MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL
MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Sai Ana gobe biki Malika tazo ita da Saleem wanda Hajiya wannan karon tazo tama Rigasu gaba da kwana Uku kafin suzo,Su merry malika tabari agida Tunda ba Dade zasuyi ba,Koda suka je sun iske ango ya iso Shida tarin tawagansa wadanda ya Saukesu A hotel,shima din ba dadewa zasu yi ba don In anyi biki Ranar asabar lahadi litini zai Wuce da Saleema wajen aikinsa don Bashi da Wani Hutu mai yawa.
Chan su Malika suka iske Ayda an zama yan mata,Ta kusa Shekara biyu,tana Tafiyanta ko”ina Gwanin ban”Sha’awa tana makale da Ummi ko Abbi ko Anty Saleema,ammh saboda wayon data keda shi tana ganin Iyayenta ta makale musu musamman ma Saleem wanda Tunda ya dauketa taki yarda ya Sauketa ko nan da nan chan,Dole yayi Hakuri yana Yawo da ita.
Gida ya cika da yan Kumo mata ammh banda maza dayake achan baban gidansu Daddy na kumon za”a Daura Auren,so su Abbi ne zasu Bisu chan wannan karon basu zasu biyo ba,Ranar daurin Aure Tun Safe Su Abbi suka kama Hanyar kumo tare da Saleem da Ya marwan da ango da tawagan abokansa,Sauran abokan Abbi da Wadansu wadanda aka gayyata Duk chan kumo zasu je,sai dai su Hadu achan.
Karfe 2:30pm Aka Daura Auren Saleema da Angonta Sadiq,Akan sadaki mafi daraja da kima,basu baro kumo ba,sai da suka tsaya sukayi Walima agidansu Abbi kafin su Dauko hanyar komawa Abuja cikin Rantattsun motocinsu.
Abangaren Gidan Biki kuwa ya cika Dakam da jama”ar kumo data Saleem da Jama”ar Ummi da Abbi Allah Sarki Harda yan malumfashin sunzo ma Ummi biki Mota guda,Wanda harda Matan Baffan joda Wato wanda yabada Auren Ba Ummi kadai ba Hatta Hajiya Taji dadi sosai Suka Dinga ina suka saka dasu saboda karramawa Ummi ko bak’inta kawayenta ne lauyoyi kowacce kagani babbar mace mai ji da ado da Dukiya mai yawa kunnawansu da hannayensu suna Kara kaina Zinare da Azurfa kamar ba kudi ake Sakawa Asiya ba.
Saleema ma taga jama”ar daba ta taba tsammani ba,Domin yawancin yan Sch din su na Buk yan Faculty su na medicine duk sunzo mata harda Wadanda sukayi Housemanship dasu,A Murtala Aminu kano,Abun mamaki Nadira ta cika alqawari wajen karfe 12 na Rana sai ga tazo Direba Dr Hambali ya saka ya kawota Saleema taji dadin Zuwanta haka ta Rumgumeta tana mata sannu da Zuwa dayake ita da yar Dr Hambalin tazo mai Suna Farha.
Takaita har Wajen Ummi sun gaisa ta mata Allah sanya alheri harda 5k dinta kusan Dama Nadira tana da wayau,tasan yadda zata kyautatama Mutum harda wata 5k din tabama Ummi tace inji momi tace ace mata bazata samu Zuwa ba,alhalin Momi da Zahra ma basusan Auren Saleema ya taso ba, Abbi ko hidima tamai yawa Bai kira Bukar Madan ya sanar Dashi ba.
Saleema dakin dasu Malika da Joda suke Dakin Hajiya Babban nan takai Nadira,sunyi mamakin ganinta ammh sai suka Shanye mamakin ganin yadda Ta nufosu da dariyarta da komai,gaisawa sukayi suna Tambayan Juna yaushe gamo,Malika sai kallon Nadira take ganin yadda takara kiba da Cika kamar ba ita ba lalle ta samu kwanciyr Hankali.
Itako Nadira Malika take kallo ganin yadda cikin jikinta yayi kato,sannu ta mata hartana Zolayanta da ko yan Biyu ne,Malika tayi Dariya kawai domin lokacin tana cikin Takaichi ne domin Kayan ankonsu da sukayi ita da Joda da Saleema da Ummi ,sunki Shiganta dalilin haka fa Ummi tace kada ayi mata Riga da Sikat ayi mata Doguwar Riga ne,ammh kwata kwata taki Shiganta,Har karba Ummi tayi ta kira mai dinki ta sake bashi ya dan Buda,ammh koda Malika ta sa,yadai Shigeta ammh kuma ya matse mata ciki Sosai tana Numfashi Sama sama,dole Ummi tace ta cire,Kuka ne kadai Malika batayi saboda takaichi Dole tana ji tana ganin kowa da kayan kwarai ita sai wata Doguwar rigarta ta sanya mai Roba na kamfanin Armani,ganin haka ne yasa Ummi ta bada Wata atamfa tace yanzu take so a dinkama Malika mai yalwa yadda zata samu ta Sanya.
Nadira sai after la’asar tatafi Malika ko da karfin Hali harda tambayan Zahra Nadira tace tana gida,mirmishi kawai Malika tayi tace agaida mata da momi da Zahra Nadira tace zasu ji,har wajen mota suka Rakota ita da Joda kafin suyi sallama su Fada mota bayan an basu kaya biki,har suka bar Haraban gidan Su malika Na daga musu hannu.
Yan Daurin Aure basu dawo ba Sai After sallar mangarib,sai gasu Sun Shigo,Falon gidan suka baje suna Sauke gajiyan Hanya Yan kumo na musu barka da Sauka,shikuma ango da tawagansa a hotel da suka sauka suka yada zango harda Shi Sadiq dinn,Ya marwan Dai matarsa ya nema ta bashi abinci don Yunwa yakeji koda Saleem yaga Uban garan da joda ta Hadoma Ya marwan kwabe Fuska yayi yana Tambayan Shi ina nashi,Ya marwan na mai Dariya yana Fadin”Ka kira matarka mana,nima ai matata ce ta gatantani..”Jin haka yasa Joda ta saki dariya tana Fadin”Ai ko ya kirata bazai jita ba yanzu tana chan tana kumburin Kaya ya ki Shiganta harda wanda Ummi ta bada aka Dinkamata yau din nan..”
kwalalo ido Saleem yayi yana Boye dariyarsa yake Fadin”Ke Da gaske..? Kice yau akwai danja kenan,ai ko bari na noke ya marwan yiman alfarma ci wajen wanda matarka ta kawo ma,Wlh yau In Malika ta ganni na zama Nama..”Dariya suka sakamai Shida Joda,sai ga Ayda ta Shigo da kuka Hawaye Shaba Shaba da majina,Joda ce tayi Saurin Daukanta tana Fadin”A”a Aydan Abbi waya tabaki..”Tana murje ido tace”Annie…”Dan ware ido Saleem yayi kafin yace”Tab yasin sai dai kiyi Hakuri Ayda ta,nima in naje Rama miki ai nakai kaina,Srry kinji zo nan kyale Annie..”Yafada yana mika hannu ya amsaheta Hawayenta yake Share mata yana Fadin”Ke ne Ayda kin cika Rigima kina ganin Annie naki ta zama sai a lallaba ammh sai ki dinga Zuwa kina damunta,Bakije wajen Abbi bane,ko baki ganshi bane..”Kai ta gyada kamar wata Babba kafin ta Washe baki ta tashi daga jikin Saleem ta koma ta Dane Bayan Ya marwan tana Kiran”Dadddi…”Rikota yayi yana Dariya yana Fadin”Aydata,ai na dauka yau ba’a ga Daddin bane..”Rikota yayi yana mata Wasan daya saba yana Cafata sama Tun tana jaririyarta yake mata Haka,harta girma data ganshi zata Nufeshi ya dauketa yana mata Wasa yanzuma Dariya take kyalkyalawa cike da Sha”awa Joda ko wayarta ta Fitar tana musu video tana aika musu da mirmishi Shiko Saleem bai biye musu ya jawo kulan Sinasir din da Joda ta kawoma Ya marwan ya loda uku A filet ya zuba miyar da akayita da Naman rago,ya ja gefe yana lodama cikinsa don Zahirin Batu yau din nan yasha Yunwa don ko a kumo bai wani tsaya yaci abinci sosai ba Saboda Shi haka yake bai cika Cin abinci agida ba.
Suna cikin haka Sai ga Malika ta shigo da tsinin Cikinta agaba hannunta Rike da Doguwar Rigar da Ummi ta kara badawa aka Dinka mata ammh Still taki Shiganta,Tana Shigowa Fuskarnan ba Annuri ta Nufi Saleem yana cin abinci sai ji yayi ta ta tsayamai bisa kai tana Tura baki dagowa yayi yana kallonta ganin haka yasa ya danne Dariyan dake neman kwacemai yace”Uwar biyu meya faru ne..? Na ganki kuma da Riga ahannu lafiya ke baki sa kayan bane,kiman kwalliyan dashi..?.”.Yafada yana kallonta mganar daya Fada kamar ya Tunzurata ne,kawai sai ta Fashe da kuka tana Fadin”Yaushe zan yi wata kwalliya da wannan cikin,Kowa ya saka kayanshi mai kyau ammh banda ni,shine kuma kai kana nan zaune ko ajikin ka..”