MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL
MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

yana Danne Dariyanshi yace”Ashh,duka sunki Shiganki ne,Kai Abu baiyi dadi ba gaskiya,…”Tana Share ido tace”Wannan ma fa Ummi ta kara badawa akamin Dinkin Sauri itama bata Shigeni ba..”Ido ya zaro yana danne dariyarsa yake Fadin”Kai don Allah..? Kuma sai kace wata giwa ace Abu har an sake dinkawa ammh kuma yaki Shiganki..”Ya Fada yana Dan Ware ido kamar gaske.
Dariya ce takama Joda da Ya marwan wanda suke ta Danne ta kada ta Fito Tun Shigowar malika,Wani kallo ta Watsama joda kafin tace”Ke kuma wa kike ma Dariya..”Tafada cike da Haushi Ya marwan yayi Saurin tashi yana Rike Ayda yake Fadin”A”a fa kada ki Wuce kan matata,ga mijinki chan Shiya fara dariyan fa..”Yafada yana nuna Saleem da baki,wanda ke kokarin Rike dariyansa ammh kuma taki rikuwa sai da ta Fito Waje,Malika ta tsaya tana kallonsa cike da takaichi ,mikewa yayi yana Dariya ya Daga hannu yana Fadin”Allah ban miki dariya ba,Srry afuwan haba Malika ta,Haba yar Amanata,Kinfan san Nidake bata baci kada ki bari Ya marwan ya Hadamu fa..”Ya fada yana Dariya wacce takasa tsayawa.
Da Haushi ya kama malika sai ta bishi zata makamai Rigar hannunta tana Fadin”Zaka sani ne,wato ma Dariya kake,Tunda ni kamin ciki kabarni da aiki ko,ai akanka zan Wuce yasin kuwa..”Ganin tayo kanshi yasa ya haye gadon yana Dariya sanin dayayi bazata iya hayowa ba,itako ganin haka yasa tayi tsaye kafin ta saki kukan Shagwaba,Ganin haka yasa ya sauko daga kan gadon ya Rumgumeta ta baya yana Fadin.
“”Srry bari kuka kinji,nine ko..? Bazan karaba insha Allahu na bar dariyan.”Yafada yana Kamkameta ta gefe daya kuma ya zuro duka hannayensa biyu yana Shafa tsinin Cikinta,ya marwan da joda ko Tun Shagwaban Farko suka Fice dauke da Ayda suna Dariyansu Saleem,shiko dakyar ya lallashi yar rigimar nashi tayi Shuru,abinci ma sai abaki ya bata,yayi mata wanka ya Shafamata mai,Ranar dai bata sanya kaya ba ammh Washe gari Dole Saleem ya Fice Zuwa neman ma Malika wanda zai Dinkamata kayan da zai Shigeta kada Ta Cinyeshi danya da Masifarta.????
Washegari ko Sai da Malika ta Sanya Wani leshi wanda Saleem yasa aka Dinkamata Riga da zani,rigar sai aka Budeta sosai har Zuwa gwiwanta,Dalilin daya sanya ta barshi ya Fita kenan ammh da tace wlh sai dai su zauna tare agida Tunda dai Shi yayi mata Abunda kaya suka Daina Shiganta,????Saleem yaso su koma katsina Aranar ammh Ummi ta hana Dole suka bari sai monday,yan kumo da abokan Sadiq dai Aranar suka koma.
Ranar monday Tun Safe da karfe 10 am na Safe iyalan IG kabir kumo,suka Raka amarya Saleema da angonta Sadiq suka hau jirgi zuwa garin Abia inda Sadiq din yake aiki acikin masu rakiyan Harda Abbi da Ummi da Hajiya babba da Hajiya binta da malika da Saleem,da Ayda da joda da ya marwan,dukkansu suka rakasu har Filin jirgin Nnmadi azikiwe internationl Airport,suka rabu cike da kunci Saleema dakyar ta saki Abbi da Ummi wanda ta Rumgumesu tana kuka,hakama tama Saleem da Ya marwan Wadanda suma sunji ba dadi musamman ma Saleem domin Shine yafi kowa Shakuwa da Saleema,haka ta Rumgume joda da Malika tana kuka,wani karfin Hali ta rike Ayda wai sai tatafi da ita????Malika ko tace ta bata Halas malak ta tafi da ita har Saleema ta fara murna Saleem yace Bazai yuyu ba ta bari ta kara girma lokacin,Sunzo ganin gida,sai ta tafi da ita,Dole murnan Saleema ya koma ciki Dakyar Sadiq yajata suka Shiga jirgin Tunda ana ta kiran Sunanyensu,Haka suka dawo gida jikinsu Duk yayi Sanyi musamman Ummi,Motar Saleema kuma Sadiq yace zai aiko Direba yazo ya dauka ya kaimata chan,Tunda achan zatayi Service dinta,kusa da mijinta.
Suna dawowa Daga raka Saleema,Su malika sukayi Shirin Tafiya,Ummi taso su tsaya ammh Saleem yaki,wai saboda wajen aikinsa,kuma bashi da alamun barin Malika dole Ummi ta bisu da Allah kiyaye hanya,Wannan karon Saleem yacema Ummi zasu tafi da Ayda bata hanasu ba Tunda yarsu ce,ammh sai Ayda ta watsa musu kasa a ido ta makale Ummi tana kuka Dole Saleem ya kyaleta,da Abbi yaji lbri dariya yayi yana Fadin”Su Saleem masu ya”Toh rigimar me yakeyi ga matarsa chan da wani cikin,ko kuwa Rashin kunya yaran zamani..”Dariya kawai Ummi da ya marwan sukayi tayi Sanin Halin Saleem din da Shi kanshi Abbi.
Tare da Hajiya Binta suka Wuto katsina sai aka bar gida Daga Joda sai ya marwan wanda sai Wani Sati zasu koma Lagos din,Su malika sun isa gida lafiya,hajiya kuma har gida suka kaita,koda suka koma su Merry sun gyara ko”ina na gidan,Saleem baima Zauna ba office ya wuce saboda an kirasa yana da baki itako Malika Suna dawowa Ta fada gado tana barci don ta gaji ga bayanta ya Rike kafarta kuma ta haye Saboda Zaman mota.
Naga alaman yan group din Hafnan and Janaf paid group, da ku da Yan Malika malik paid,kun fara gajiya da Malika,kundaina nemanta balle zuzuta da Sharhi????Kodon kunga tana muku bankwana..? Karku damu Soon zamu dawo mu Daura ,Bansani ba ko kafin nayi muku ZAMAN GIDANMU mai cike da kunci,ko kuma sai bayan na kammallashi ne zan yi muku NANNY _Mai Reno Free wanda sadaukarwa ne gareku masoyan kwarai Malika malik paid,da kuma Janaf and Hafnan Paid,ALLAH YABAR KAUNA DA ZUMUNCI NA HAR ABADA..”Janafty tana alfahari daku.._
SHAKIRA janafty..
MALIKA MALIK…!
(Sai na rama..)
Mallakar:Janafty????
KUDUBI GIRMAN ALLAH KUREMIN AMANATA,NAYI MUKU ADALCI NIMA INA BUKATAR KIYIMA KANKU KUYIMIN ADALCI KADA KU FITARMIN DA BUK WAJE DON ALLAH????
Kada ki karanta inda baki biya ba,inda kina so kiyi karatu cikin salama ki biya kudin karatu akan 200kachal???? ta wannan account Nombar 0552179550 JAMILA UMAR Gtb ,ko kuma katin Mtn ta wannan Nombar 09069067488,Aturo hoton kai tsaye,ta Nombar dana bada
37
………….”Malika Da Saleem sun Cigaba da Renon cikin Malika wanda ya Shiga Wata na Tara ammh kuma yayi girman gaske gashi ta kara Hauhauwa in ka kalleta Sau daya bazaka ce Malika bane Dole sai kara kura mata ido kafin ka tantance itace ko ba ita bane.
Gabadaya ta rame tayi baki ta Rame,gashi Ta kumbura tayi Suntum,Tashi dakyar zama dakyar,shikanshi Saleem din Hankalinshi take yake da Tsausayin Malika,Sun Riga sun gama Shirin Haihuwa ganin Watan Haihuwan ya Shiga,ammh kuma haihuwan Shuru har Cikin Malika Ya haura Wata Tara ya Shiga na goma,ammh Haihuwa Shuru ganin hakane yasa Ummi tace Hajiya binta tazo ta Dauki Malika suje asibiti aduba agani in Haihuwan ta garara,kawai ayi mata operation,saboda wahalan tayi yawa ko itama Malika ta Wuta da wannan Wahalan.
Da Ummi ta kira Saleem Tana Fadamai Shawaran data yanke,sai ya nuna bai yarda A kai Malika asibiti aje akwakulo mata Nakuda ba,Su kara Hakuri Zuwa nan da Sati daya su gani,in bata ji komai ba,kuma bata Farajin Nakuda ba,sai a tafi asibitin ansan yadda za”ayi,Ummi bata ki Shawaranshi ta bar mganar haka,ammh kuma har Satin ya Shude wani ya Shiga Ba mganar Haihuwa,Dole Saleem ya yarda ya Dauki Hajiya Binta ita da Malika suka Nufi Asibitin datake awo Wato Federal Medical Center katsina.
Suna zuwa aka shiga da ita dakin Scanining,nan suka iske yan biyu ne acikin malika,don sai alokacin Allah ya gwada musu don ko da take Zuwa awo suka mata scaning Namiji daya suka gani Allah ya hanasu ganin dayan,dama toh ai karambani ne,Allah kadai yake da ikon sanin Abunda zai Faru yanzu ko anjuma,kuma Shike da ikon ganin komai,kuma Ya zartan yanzu kuma ya Faru,likitoci kawai wani lokacin Allah na basu dama ne,ammh sudin ba Allah bane basu isa su ga Abunda ya Halitta acikin mace ba,sai dai in Dan Allah yaso ya gwada musu da kanshi.