MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

SHAKIRA????

MALIKA MALIK…!
(Sai na rama..)

Mallakar:Janafty????

KUDUBI GIRMAN ALLAH KUREMIN AMANATA,NAYI MUKU ADALCI NIMA INA BUKATAR KIYIMA KANKU KUYIMIN ADALCI KADA KU FITARMIN DA BUK WAJE DON ALLAH????

Kada ki karanta inda baki biya ba,inda kina so kiyi karatu cikin salama ki biya kudin karatu akan 200kachal???? ta wannan account Nombar 0552179550 JAMILA UMAR Gtb ,ko kuma katin Mtn ta wannan Nombar 09069067488,Aturo hoton kai tsaye,ta Nombar dana bada

39

………….””Har Zuwa Ranar Suna Kullum Malika sai taje gida,in Saleem zai Fita office Tare suke Fita ya sauketa shikuma ya Wuce,Daga Hajiyar har joda sunji dadin Haka sosai,Yan Malumfashi sunzo mota biyu,mota daya daga barayin Dangin Baban Joda,daya kuma Daga Family dinsu Hajiya,wato Baffanin Malika kenan,hakama yan kumo sunzo duba bby,Sun kuma zo da Abun arzikisu sukayi barka suka koma.

Ummi ma tazo,Da kayan suna Niki niki da nata dana Abbi dana ya marwan Wanda dama joda tazo da duka kayan Suna na bukatan da suka siya na haihuwa,sai kuma ya Turama Ummi kudi ta kara mata,Abun fa masha Allah sai wanda ya gani Ya marwan yazo kwana daya yayi ya koma inda yayi ma yaro Huduba da SALEEM wato yama Acp takwara kenan jin wannan Suna yasa daga Saleem din har Malika sukayi bajinta ban girma Malika makullin mota sur tabama Joda Shiko Saleem Kudi ya bata 100k ita kuma Malika ta dora mata Nata darin akai making 200k,Joda Saboda murna sai da ta Rumgume Malika kamar ta mata kwallar saboda godiya,Hakama Hajiya tayi ta godiya,itako Malika tace don Allah su bari,miye amfanin uban Dukiyan datake dashi in har batayi ma nata ba.

Saleema ma tazo Ranar suna ta kwana ita da malika sai washegari ta koma Abuja ta kwana kafin ta Wuce,Taro ya tashi lafiya sai Fatan Allah yara young Acp,wanda suke kira da Junior.

Hajiya ce ke Kula da Maijego da danta cikin kwanciyar Hankali,Hakama Malika itama tana cigaba da kula da kanta da kuma Mijinta da kuma ya”yanta,hakama Shima Saleem yana iya Bakin kokarinshi na ganin ya Sauke dukkan Hakkin Malika da na ya”yanshi daya Rataya awuyanshi,game da Harkan kasuwancinta Shi Malika ta dora Amatsayin manajojin kamfafoninta,duk wani kudi da zai Shiga ko Ya fita,ko in wani Abu ya taso,sai dai in Abu ya gagareshi sai ya Fadama Malika ita kuma amtsayinta na wacce tasan kasuwanci sosai sai ta Fitar da mafita cikin Lokaci,Shiyasa Kasuwancinta da Kudinta suke kara hauhauwa.

Mganar koyamata Mota kuwa ya cika alqawari Duk Ranar Asabar da lahadi suke Fita da la”asar yana koyamata mota dayake Malika akwai kwalkwalwa basuyi wata ba ta koyi mota sosai,har tana tuka kanta taje gidan Hajiya ko asibiti,ammh bata taba Tafiya mai Nisa ba,sai dai ko cikin gari in zata Fita.

Joda kuma ta cigaba da jegonta cikin kwanciyar Hankali ayayinda Da hajiya ke kula da ita,bata koma ba sai tayi wajen wata biyu,taje Abuja ta kwana biyu taje malumfashi ta kwana biyu Shima,har wajen Malika tazo ta kwana,Washegari mijinta yazo ya dauketa suka je Abuja suka kara kwana daya suka daga zuwa birinin na ikko da su da Little Acp dinsu wanda yayi kiba sosai yasamu Nonon uwa mai kyau da kuma kulawa in ka ganshi gwanin ban” sha’awa.

Saleem ya saka Ayda awata private,sch Bby clss,saboda bakinta ya bude sosai ga Shigen wayau shiyasa Saleem ya sata amkaranta bakinta yakara bude achan,Malika ke kaita watarana taje ta ta Dauko Watarana kuma Saleem ya kaita kafin ya Wuce office in ko ya makara sai ya barta Malika ta kaita,Abun nasu cikin kwanciyar Hankali gefe daya kuma tana cigaba da Renon yan biyun ta suma da suka habake sukayi kiba sosai sai da wannan karon goyon Rigimammu take,don su Aryan akwai Rigima da daya ya Fara kuka,toh Daya zai dauka,Haka take Fama,don ma su merry suna kokarin Taimakamata da Renonsu wani lokacin.


Zahra ta yi sanyi Fiye da yadda kuke Tunani ta chanza daga zahra ada ta koma Fatimatulzahra’u Wacce take da Tarin natsuwa da hankali yanzu ba wannam rawan kan,da kuma shigen iyayi bashi,Game da zafin kishinta kuwa ta Fahimci Halittanta ne,sai ta koma tana Rokon Allah ya rage mata wannan Zafin kishin,kuma Alhamdullah,Yamzu Abun ya fara ragewa ba kamar da ba.

  Auren Nadira shiya kara maidata wani so silent,ada ta saba komai tare suke koda suka rabu da Saleem,kewar batamata yawa saboda Tana ganin Nadira ko banza zasu kwana tare su tashi tare,toh yanzu Nadira tayi Aure tana gidan Mijinta tana zaune lafiyanta,Ta kwantar da Hankalinta Da Zahra Taje gidan tayi mamakin ganin kibar da Nadira ta narka ya”yan Mijinta kuma shashenta suke Wuni Suna Anty kaza zanci ita kuma tana ta Ina kasa dasu,shiyasa ta Shiga ran iyayen kunsan me da wawa,Kwata kwata suna tafiyar da kishinsu Cikin tsafta Domin kunsan ba inda ba”a kishi sai dai akwai masu na ilimi dana Jahilci,Zahra bata fahimci Nadira nada ciki ba sai da ta sanar da ita da kanta tace mata tana ciki na tsawon wata Hudu,Abun ya daki zahra haka ta koma gida ta kulle kanta adaki tana kuka,Tana kara Nadamar Abunda ta aikata da”ace ta kwantar da Hankalinta da yanzu kila ta haihu Bama daya ba,ammh gashi har Nadira tayi aure jiya jiya har ta samu ciki,haka dai ta kwana kuka ta kuma yi alqawarin maida al”amarinta ga Allah ko zai kawo mata mafita.

Momi tana iya bakin kokarinta wajen ganin Zahra ta saki ranta ammh sai ahankali Shiyasa ta Shirya musu Tafiya lagos wajen Hajiya baraka mahaifiyar Su Nadira,Zahra taji dadi sosai Balle ma hajiya baraka macece mai Fara”a da barkwanci Shiyasa Zahra ke jin dadin zama da ita,sati daya Momi tayi ta baro Zahra chan ta dawo kuma ba laifi zahra ta saki ranta dayake ta sake aure bayan Rasuwar Mahaifinsu Nadira,har ta haihu,Zaman lagos yayima Zahra dadi sai tayi wata biyu kana ta Biyo ya Nadir suka dawo tare wanda Suka isketa achan Shida matarshi Sati daya sukayi da zasu dawo da taboyosu.

Bayan dawowarsu ne Ya Nadir yazo har gida ya samu momi ta complain Din zaman da Zahra take haka babu Abunda takeyi,gashi yaga Duk ta rame ta koma kamar Zahra bukar Mada,momi tayi bayanai ta yi iya bakin kokarinta ammh Zahra sai ahankali ganin haka yasa yasamu Abba ya mai mgana zai Nema ma Zahra aiki saboda zaman kadaichin yayi yawa,Bai yi mai musa ba,shiyasa ya karbi Takardunta bata da masaniyar komai sai da gidan Redion Freedom kano suka kirata interview Shi da kanshi yazo ya dauketa ya kaita tayi interview,cikin Nasara ko sati batayi da zuwa suka Turo mata sakon Sun Dauketa aiki ashashen labru,murna wajen Zahra ba”a mgana Haka ta Rumgume ya Nadir tana murna momi da Abba suna dariyan Farinciki Domin rabonsu da ganin murnan Zahra haka Har sun Manta Arana.

Ranar data Fara Zuwa aiki Ranar Ya Nadir ya bata key din sabuwar motar daya Siya mata 4matic,mai kyau,Zahra kamar bakinta zai Tsage saboda godiya,hakama su Abba da momi suna mai godiya ya bata rai yace Haba Zahra fa yar”uwanshi ce saboda haka zai iya komai domin ganin Rayuwarta ta dawo kamar da,Haka ko akayi acikin Sabuwar motarta tafara Zuwa aiki Ranar,Data tashi kuma ta biya gidan Nadira ta nuna mata Sabuwar motarta itama Nadira tayi murna haka suka Rinka Dane motan suna Santi,ita kanta Nadira murna ya kamata ganin Zahra Ta chanza kamar ba ita komai yanzu tana yinshi cikin aji ne,ganin Zahra ta Shirya zata tafi tace mata zata biya gidan Ya Nadir,aiko Nadira tace sai taje Dr ta kira awaya tace mai zata gidan Ya Nadir ita da Zahra yace adawo lafiya,saboda kwakwa Nadira ita tayi Driving dinsu zuwa gidan ya Nadir suka kuma yi sa”a suka iskeshi agida nan Nadira ta sakamai kukan wlh itama sai ya Siyamata mota,Yako yace bazai siya mata ba taje mijinta ya Siya mata nan ta bare baki tana kukan Shagwaba Zahra da matarshi wacce suke kira Madam suna mata Dariya sai yammah Zahra ta maidota gida suna tafe suna Hira Nadira na kara Yima Zahra Nasiha da kuma hakuri da Rayuwa Zahra ta mata alqawarin insha Allahu ta chanza ita yanzu ko me mata Uku ce itace ta Hudu yazo ciki zatayi dashi ta gaji da zaman gida,Don ma dan aikin nan da Ya Nadir ya samo mata shike Debemata kewa ammh Kadaichin yayi mata yawa Sosai,Dama haka Rayuwa take Duk wanda baiyi Sharar masallaci ba to ai zai yi na kasuwa kodon Dolensa don Ubanshi..”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button