MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL
MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Ada yaso ya Ci ubanta batare da alakar aure ta Shiga tsakaninsu ba sai ya duba da ita malika bazata damu ba,domin dama bata daraja kanta ba, balle tadamu don wani ya banzarta da darajanta,babban Abun damuwar mutumcinsa da kuma mutumcin Family dinsa,tare da tarbiyan da Abbi da Ummi suka basa,mezai ce musu in har ya aikata wani barna,wanda bai kamata ba tabbas wajen Ramuwa,shi zai kashe kansa bayan yabarma zuru”rsu abun fada na har abada,shikuma yayi watsi da mutumcinsa,don duk Duniya babu Abunda Saleem yafi darajawa kamar LOKACI DA kataba MUTUMCINSA.
shine dalilin da Yasa yayanke shawarar aurenta duk da shikanshi in ya tuna hakan sai ya tsani kansa,ammh bashi da mafita ne sai ta hanyar aure,yadda zai ci ubanta dakyau bayan ya nunamata cewa duk wanda yataba kakinsa ko yaci zarafin wani ko yataba mutumcinsa wlh tallahi bazai taba kyalesa ba.
Baya da ra”ayi zama agidajen gwannati wanda take ba ma”aikatan ta, gidanshi ya siya wani Dan daidai mai dauke da Flat biyu sai haraban farfajiya wajen adana motoci,nan bayan Headquater su ne,a anguwn Birnin ruwa.
Wannan Shine.
____________
WACCE MALIKA MALIK..
“””ALHAJI ABDULMALIK DAN KASUWA Shine asalin sunan mahaifinta wanda ya kasance bakatsine wanda ya Fito daga jahar katsina A karamar hukumar * MALUMFASHI*.
Alhaji Abdulmalik,yataso ahannun kakarsa ne ta bangaren uwa,sakamakon maraya ne,duka iyayansa sun rasu Tun yana karami,ya taso ahannun kakarsa mai suna INNARO,wacce ita silam sangarta da kuma rashin kwaba da Alhaji Abdulmalik yataso dashi tun yana yaro,sakamakon gidansu irin gidan gandun nan,kowa Abunda yaga dama Shiyakeyi,gabadaya gidan yayi suna arashin tarbiya da Sanin mutumcin manya kawunanshi ma haka sukeyi shiyasa shima yataso awannan Turban,inda Allah ya taimakeshi innaro batayi wasa da karatunsa ba,dayake kafin mutuwar mahaifinsa dan kasuwa ne sosai yana da Abun hannunsa,to tun da aka raba gadonshi innaro take juyamai dayake itama irin yar Duniyan nan ne babu Ruwanta duk wata kasuwa dake ci ranaku duk tasansu,to dashi take mai hidima har ya kammallah sakandiri sch dinshi ya wuce jami”ar Usman DanFodiyo University inda yake karantar Business Admistration,domin tun yana karaminsa yana da burin zama gawurtattacen dan kasuwa,wanda zai tara kamfonino ya dinga harka Da turawa duniya tasanshi.
Zuwanshi mkranat ne,suka hadu da IGP KABIR KUMO,Har sukayi abota na tsawon lokacin da suka dauka suna mkarantar dayake kuma dukkansu kowa kwaro ne adepartment dinshi,shiyasa sukayi zarra,amakarantan kowa yasansu,ko alokacin Kabir yana yawan yimai Fada in yaga sun Fita ammh lokacin sallah yayi kowa yatashi yana barin jikin zuwa masallaci,ammh banda shi,toh ganin kabir nayimai Fada ne yasa yafara kokarin gyarawa ammh na ganin ido ne,indai basa tare,Abdulmalik bai damu da yin sallah akan lokaci ba,wani lokacin sai yazo barci zai hada su duka gabadaya,ga shi bashi da ilimin addini,ko kadan ko sallar ma nashi akwai gyara,shidai kawai Babu Abunda yasani sai yayi karatu yazama yawani mai kudi ,duniya tasanshi yayi gina gida mai kyau da tsari,ya kuma auri mace kyakyawa kullum burin Abdulmalik kenan
gama karatunsu shi yaraba zumuncin dake tsakaninsu,domin tun suna gabda gamawa Kabir ya lura sam Abdulmalik yarage sakamarmai Fuska kuma yarage shigemai kamar da,saboda yana mai Fada da nasihan yabi Duniya ahankali,shiyasa da suka gama mkranta bayan Kabir yatafi police staff jos sau biyu sukayi waya da Abdulmalik inda yake sanar dashi yasamu schoolarship daga gwannatinsu,zai tafi kasar England achan zai yi master dinshi,fatan alheri Kabir yayimai,toh Tundaga lokaci babu wanda ya sake neman kowa domin Abdulmalik na zuwa kasar England ya chanza layi kuma baida contact din kabir din Shiyasanya basu kara jin juna ba.
Zuwanshi kasar England itace mafarin komai ba,domin Tunda Abdulmalik ya Shiga cikin Turawa shikenan Burinshi yakaru,yayi budewar ido sosai mussaman da mata,sai dai Abu dayane Allah ya tsareshi baya neman mata,sai dai iyakarsa ya tsaya iya Romance da Abun da ba”a rasa ba,ammh bai yarda ya zama mazinaci ba,yayi kokarin maida hankalinsa kan Abunda ya kaishi har ya kammallah master dinshi,akuma shekaran ya dora da phd dinsa duk akan harkan kasuwanci,akuma alokacin ne yafara aiki da wani kamfanin Turawa na sarrafa takalma,ko shekara baiyi ba akamfanin suka samu lambo yabo,saboda yadda ya jawo musu kasuwa da suna sosai aduniya Tuni Abdulmalik yaji kanshi yayi sama balle da kamfanin ta shiryamai taron godiya tare da wasu kyautan kudade,da kuma dorashi amtayin Md na kamfanin alokacin.
Juliyat tana daya daga cikin ma”aikatan wannan kamfanin,wanda Tunda tasaka idonta akan Abdulmalik taji duk Duniya babu wanda takeso sama dashi,ganin yaki bata fuska sai tayi ta amfani da kissa da kissina irin na mata har yafara kulata da sunan aiki,sunyi tsawon wata Shida suna Abota kafin ta rikide takoma soyayyah mai zafi,basu Rufe Shekara ba sukayi aure,wanda dalilin haka sai da yayi alqawari da iyayan Juliyat cewa bazata taba chanza addini ba,kuma ya yarda saboda shikanshi ilimin Addinin bai gameshi ba balle yagane illah dayayima rayuwarsa.
Sunyi aure tatare a gidanshi wanda kamfani ta mallakamai,watan su goma da Aure Juliyat ta haifi yarta mace,wacce tasha wahala sosai wajen haihuwarta,wanda sai da akayi mata C.S cikin ikon Allah juliyat batayi tsawon rai ba don ko Abunda ta haifa bata gani ba,Allah yayimata rasuwa,mutuwa data girgiza Abdulmalik sosai,kwanaki akayi ana shagali kafin abunne gawan Juliyat,itakuma Jaririyar data haifa sai ya mikata ga mahaifiyar Juliyat wato MADAM DORA,ta riketa kafin yadawo daga Seminar da zashi wanda kamfaninsu taturashi har kasashe uku,zai dawo nan da wani lokaci,ta karba tana kuka domin yarinyar babu inda tabaro uwarta Juliyat,ranar da zai tafi ya sakamata Suna MALIKA
Ammh ta hanyar nuna min kauna da soyayyarku wajen Siyan MALIKA MALIK Akan Naira 200 kachal????,ta wannan account Nombar, *0552179550 JAMILA UMAR GTB,sai ki Turo Shaidan biya ta wannan nombar *09069067488* ko kuma katin waya na MTN,shima sai ki Dauki hoton katin aturo kai tsaye ta wannan Nombar 09069067488 Sai kun zo ina maraba daku masoyana..
Karku manta da garabasanmu mai son Siyan Biyu KISHIN MATA,na HAFNAN,300 ne kachal????shima zai iya Turo ta nombar bankin dana bada ko katin waya na MTN ta nombar saman dana bada, ko kuma kai tsaye ku Tuntubemu ta wadannan Nombobin domin karin bayani…
plz and plz zan Roki wata alfarma masu yiman VTU,Ko Tranafer don Allah su bari gamai bukatar Siyan Littafin malika malik,kai tsaye ya Turomin ta account Nombata 0552179550 JAMILA UMAR Gtb,ko kuma kai tsaye Amin mgana ta Wannan Nombar 09069067488,Aturo creadit kai tsaye bayan andauki Hoton katin,ina maraba daku masoyana na gaskiya
JANAFTY
????MALIKA MALIK????..!
(Sai na rama..)
ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى ASSɷ????
Mallakar:Janafty????
Dedicated to my Sweet Dota RAHMA ABDULNASEER NIGER ????Ladingota ikon Allah…,Allah ya albarkaci rayuwarki D’iya Ta gari????,endless of love Dota????????????
5
“”Bai waiwayi Malika ba sai da tayi Shekara hudu aduniya,ammh duk bayan watan Duniya yana Turamata over 5k abankin madam dora domin hidimarta,shiko bashi wannan kasar bashi wannan duk domin yaga mafarkinsa ya tabbata,itako Malika tatashi hannun Kafurai ne,bata taba zaton tana da Sirkin kamshin musulunci ba.