MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Koda ta koma daki kasa barci tayi wayarta ta Dauka ta latso mai kiran Daidai lokacin dayake zuba hon akofar makeken gidan, nashi megadi yataso ya budemai yana mai Barka da Zuwa shima cike da mamakin yau yallabai yayi dare,duk mai irin aiki irin nashi kowani lokaci zasu iya Fita.

Sai da ya Daidaita motar a parking space kana ya daga kiran Malika wanda na Uku kenan ya Shigo wayarsa,Tana jin ya daga ta Fashemai da kuka Dan ware ido yayi yana Fitowa daga motar yake Fadin”Meya Abun kuka kuma..? Hmm mata sai abarku ku bata mutum rai kuma ku Fishi nuna ku aka cuta ko..?”Tana Share hanci tace”Don Allah Mallam ka ya Femin,ka dawo gida hakanan Hankalina yaki kwanciya Zuciyata tana Ta Tunanin kila ko kana tare da Wata ne..”Mirmishin gefen baki ya saki kafin yace”Na shigo gida yanzu..”Daga haka kawai ya yanke kiran,jin yace ya Shigo gida yasa ta Fito daga daki da sauri tana kallonshi ya Shigo yana Takunsa cikin isa,har ya hauro saman yana kallonta bai mata mgana ya Bude dakinsa ya Shiga ya maida kofa ya Rufe Ajiyar Zuciya Malika ta sauke kafin ta koma daki tana Share kwallar Daya Tarun mata.


Har washegari Saleem bai saki ba,,sboda yana Fushi da ita ko karyawa baiyi ba,da goggo Hadiza ta matsamai ya tsaya ya karya sai yace zai karya a office in yaje,kuma Malika na zaune adakin goggon Hadizan daya  shigo gaisheta da Safe,Ayda kadai ya daga Data rugo tana gaisheshi ko su Aryan dake hannunta bai karba ba Daga hannunta ya lakace musu hanci yana musu wasa koda Malikar ta gaisheshi dakyar ya amsa kamar yana Ciwon baki ganin haka yasa Malika taja bakinta ta Tsuke ya har Fice,goggo Hadiza ba macece bace mai Shiga Sha”anin yara,kuma Abu na ma’aurata Shiyasa tayi musu bakam kamar bata Fahimci basu jituwa ba.

Tafi tafi Fushin Saleem yama Malika tsauri wajen Sati daya Abu yaki Wucewa awajensa,gashi yanzu baya zaman gida kwata kwata,baya Shigowa sai around 10 kuma yana Shigowa zai Shige dakinsa ya Kulle,malika tanemi hanyar Sulhu ammh yaki bata dama,shiyasa itama ta Kama kanta,iyakarta dashi gaisuwa sai ko in ya Shigo dubasu Aryan,wani lokacin ma Dakin goggo Hadiza yake tarar dasu,ganin yadda yaki Fahimtarta shiyasa Itama Ranta ya baci da wannan Fushin mara Dalilin da Saleem ya Dauka da ita gabadayansu suka Share juna kowa na ganin Shi ba’a mai Daidai ba.

  ****
Ranar da Malika tayi Arba”in Ranar Ya marwan ya kawo joda gida domin cikinta ya Shiga wata na tara,kuma bashi da wani Hutu,shiyasa ya dawo da ita gida ta Haihu tunda chan kudu ne,koda hajiya ta kira Malika ta sanar da ita cewa kawai tayi zata kira jodan don yanzu bazata ce zata zo ba,kada ta kara wani laifin,Kuma shi Saleem din Ya dauko su daga Airport, Daganan Motar haya Ya marwan ya Shiga ya tafi Abuja achan ya kwana sai Washegari ya hau jirgi ya koma birin ikko don Ba”a bashi Hutu ba wannan ma Excuse ya dauka da zai kawo Joda gida.

Har Joda tayi Sati da Zuwa ammh kuma Malika bata jeba,Bai cemata ci kanki ba,itama bata tayaba ta rabu dashi,Aranar kuma Yasa ka Direba ya maida goggo Hadiza gida,domin ta matsa zata tafi,saleem ya hadamata Sha tara na arziki hakama Malika tayi ta godiya tana saka musu albarka,Malika ko sai tayi kwallar harta Fadin in goggo Hadiza tatafi zata kara zama marainiya bata da mai kula da ita,itako goggon Hadiza tace Kina dashi mana Malika ga mijinki nan,Cewar datayi haka sai da Malika ta kalli saleem Shiko ya Hade rai kamar bai taba Dariya ba,sai da suka raka goggo Hadiza bakin mota dama Direban gidan Hajiya ne zai kaita,har suka Fice Daga gidan suna daga musu hannu,Shi Saleem yana dauke da Ayda ne,ita kuma Malika Ayyan ne ke Hannunta Aryan ya gama Rigima ya kwanta,Gaba yayi ya barta ita kuma tana Shigowa ta haura sama,Bai Shigo ba sai da Ayda ta tafi wajen su Merry shikuma ya hauro sama dakin Malika ya tarar da ita tana bama Ayyan Nono,Tunda taga ya Shigo Fuskarshi ba Fara”a tace topha,aiko illai gabanta ya tsaya yana Fadin”Miye Dalinlinki na cema goggo Hadiza in tatafi Zaki kara zama marainiya,wannan wata irin mgana ce,sai kisa tayi tunanin ko ina cutar dake ne fa..”Yafada yana mata wani kallo,kanta ta dago tana kallonshi idanuwanta sun ciko da kwallah,,ido cikin ido suke kallon Juna kafin ita tafara Janye idonta Hawaye Datake kokarin Rikewa suka zubomata tasa hannu ta Share Abunda ta iya cewa kawai Shine”Kayi Hakuri..”

Yadda tayi ne jikinsa sai yayi Sanyi,duk Fushinsa sai ya sauka sausauta murya yayi yana Fadin”Kidaina irin haka ba dadi sai ta dauka wani abu ne..”Kanta na kasa ta dago tana kallonshi tace”Ba karya nayi ba,yanzu kadaina kula dani,Haba mallam takan laifin da nayi bisa kuskure kadan sai ka dauki Fushi dani mai tsawo haka,Sai yanzu nakeji ni Marainiya ce ada,ina ganin ka lullubemin maraicina amhhh..”TaKasa karisawa tayi Kuka taci karfinta da hanzari ya isa gareta ya zauna kusa da ita Ayyan ya karba ya Fita dashi sai gashi ya dawo Shikadai,Hannu ya mikata mata ta karba ya mikar da ita tsaye Habarta ya tallafa yana kallon kwanya idanuwanta kafin yace”waya gaya miki ke Marainiyace,Haba Amanata indai ina raye har abada baki ba kukan maraici..”Yafada Cike da kulawa,Runtse ido tayi hawaye suka kwaranyo mata kafin tace”Ka chanza mallam,ka barni inata wahala da Fushinka..”Harshensa ya sa yana lashe hawayenta,sai da ya lashe kaf,kafin ya Rumgumeta kam yana sakin ajiyar zuciya yake Fadin”Am srry Nayi kuskure insha Allahu baran kara ba..”Yafada yana kamkameta,ajiyar zuciya ta sauke tana zagaye kugunshi da hannuwanta,cikin muryan Sanyi tace”Nayi kewarka Abbu Ayda..”Ta fada tana sakarmai kiss Awuya kamkameta yayi yana Shinshinar Wuyanta kafin lokaci kadan sungama Rikita juna da salon wasanninsu,Cikin Fitan hayyaci suka raba junansu da kayan jikinsu,Kafin su Dangana da kan makeken gadonsu suna Tsotsan juna cike da kwarewa da muradi mai girma.

Ranar dai ma”auratan komai ya Daidaita tsakaninsu Haka suka kwana manne da juna,don ma Rigimar su Ayyan ta hanasu sakat,ammh duk da haka Sun mori juna ba laifi Saleem ya Famshe kwanakinsa,dama gashi goggo Hadiza ta gyare yarta Sosai Acp ya yaba kuma yayi ta sambatu????

***.
Washegari kuma suka tashi da Lbrin Haihuwar Joda wacce ta haihu lafiya kalau agida,sai da safe Hajiya ta kaita Federal medical Center Katsina,aka duba ita Bby lafiyanta Kalau,Ta haifi da Namiji masha Allah,Dama Malika Ranar take Shirin zuwa sai aka tafi da murna gabadaya,Saleem ya ijiyeta agidan bayan ya Shiga yayi barka Shima ya Wuce office yabar Malika nan sai dare yazo ya dauketa,suna hanyar komawa gida yake sanar da malika zata fara hawa daya daga cikin motocinta da kanta,ammh sai dai su bari Weeked ya dinga koyamata mota,Malika tayi ta murna harda kwallar Farinciki,Abun yayi ma Saleem dadi ganin Walwalar Malikarsa zata dawo,domin shi yanzu babban Farincikinsa yaga Malika na cikin Farinciki akoda yaushe..

Don Allah zan Rokeku wata alfarma Kada ku Cutar dani wajen Hadamin Malika waje daya bayan na kamallashi, na ganshi yana yawo agroups,kamar yadda ni Janafty nafada ba yadda zan mallaka ma mutum malika a 200 kachal,haba na be joking aie,kudin karatu kuka biya bana Mallaka ba,so plz and plz Kada ku Fitarmin dashi ko bayan nagama Don Allah na Rokeku..????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button