MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL
MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Ahaka su Ummi suka iso suka sameshi sai da Ummi ta Faffatakeshi waje kana Ya Fita,harda Rigimammiya Ayda aka zo,aiko nan taga Bbys ta makale tace bazata koma ba,Ummi tayi tayi Ammh Ayda ta makalema Malika tana Santin Kannenta,Dole su Ummi suka tafi suka barta wajen Hajiya,washe gari sai ga yan Malumfashi sunzo Duba Malika ,mota guda basu jima ba suka koma Dama ganinta sukazo yi,washe gari kuma sai ga yan kumo suma mota guda sunzo Duba Malika da zaratan magidantanta,wanda taji sauki sosai kamar ma ba”ayi mata aiki ba..
Joda ko da Saleema awaya suke kira suna ji kamar suyi tsalle suzo,saboda Zumudi ammh kuma duka mazajen nasu sunce sai sun Duba sun gani,ammh da Wuya su barsu suzo,Kwanan Malika 5 Aka sallameta ta koma gida Tunda taji Sauki sosai Dole Hajiya ta Dawo nan tana Kula da ita su merry na taimaka mata Tunda hidimar dayawa gata yan Biyu gata Ayda wacce ake Daga da ita sai ta Dauki Yan biyu,kuma ba dabam dabam ba,a”a so take abata ta dauka Duka biyu alokaci daya in ance bazata iya ba,sai tasaka kuka sai Babanta yazo ya Dauketa yayi ta lallashi ko yabata wayarshi ya Shigan mata game take Hakura..
Awannan karon ma Saleem ya Shirya Sunan Kece raini,Domin Sa guda Za”a yanka banda Raguna uku da kaji,Abun fa sai wanda ya gani,Ana gobe Suna Saleem yayima Yara Huduba da KABIR Da kuma ABDULMALIK Sunan daya Dadala Ran Malika Sosai Ganin yau ta Haihu da cikinta tama Daddylove takwara Shida Abbi,Abbi ma yayi murna Shima yayi bajinta Sosai,Maman Abba ma tazo ana gobe suna,Saleema ce Kadai ta samu Zuwa Joda kam tayi nisa dayawa,bama haka ba cikinta ya Tsufa mijinta yace baigama mata Shiri ba so yake in tazo to bazata koma ba sai bayan Ta haihu Dole ta hakura….
Sunan Zaratan mazan na Saleem an Shiryashi Domin Tun Ana gobe sunan Mota ta dinga sauke duk wani Nau’in Lemon sanyi na Sha da kuka sani sai da aka Saukeshi,duk kuma wani Ruwa na kowani kamfani Shima an Saukeshi Domin Taron gobe,Su Maman Abba da Saleema ko Tun daren Ranar suka Dinga Soye soyen Naman Raguna da kuma kaji,Domin bakin da zasu zo gobe yan Suna Duk da dai Duk yan”uwa ne da abokan arziki,Wannan karon ma Ummi akwati Hudu tayi na malika daya na Zaratan magidanta kuma Kowa daya daya,hakama Abbi yayi musu akwatina Shake da kaya na malika dana Takwaranshi da kuma mai Sunan Abokinshi.
Washegari Ranar Suna,Baki na nesa dana kusa Duk sun Hallara Jama”ar kumo ma sunzo,Jama”ar Malumfashi ma sunzo mota guda Domin taya Saleem murna Shida Malika,wacce ta kece cikin Shigan ta alfarma Kafafunta da hannayenta sun Dauki Shekin lalle ja da baki wanda yakara Fito da ita sosai,yan biyu ko Wadanda akeyima alkunya da AYYAN DA AYRAN suma an cakare su cikin kayan alfarma gwanin ban’Sha’awa wadanda suke kama da Ubansu sak kanar yayi kaki ya ijiye,Mganar Abinci ko,Reataurant ne guda Saleem ya yi odarsu suka zo suka baje kolinsu Kowani Nau’in abinci akwai su Awajen komai kake bukata aikwaishi Sai dai kaje ka diba son Ranka babu mai hanaka ko yayi maka iyaka.
Wajen Misalin karfe 12pm sai ga Motoci har biyu cike da Mata,Da farko anyi mamakin ganinsu ganin yadda suka ci angonsu cikin wani Leshi mai Ruwan Hoda wanda keda zanen kwalliyan green ajiki,kowacce ta daka Uban Dauri ta chaba ado ba Raini,Akallon Farko zakayi musu ka gane ba Raini don ba yaku bayi ba ne????,Sai bayan Sun Shiga ciki ne,Malika ta gansu sai fa Ta tuna su, Masoyanta ne daga HAFNAN AND JANAF PAID GROUP da kuma yan Amanata wato MALIKA MALIK PAID GROUP ,Nan da nan ta karbesu hannu bibbiyu ta hadasu da Maman Abba da Saleema tace aware musu daki na musamman,saboda bakinta ne,nan da nan ko aka Shiga ina aka saka dasu,Haka aka dinga jera musu Nau”o’in abinci da lemuka Kala kala gabansu bayan Uban Naman Rago soyayye da kuma Naman Kajin da suka dinga yi musu hy acikin manyan Filet din da aka Jirke agabansu,Tuni Su Sahiba Sarkin kwadayin Naman kaji,Tafara Hadiyan yawu kamar wata mayya ta mika hannu zata dauka Uwar dakina Chubado muhmmed ta kabe mata hannu tana Fadin”,Haba hafsy meye haka ki bari mana za”a baki kina Abu kamar baki taba ganin naman kaza ba,don Allah karki badamu mana Acp Saleem ya Shigo yaganki kina Halainiyar Naman kaza ya Rainamu..”tafada cike da yanga ammh itama cikin Zuciyarta da bakinta kwadayin Naman ne ke cinta ammt ta danne,itako Dotata ladingo kusan Abunka gamai ciki,????????miyanta har ya tsinke ta Kafe Ferfesun kayan cikin dake wajen da ido,Sisinah Aisha alto ganin haka yasa ta matso mata da kwanon gabanta tana Fadin”,Ci Abinki Diyarmu Shalelenmu ni da Janafty,kada ki kwari Jikanmu????Fadin haka keda Wuya Dota ta fara Sharban kayan cikin nan ko jinta tasu Maman kausar da Fati sadiq da suke mata Tsiya bata yi ba,Su Nazeefa ko da Ummu bilal,ummu bilal2 da Ummi haneef,sune manya sai wani manyance suke suna tsara komai,ammah Abun mamaki da sun Fakaici indon mutane sai su Tura hannu cikin Farantin Nama su debo su Tura cikin wasu manyan jakunkunan da suka zo dashi kamar zasu saka kan mutane Ashe saboda suyi Satan Nama ne????.
Hajiya Zuwaira ko da Kawa juwai,ko Suna barayin lemuka,sunfa sha har sunkusa amai ammh haka suka dinga Turawa har suna guzuri ajaka toh Abun ne dayawa Shiyasa babu Wanda yabi takansu,su Aisha amarya,su Aisha musa,su Amsopy,Asma”u Bafarawa,Asmau shehu,asmeey,Aisha usman,Bbj da bilkisu sani kuwa harda Fadan Fride rice,yadda kukasan basu taba ci ba????Sai da su Dijah Abdul da fatima Musa,ta niger,fati sadiq,Fatima Xahra da fee sai jikar hajiya,haleem Sweetheart dina,jidda lawan,khadee Noor,Khadija muhd manga,khadija usman,khadija bashir,momy h,mmn Nabila,,mm Teema,mmn Useey,mmn kausar,Mmn bby,mmn khairat,mmn Nazeer,mmn Rabia,mmn Ummulos,mmyn Abdul,murja bakugu,suka rabasu Alhalin suma kowacce ta cika jakanta da Awaran kwai da aka kawo musu,Sata ce taci sata,ba wacce bata sata tayi cikin Jakanta dashi ba,ammh suna raba wasu fadan Hinkafa????????,Ai Ba Abun Haushi sai yadda su Besty ta da Nucy girl,Rafi”atu,yar Fulani,Saleema Hamza,Sardiya,Ummi,my Azeeza,deejart,Fatima garba,Hadiza,mmn basma,mmn sayeed,mmn Baraka,Malika masoyiya,mmn Amira,mrs umar,Durlig Rukayyah,mumy Halil,Rouky,Suwaiba,mmn Sadiq,Nafisa,mmyn sani,mrs zainab jega,Fatima umar uwaisu,Shafa yola,wasila,Rafiatu s Rimi,Khadijat usman,Bilkisu Duwan,Suka Dinga bi suna kulla Duk Abincin da suka rage aleda suna Turawa ajaka da Nama ne,dasu lemuka,da Zuwaira da Nazeefa,da su Ummi bilal sukayi musu mgana cewa sukayi abarsu su jida,gida babu,bikin irin na Malika kuma sai Rabo ya Ratsa makota kuma sai daidai????????Sun dai ci sun sha don ko Sunan yan biyu sun fa goge Wuya Da Naman kaji Abun ba Dama.
Sai dai kuma da suka tashi Tafiya basu bar Malika haka ba,Kowacce sai da ta bata dan Abun suna,kafin suyi musu sallama su Tafi bayan kowacce ta cika jakanta da abubuwa,Malika ta rakasu har Wajen mota tana yi musu Fatan Sauka Lafiya,amotarma ma fa Allah ya tsare da anyi Dambe don Mmn Sadiq,ce da Sahiba suka so su kasa hali kan cinyar Naman kaza da Sahiba ta sato acikin Sikat dinta????Sai da Direba ya tsawatar yace kada wacce Ta kuskura tamai Fada amota kana kowacce ta Shiga taitayinta.????????????????????????????????