MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Yan biyu ne,ammh daya ya jirkice kafarshi tana wajen kan dayan,Shi dayan yana so ya Fito,ammh kuma kafafun dayan daya chanza wajen zama ita ta tokoreshi,koda dayan zai yi yunkuri Fitowa sai kafar dayan ta tokoreshi ta hanashi kuma shima so yake ya Fito,ammh kuma ta kafafunsa Tunda Ya jirkice,lalle ikon Allah,Shine Dalilin Daya sa Harta Wuce wattanin Haihuwarta bata haihuwa ba,da ace ta kara wasu kwanaki in suka yunkuru zasu Fito gabadaya zata iya Rasa Ranta suma yaran koda zasu Fito may be suma ba’a raye ba saboda sun Jigata aciki sosai…

Bayanin da Dr yayima Saleem da Hajiya kenan ya kuma umarci Saleem daya sanya hannu yanzu zasu Shiga da Malika dakin Tiyata Domin Cetonta ita da Abunda ke Cikinta,kuma suka bashi Umarnin yaje ya biya kudin aikin yanzu yanzu,Jikin Saleem na Rawa ya Rattaba hannu kafin ya kwashi Gudu yaje ya biya kudin Aikin da za”a ma Malika,Cikin lokaci kadan suka gama Shirya malika cikin kayan Tiyata suka gungurata zasu Shiga da ita dakin Tiyata,Lokacin Su saleem suna wajen Da hanzari ya karisa ga Malika ya riko hannunta haka ke Zubomata sha,ya sanya hannu yana Sharemata yake Fadin”Stop crying kinji za”ayi aikin lafiya insha Allah kinji..”Kuka ya kwace ma Malika ta sakeshi tana Shesssheka take Fadin”Mutuwa zanyi Mallam,ka yafemin don Allah..”Abunda ta Fada ya Kashema Saleem da Hajiya gwiwa bai samu zarafin mata mgana ba,Suka gungurata Zuwa dakin Tiyata wanda Hannunsu dake sarke da juna ya Rabe,har aka Shiga da ita suna kallon Juna Malika na Fitar da kwallah..

Kai Saleem ya Dafe yana kiran Sunan Allah,haka yaji Duniyar tayi masa kunci Bai Saurari Hajiya dake Fadin ya bar Damuwa Malika zata haihu lafiya,cikin mota ya koma ya Dafe kanshi da Sitiyarin mota yana Fidda Numfashi sama sama yana kallon idanuwan Malika suna Fitar da kwalla,tsigar jikinsa ne ya tashi sai yakeji kamar kallon bankwana tayi mai,Saleem har sai da ya Fitar da hawayen Tsausayin kanshi dana Malika,nan cikin motan ya cigaba da zama don baida kuzarin komawa cikin Asibitin yana ji wayarsa dake cikin aljihu tana Faman Ruru ammh kuma yakasa sanya hannu ya Cirota balle yaga kowaye mai kiran nasa.

Ummi ko dagachan Bangaren Hankalinta amatukar tashe yake ganin Tana ta kiran Wayar Saleem bai dauka ba,bayan kuma sunyi waya dashi Sanda zasu kawo Malika asibiti ganin bai daga kiran nata bane yasa ta maida akalan kiran nata kan Hajiya Binta ita ta dauka ta mata bayanin Abunda ke Faruwa,hankalu fa sun tashi sosai don nan Ummi take Sanar da Abbi wanda Shima hankalinshi ya tashi ammh sai suka barma Allah komai suka koma mata Fatan Allah yasa ayi aiki lafiya kuma afito da kai lafiya.

Shudewar Awa uku likitocin da suka Shiga da Malika sukayi kafin Su Fito,Kowanne Fuska ba Annuri Hajiya dake zaune awajen,tayi Saurin mikewa tana Tambayansu ya Malika..? Anyi Nasara kuwa..? Basu samu bata amsa ba illah tambayan Saleem da sukeyi ganin haka yasa Hajiya Binta tayi waje da Gudu,aharaban asibitin ta tsaya tana Neman Saleem bata ganshi ba,har masallacin shashen maza ta leka ammh bata hangoshi ba,ganin motarshi a parking space ne yasa ta karisawa ta Gudu ta kwankwasa glass din gaban motan tana Fadin”Saleem,Saleem malika..”…

Kansa na Bisa Sitiyari Barci ne ya fara dibanshi Harda Mafarkin An Fito da Malika ta Haihuwa lafiya kamar amafarki yaji buga glass,shi ya tadashi A Firgice yana bin inda yaji karan da kallo,dayake motar Tinted ne na waje baya ganin na ciki,shi ya Fara ganin Hajiya,ganin yadda Fuskarta ya Nuna damuwa ne yasa ya balle murfin mota ya Fito yana Fadin”Gani Hajiya lafiya..? Sun Fito da Malikar ne..? Hajiya Bakinta na Rawa tace”Eh nemanka suke..”Jin haka yasa ya Runtuma da gudu Zuwa cikin Asibitin Jikinsa na Rawa saboda Fargaba,itama Hajiya ta takemai baya.

Yana zuwa kofar Theater Room ya Gamu da likitocin bai jira cewarsu ba yafara Fadin”Hop d Operation is Sussesufull,…? Kallon Juna Sukayi kafin wani daga cikin Likitocin ya Dafa kafadanshi yana Fadin”Yes..d bbys are in good condition buH….”Saleem yaji Zuciyarsa na lukude ya Warce kafadansa daga hannu Dr yana Fadin”Buh waht…? Yafada Duka idanuwansa suna waje…

Kansa na kasa yace”Buh u lost her…”Zaro ido Saleem yayi cike Da firgici ya cakumo Wuyar wanda yace Malika ta Rasu yana Fadin”Kutumar ubanchan,Matar tawa ce zaka ce min bata,kana da Hankali kuwa,Wlh sai na kasheka nima…”Yake Fada da alamun ya Fita daga hayyacinsa,Hajiya data Fahimci Abunda ya Faru ta dora hannu aka tana kuka tana Fadin”Innalillahi wa’inna Alaihirraju’un..”Sauran likitocin ne suka Rike Saleem suna Neman rabashi da Wuyan wanda ya shaka,ammh sai Fuzge Fuzge yake kamar mahaukaci yana Fadin Shima sai ya kasheshi indai Bai Fitomai da matarsa ba.

Wani daga cikin Dr din ya Riko Kafadun Saleem da karfi yana Fadin”plz mrs man Cool down We know ur Feeling.buh am so srry to say u Wife iz Dead,we are Srry…”Zuru Saleem yayimai da ido yana kallonsa kafin yaji Duniyar na juyawa dashi kafin kace me, ya Sulale zai Fadi asume Dr din ya Rikeshi yana kwalama Nurses kira,nan da nan sai gasu da gadon daukan Marasa lafiya suka daukeshi Suka dorashi suka Shiga dashi wani daki.

Wata Nurse ne dake Dakin Tiyata ta Fito da Sauri tana Fadin”Sir She iz Breathing,…”Zaro ido sukayi atare kafin su Rankaya cikin dakin da hanzarinsu cikin gaggawa,shiko Saleem taimakon gaggawa akabashi kafin asamu ya Farfado aka yimasa alluran barci,Hajiya dake waje ban da kuka da Salati Babu Abunda takeyi tana cikin wannan Halin ne sai ga wani likita ya Fito daga Tiyata Room din daga ganinshi Musulmi ne,kallon Hajiya yayi yana Fadin”Mama kuyi hakuri da Abunda ya Faru lokacin da suka Ciro bbys din dake cikinta sai Numfashinta ya dauke,so sun zata ta rasu buh yanzu Numfashinta ya dawo komai ya Daidaita mun mata alluran barci zamu Kawota dakin Hutu ita yaran ta samu Twice,Duka Maza..”,

Hajiya Binta Tana washe Baki take Fadin “Alhamdulillah..Allah mungodemaka..”Take Fada tana Share kwallah,Daidai lokacin kuma wayar Ummi tashigo wayarsa nan da nan Hajiya ta daga bayan sun gaisa take tambayanta ya ake ciki..? Nan Hajiya Take Sanar da ita komai,Ummi ta Girgiza kai Tana Fadin”Ina Shi Saleem din..? Hajiya tace”Sun Shiga dashi ciki suma yayi lokacin da sukace Ba malika..”Ajiyar Zuciya Ummi ta sauke Kafin tace”Allah ya sauwake Allah yabata lafiya ya kuma Raya Abunda aka samu,Da safe muna nan Tafe..”

Dahaka sukayi sallama da Hajiya nan take Fadama Abbi Abunda ke Faruwa,ga murna ga damuwa sun tattara komai sai gobe in sunje sun gani kafin kace kwabo Haihuwan Malika ta zaga dangi,shiko Saleem sai da Daddare ya Farfado inda ya samu lbrin Malika bata mutu ba,sai lokacin yaji Abunda yamai Nauyi akai ya sauka,itako Malika bata Farfado ba sai Washegari,Dayake Hajiya ta kwana da ita Shikuma Saleem yakoma gida,Tana Farfado Abunda ta Haifa ta Fara Tambaya inda Hajiya ta mika mata su Duka biyu,kukan Farinciki Malika ta saki ta kamkame yaran,Kafin ta tambayi Saleem nan Hajiya ke Sanar da ita Abunda ya Faru,wani Farinciki ya Ratsata ganin Har Suma Saleem yayi Saboda Ance ta Mutu lalle ba karamin So da kuma muradi Saleem ke Mata ba.

Saleem Sai wajen 10 yazo,shi yazo musu Abun karyawa,shida merry yazo Saboda tataya Hajiya zama,Lokacin dayayi Arba da Malika agaban Hajiya ya Kamata ya Hadata ida yaran ya Rumgume yana Hawayen Farinciki,Malika na mai Dariya mai Suma,Keyarta ya make yana Fadin”Waya ce miki na suma..? Inda ace kin Mutu da nima binki zanyi Amanata,..”Kansa ta Shafa tana Fadin” Bazan Mutu ba Mallam,ina tare dakai Abadan,dakai zan rayu da kuma kai zan mutu..”Bakinta ya Sumbata cike da So Da kauna,hajiya dai Tuni tayi waje don Saleem dare dare kan gado yana ta Sumbatar Yaran,,yana kuma Hadawa da uwarsu,yana kuma ma Malika dariyan wannan karon ma yaci gari domin Gabadaya yan biyu kamaninshi suka debo,wannan karon ma Farar Fatar Malika kadai suka debo ammh har Shape din hancinsu,irin na Acp Saleem ne.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button