka bala’in ai ya lallabata arabu lafiya,ko abinci bata ci daga Shasshaka sai awara take iyaci,sai daga baya kuma tafara cin kwaden garin kwaki ,ai Dole Acp Saleem ya jingine buhun gari,????Shasshaka kuwa maman Abba keyowa tana kawomata,domin ita ke kula da Malika jamgwanm,,in kuma batanan Tasaka merry ta mata wata Rana ma sai an gama ta kawo mata Tature tace bataci????Shiyasa ACP saleem fa ya ijiye kiyuwa ya zage yana Taimakon Malika don in ya Zauna harta Wajen kwanansu sai yazama bolan Juji saboda Rashin gyara,gashi ta hana Merry Shiga dakinnsu guda biyu,iyakar gyaran nata daga dakinta sai Falo,da kichen…..
SHAKIRA
MALIKA MALIK…!
(Sai na rama..)
Mallakar:Janafty????
KUDUBI GIRMAN ALLAH KUREMIN AMANATA,NAYI MUKU ADALCI NIMA INA BUKATAR KIYIMA KANKU KUYIMIN ADALCI KADA KU FITARMIN DA BUK WAJE DON ALLAH????
Kada ki karanta inda baki biya ba,inda kina so kiyi karatu cikin salama ki biya kudin karatu akan 200kachal???? ta wannan account Nombar 0552179550 JAMILA UMAR Gtb ,ko kuma katin Mtn ta wannan Nombar 09069067488,Aturo hoton kai tsaye,ta Nombar dana bada
35
………….Malika bata samu Saukin Laulayi ba sai da cikinta yayi kwari yakai kimanin Wata Hudu kafin Tafara dawowa daidai tana kuma kokarin Maida jikinta,Ammh lokacin yana Farkon Shiganshi Malika tayi Rama Sosai kamar Wacce take ciwon Tari,ammh yanzu Alhamdulillah Tafara Maida jikinta ba kamar Da ba.
Yau ma takama Weekend ne,ACP SALEEM yana gida bai Fita ko”ina ba,Yana daki ya kwanta bayan yagama latse latsensa ajikin laptop dinsa,malika kuma Tun Safe ta Fita Zuwa kichen Don Jiya dakyar tayi barci sakamakon kwadayin Cin Garin kwaki daya matsa mata Shiyasa tatashi da Safe zata karya dashi.
Kwadashi tayi da Kolokuli da kuma Manja kafin ta zo Falo ta zauna kan Kujera taja Filon kujera ta Daura Bisa kafafunta bayan ta Dora Filet din kwadan garin Saman Filo,cikin Zumudi da Murna take Tura garin Daga ganin yadda takeci kasan Abun ya kaimata,don ganin yadda Fuskarta yake Sakin Annurin Farinciki,Rabin Hankalinta naga Talabijin tana kallon Gidan Badamasi atashar Arewa 24 da,Haka kurum take son Shirin Don yana Sata Nishadi.
Merry ce ta Fito bayan ta Duka ta Gaisheta,Amsawa tayi kafin tace ta Shiga kichen ta gyara mata Shi ta gogeshi tsab,don yanzu tana kokarin sakawa a tsaftace waje ammh fa ba da kanta zatayi ba,don Malika ko Acp ya Fita Attaka yanzu????????.
Yadade tsaye daga kofar dakinsu yana Kallonta,Hannuwanshi cikin aljihun Wandonsa,na barci baki mai wani Roba ta kasa,jikinsa kuma babu Riga gabadaya yalwar gashin kirjinsa wanda ya kwanta yayi luf duk ya bayyana,batason da tsayuwar mutum ba balle taji karisowarshi sai dai kawai taji ya Dauke Filet din garin yana kallonta gefe daya kuma yana yamutsa Fuska kamar yaga kashi .
Dagowa tayi tana kallonshi kafin ta kwabe Fuska tana Fadin”Kai Mallam don Allah Ka bani bafa kyau mutum na cin abnci ana katseshi kafini sani,kune malamai magada Annabawa..”Tafada tana mai yar Dariya tana kuma gyara Zaman Shegiyar Shimin datake jikinta wanda Cibiyartama awaje,kwata kwata cikin nan ya chanzamai mata fa,Yanzu malika bata iya Wuni da kayan kirki Sai tace Zafi takeji,daga ita sai Karamar Riga da Wando.
Da kallo ya Bita kafin ya kara bin garin da kallo yana Fadin”Wai ke baki gajiya da Dura ma cikinki wannan Abun .? Baki tsoron ki haifomin bby,da Tabon garin kwaki..”Yafada yana Tamke Fuska Dariya ya bata Har Sai da ta Dara Tana Fadin”Au dama ana Haifan yara da tabon Abunda Uwa taci lokacin suna ciki ne..? Lalle ko da har dakai ka Fito da Tsiron Danwake don Ummi ta gayamin da cikinka Shine abincinta Shida Wainar Fulawa..”Ta karishe Fada tana Dariya.
Zaro ido yayi yana Fadin”Wai da gaske…?,Dariya Malika ta Kece dashi harda Dukawa,ganin haka yasa ya Bata dankwashi akai yana Fadin”Kazamar mai ciki kawai,wato nine yau na zama cartoon dinki ko..?”Tana Sosa kanta ta kwaremai baki tana Fadin”Wayyo tsakiyar kaina ya Burma wayyo Ummi da Abbi Mallam ya Burmamin tsakiyar kai..”Ta Fada harda matse ido,kamar gaske,dariya Abun ya Bashi har sai da Duka hakoransa suka bayyana Waje…
Kusa da ita ya Zauna yana Fadin”Yarinyarnan yar Sharri ce,dan wannan yafa danayi miki ne zaki sakamin kuka kice kanki ya burma,salon kijamin Sharri,in mazaki kukan Jini ne yarinya bamai Cetonki yau..”Jin haka yasa ta bata Fuska ta mika hannu tana Fadin”Ni dai bani Abuna..”Tafada tana kokarin amsa,shi kuma ya maida shi bayanshi yana Fadin”Anki abaki,in kina da karfi ki kwace…”Jin haka yasa ta mike zata tsallaka dayan gefe,shi kuma yayi Saurin mikewa ya daga Filet din sama yana Fadin”In mutum ya isa ya kwata din..”Tsalle ta Fara tana Fadin”Don Allah ka bani,wayyo…!”Dariya ta kamashi ya danne yana Daga mata gira yake Fadin”Au bazaki iya karba ba.? Amshi mana..”Yafada yana sauke hannunshi tayi Caraf zata kama ya dage sama yana Dariya,ganin haka yasa ta Fara Diddira kafa tana kukan Shagwaba,Tanayi yana kallonta yana jin Nishadi sosai yadda take Diran Kafafun ne,Ko’ina na jikinta na motsi yasa wata Sha’awarta takamashi Lumshe ido yayi yana Fadin”Tsaya tsaya..Gashi..”Ya fada yana mikamata Da Sauri ta dakata tana Washe Baki ta mikamai hannu,miko mata yayi ta saka Hannu kenan zaka karba ya Maida bayanshi yana fadin”Da Sharadi ammh..”Jin haka yasa ta Mele baki tana Fadin”Kayi ka Fada,don daga yanzu nadaina Biye maka,sai wahalar dani kake da wayau..”…