NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Neehal na na kitchen ta na yiwa Dad pepper chicken Mama dake falon a zaune ta na kallon labarai ta shigo kitchen ɗin ta na faɗin. “Neehal kin kusa gamawa.?” Neehal ta ce “Ehh na kusa.” Mama ta ce “Kawo in ƙarasa ki je falo Sadik ya zo.” Neehal ta juyo da sauri ta na duban Mama cikin fad’uwar gaban da ba ta san dalilin ta ba.” Mama ta ƙaraso cikin kitchen, Neehal ta na Ƙoƙarin fita Mama ta ce “Ki zuba masa abinci mana.” Neehal ta ce “Toh, hijab zan ɗauko.” Jiki a sanyaye ta ƙaraso ta zauna a kujerar kusa da shi bayan ta ajiye masa abinci a gabansa. Kanta a ƙasa ta ce “Ina yini.” Sadik da yake ta binta da kallo ya ce “Lafiya k’alau ya aiki.” Neehal ta ce “Alhamdulillah.” Sadik ya gyara zama cikin kulawa ya ce “Ba ki da lafiya ne na ganki wani iri.?” Neehal ta ce “Lafiya ta k’alau.” Sadik ya ce “Uhm, ko ki tambaye ni yau ina shiga.?” Neehal ta ce “Ai zan tambaye ka, dafatan dai Lafiya.?” Sadik ya ce “Lafiya lau, sha’anin aiki ne ya kawo haka.” Neehal ta turo baki gaba ba ta ce komai ba. Sadik ya yi murmushi cikin tsokana ya ce “Fushin me ki ke yi to.?” A shagwab’e ta ce “Ni ba fushi nake ba.”

“Uhm rigimar autanci ce ta motsa kenan.”

Neehal ta yi murmushi saboda yanda yay maganar ya bata dariya. Hirar su suka cigaba da yi cikin nishad’i, wani irin daɗi take ji saboda ganin Sadik, cikin lokaci kaɗan ta ware suka shiga hirarsu. Sadiƙ mutum ne da ya san takan bi da duk wanda yake mu’amala da shi, mutum ne mai tsananin kirki da hak’uri, gashi da sanyi kamar ba lawyer ba, sai dai akwai kaifin tunani da saurin fahimtar abu, ga uwa uba nutsuwa da addini. Abun da yake ƙara burge Neehal da shi nasiha da faɗin gaskiya a kodayaushe, ko yaya kuka ɗan zauna dashi sai ya tunatar da kai wani abu na addini da mu’amalar rayuwa. Mama ma yaron ya na burgeta, ta yaba da hankalinsa da nutsuwarsa, shi yasa ba ta hana mu’amalar su da Neehal.

Kwanci tashi babu wuya a gurin Allah, yau gashi bikin Ameen ya matso saura satittika, shirye-shiryen biki ake ba kama ƙafar yaro, ɓangaren gidan amarya da gidan Ango, ba yama kamar gidan su Amarya, dan su yanda suke tsara bikin ma sai anfi sati ana shagali, ango ne yake neman ba su cikas dan shi ya ce bashi da lokacin ɓatawa a yawon zuwa events, amarya dai ta na ta lallab’ashi a kan ya amince amma ya ƙi. Su Mama shirin su suke sosai ita da ‘yan’uwanta, Ameen ya saki kuɗi an haɗa lefe na gani na faɗa, Aunty Sadiya da Aunty A’isha ne suka haɗo masa. Ƴan’uwan Dad ma masu murna da auren ba a barsu a baya ba gurin nasu shirin.

Yau Saturday Misalin ƙarfe goma na safe Neehal ta na kwance a kan gadonta ta na bacci ta ji ana tashin ta, a hankali ta buɗe idanunta dake cike da barci ta na karanta addu’ar tashi daga bacci a zuciyarta. Ameerah ‘yar gidan Uncle Mahmud ta gani tsaye a kanta, yunk’urawa ta yi ta tashi zaune ta na mutsitstsika ido, Ameerah ta na murmushi ta zauna a bakin gadon ta na faɗin. “Bacci har wannan ranar Yaya Neehal.” Cikin murya mai cike da bacci Neehal ta ce “Kin san jiya muka gama exam, baccin da ban yi ba ne kwana 2 saboda karatu nake ramawa, yaushe ku ka zo?.” Ameerah ta ce “Yanzun nan, Mama ta ce in shigo in tashe ki.” Neehal ta ce “Welcome, ke da Ammi ku ka zo.?” Ameerah ta ce “Ehh, suna falo suna kallon lefe.” Neehal ta sauka daga kan gadon ta na faɗin, “Kin san nima har yau ban samu nutsuwar ganin lefen nan ba, saboda exams d’in da muke, gashi har za a kai gobe.” Ameerah ta ce “Ai dama exam akwai caza wa mutum kai, Allah dai ya ba da sa’a.” Neehal ta amsa da “Amin” tare da shigewa toilet.

Bayan ta shirya suka sauko ƙasa inda suka tarar da Mama,Hajiya,Ammi,Aunty Sadiya da Aunty A’isha sun baje kayan lefen a falon suna kalla, Ammin su Ameerah sai yaba kayan take ta na faɗin “Masha Allah kaya sun yi sosai”. Neehal ta ƙarasa ta rungume Hajiya cikin murnar ganinta ta ce “Hajiyata Oyoyo na yi miseed ɗinki.” Hajiya ta ce “Kamar da gaske, ina ja’irar k’awarki.?” Neehal ta ce “Daɗina dake ba’a miki gwaninta sai ki gwale mutum.” Hajiya ta ce “Na ji ɗin.” Neehal ta sake ta ta ƙarasa kusa da Amminsu Ameerah ta rungume ta tare da gaishe ta, Ammi ta amsa mata cikin fara’a da kulawa. Gaishe da su Mama da Aunties ɗinta ta yi. Mama ta dubeta ta ce “Ki je ki haɗa break fast ki kaiwa Yayanki, kema ki haɗa ki ci.” Neehal ta ce “Mama bari na ga kayan nan sai na kai masa.” Hajiya ta tari numfashinta da faɗin “Kayan da sun kusa sati a gidan nan, mak’ota da ƴan’uwa duk sun zo sun gani amma ke ki na kwana a gidan baki gani ba.” Mama ta bata amsa da faɗin “Ba ta wani gani sosai ba saboda ta na exam, kin san Neehal idan ta na exam ba ta da nutsuwa.” Aunty Sadiya ta ce “Yanzu dai an gama, sai a bita da addu’a Allah ya ba da sa’a.” Suka amsa gabad’aya da “Amin.” Neehal bayan ta gama ganin kayan ta mik’e ta shiga kitchen ta haɗawa Ameen break fast kamar yadda Mama ta bata umarni, tunda Ameen ɗin a gida ya kwana yau. Ta ɗauki kayan ta na duban Ameerah da ta taya ta haɗa kayan ta ce “Mu je ki raka ni na kaiwa Yayan.” Ameerah ta riƙe hab’a tare fito da idanunta waje ta ce “Wa? ki je ke kaɗai dai, kin san halin kayanki fa.” Neehal ta ce “Kar ki je ɗin, kuma sai na faɗa masa in ce kince masa masifaffe.” Ameerah ta ce “Allah ya na gani dai.” Ammi ta bi Neehal da kallo bayan sun fito harta fice daga falon, Ammi ta sauke Numfashi ta ce “Neehal har yanzu ba ta maida jikinta ba tun ramar da tayi lokacin rasuwar Anwar.” Mama ta ce “To bata son cin abinci, ba dole tai ta rama ba.” Ammi ta ce “Duk da rashin cin abincin ma, amma mutuwar na damunta a rai har yanzu.” “Ai dole ne ta damu Aunty Bilki, Samari har biyu sai an kusa bikinku duk su mutu.” Cewar Aunty Sadiya cikin jimantawa. Mama ta ce “Wlh nima abun na damuna ina tsoron kar ace sanadin Neehal ake kisan nan.” Cikin tarar numfashi Hajiya ta ce “Ashsha, faɗima ba na hanaki wannan zancen ba, yanzu idan wani ya ji ba sai ya samu abun ɗorarwa ba, tunda kema uwarta ki na faɗa, kun san mutane ba sa rasa abun fad’i, yanzu sai a gogawa yarinya baƙin fenti aita jifanta da sharruka kala_kala.” Mama ta sauke numfashi ta ce “Shikenan Hajiya Insha Allahu na dena faɗar haka, shima Dad ranar da na faɗa masa haka sai ya hauni da faɗa wai a kan me zance haka, Neehal ɗin me taiwa wani da zai dinga bibiyarta ya na kashe mata samarinta?” Aunty A’isha da ba ta ce komai ba tunda suka fara maganar sai yanzu ta ce. “To mu dai muna ga Allah, kuma shi zai warware mana gaskiyar al’amari, duk ma mai nufin wani da sharri Allah ya mayar masa kansa.” Suka amsa gabad’aya da “Amin.”

Ameen ya na cikin bedroom ɗinsa ya na shiryawa ya ji a na knocking k’ofar falo, sai da ya ƙarasa shirinsa a tsanake sannan ya fito dan zuwa ya buɗe, zuwa lokacin Neehal ta gaji da tsaiwa ga kaya a hannunta. Ya buɗe k’ofar tare da yin baya dan bata damar shigowa, Neehal ta yi sallama sannan ta shiga. “Yaya a ina zan ajiye maka?” Ta tambaye shi bayan ya amsa mata sallamar. Kan carpet d’in dake tsakiyar falon ya nuna mata, ajiyewa ta yi ta na sauke numfashi. Juyowa ta yi Ameen dake kallonta yay saurin ɗauke kansa tare da zama a kan kujera 2 seater. Neehal ta zauna a kusa da shi ta na kallonsa a ranta ta na gulmarsa ganin kamar ƙara kyau yake ya yi wani fresh abinsa, Neehal a ranta ta ce “Tun kafin a yi auren, wannan ina ga anyi auren.” “Ina kwana Yaya” ta faɗa cikin nutsuwarta. Ba tare da ya kalle ta ba ya ce “Lafiya, Ya exams.?” Neehal ta ce “Mun gama jiya.” Ameen ya jinjina kai ya na dubanta ya ce “Allah ya ba da sa’a.” Neehal ta ce “Ameen.” Daga haka suka yi shiru, Neehal ta na son ta tambaye shi abu amma ta kasa saboda sanin halin halinsa, wannan ƴar sakewar da ta samu ya mata yanzu sai ta nemeta ta rasa. Wayarta dake cikin aljihun rigarta ce ta fara vibrate, hannu ta zira ta ɗauko a tunanin Mama ta ce amma sai ta ga Sadik ne. D’agawa ta yi ta na murmushi ta kara a kunnenta. “Wa’alaikassalam Yaya Sadik ɗina.” Ta fad’i haka cikin murmushi mai sauti alamun ta na cikin nishad’in kiran da a ka mata. Ta ɗan yi shiru sannan ta ce “Lafiya k’alau and you.” Ameen dake kallonta ya tab’e ɗan ƙaramin bakinsa tare da ɗauke kansa daga kallon nata, da sauri kuma ya juyo amma cikin basarwarshi yanda ba za a gane saurin nashi ba jin ta na magana cikin shagwab’a “Dan Allah da gaske kake Ya Sadik? Kar fa kasa na fito kuma ba ka zo ba.” Sosai Ameen yake kallonta, Ƴar dariya ta yi sannan ta mik’e ta na faɗin “Gani nan to.” Kallon Ameen ta yi ta ce “Yaya ina zuwa, bari in je in dawo.” Ba ta jira amsarshi ba ta fara tafiya. Bin ta da kallo kawai ya yi cikin ransa ya na ƙissima abubuwa, har ta kai bakin k’ofa ya tsayar da ita ta hanyar faɗin………..✍️

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button