NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

By
Zeey Kumurya
⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

8️⃣5️⃣

Akwai ingantaccan maganin???????? gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah.

………Misalin ƙarfe biyu Ameen ya je gidan Mama, kamar ba gidan ne kwana biyu da suka wuce a cike fal da jama’a ba duk an fashe. Zulai da Dije ya tarar suna aiki ƙasa, sai wasu cousin’s sister ɗin Dad su uku a zaune suna hira, da yake su sai jibi za su wuce dan ba’a ƙasar nan suke zaune ba. Yana shiga suka fara tsokanar shi, ya zauna suka gaisa yana murmushi  sannan ya tashi ya nufi sama. Aunty A’isha da Amira da Ammi matar Uncle Mahmud ya tarar suna gyara a parlour’n. Bayan sun gaisa Aunty ta ce. “Yanzu muke shirin zuwa gidan naka ni da Amirah da Maryam.” Ya ce. “To ya naga ko shiryawa baku yi ba?” Aunty ta ce. “Muna ƙarasa aikin nan zamu shirya mu tafi.” Ya gyaɗa kai kawai sannan ya nufi ɗakin Mama. Mama tana haɗa kayan da ta yi fitar biki da su Aunty Sadiya tana taya ta ya shigo ɗakin da sallama. Suka amsa masa tare da kallon sa. Aunty Sadiya ta ce. “Ango ka sha ƙamshi, shine ka baro mun d’iyar tawa ita kaɗai a gida.” Murmushi kawai ya yi bai ce komai ba ya zauna tare da gaishe su. Yana kallon Mama ya ce. “Mum gajiyar bikin ce naga ko murnar gani na bakya yi?” Mama ta harare shi ta ce. “Ka san abun da ka yi mun ai.” Ya langwabe kai ya ce. “Yau kuma me na yi?” Aunty Sadiya ta yi murmushi ta ce. “Zai wuce akan maganar Hafsah ne.” Da ɗan mamaki ya ce. “Hafsah kuma?” Mama ta ce. “Ka yi mamaki da muka sani ko? Tunda kai baka sanar mana ba, yanzu Ameen abun da ka yi ka kyauta kenan?” Ya sunkuyar da kansa bai ce komai ba. Mama ta cigaba da yi masa faɗa, bata san me ya faru ba amma gaba-d’aya ta ɗora masa laifi.” Ganin yanda ta ɗauki zafi sai ya sanar musu da abun da ya faru ranar da ya kaiwa Hafsat kayan faɗar kishiya. Aunty Sadiya ta yi salati ta ce. “Gaskiya Hafsah bata kyauta ba, amma ta ɓata wayonta da wauta, tun yaushe aka daina irin wannan kishin, ina ganin ta wayayyiya ashe sakarya ce.” Mama ta ce. “Duk da haka da ka bita gidan nasu, ko kuma ka zo ka faɗa mana sai a sasanta ba sai maganar ta yi nisa ba, yanzu iyayenta baza su ji daɗi ba a ce tafi wata a gida amma ka ƙi zuwa, za su ga kamar wulaqanci ne.” Ya sauke numfashi ya ce. “Ita fa ta tafi da kanta Mum ba da iznini na ba.” Mama ta ce. “Duk dai da haka, haquri zaka yi, abun da haquri bai bayar ba rashin sa ma bazai bayar ba.” Ya ce. “Shikenan Mum insha Allahu zan je gidan nasu.” Mama ta ce. “Yaushe?” Ya ce. “I will select the day.” Mama ta ce. “Shikenan, Allah ya yi muku albarka ya kau da fitina a tsakaninku, Allah ya haɗa maka kansu, kai kuma ka zamto mai adalci a tsakaninsu, Allah ya baka ikon hakan kai ma.” Ya ce. “Amin, insha Allah.” Mama ta ce. “Tun ɗazu na yi girki gashi har rana ta yi ba’a kai muku ba, zaka tafi da shi ko su A’isha su tafi da shi?” Ya ce. “Daga nan ba gidan zan koma ba direct, zan biya can gidan Hafsah na ɗauko abu.” Mama ta ce. “Yanzu gidan babu kowa kenan a cikinsa?” Ya ce. “Daa da masu aikinta, last week na je su je gida kawai idan ta dawo sa dawo, mai gadi ne kawai a gidan.” Aunty Sadiya ta ce. “Allah ya kyauta.” Mama ta ce. “Ya Neehal ɗin? I’m trying her number bata shiga.” Ameen ya ce. “May be network ne, idan na koma zan kira ki sai na haɗa ku.” Mama ta ce. “Toh, ta ce ma tabar ɗayar wayarta a nan gidan, in zaka tafi sai ka tafin mata da ita.” Ya ce. “Okay, Ina tsohuwar gidan nan ne?” Mama ta nuna Aunty Sadiya ta ce. “Sai dai in wannan uwar taka ce tsohuwa amma ba tawa ba.” Aunty Sadiya ta yi murmushi ta ce. “Hajiya tana ɗakin Neehal na da tana bacci.” Ameen ya ce. “Aikin kenan.” Harararsa Mama ta yi, ya yi murmushi.

Ƙarfe Uku da ƴan mintuna Neehal tana ɗaki tana drying gashinta data manta tun safe bata yi ba su Aunty A’isha suka zo. Ta yi packing gashin ta d’aura ɗankwali ta fita parlour. Murna kamar ta kashe ta da ta ga su ne. Suka zauna suka ci abincin da suka zo da shi tare suna ta hira. Ana yin Sallar la’asar Aunty ta ce za su tafi. Neehal ta dinga roƙon ta kar su tafi su ƙara zama, harda hawayenta su Amira na yi mata dariya. Daƙyar Aunty ta yarda suka kai ƙarfe biyar a gidan.

Kwana biyun nan Hafsat ta yi su ne cikin k’unci tamkar tana cikin k’abari, idan ka gan ta sai ka ɗauka cuta ta yi duk ta lalace ta yi duhu. Yau tun safe ta je ta tasa mahaifiyarta a gaba da kuka, wai ta bar ta ta koma gidanta ita ta gaji da zaman nan, ta san halin Ameen bazai taɓa zuwa ba. Mom ta yi shiru bata ce komai ba, ita kanta al’amarin ya fara isarta, abun kunya ne a gurinta k’awayenta su san ƴarta ta yi yaji, kuma indai aka cigaba da tafiya a haka dole wataran su sani, gashi Ameen ya wuce duk inda take tunani, bata taɓa zaton za’a kawo har i yanzu bai zo ba, ta tabbatar da maganar Hafsah na cewa Ameen ya wuce duk inda suke tunani kuma ba ya ɗaukar raini da wulaqanci. Ta dubi Hafsat cikin tausayawa ta ce. “Ki yi haquri Daughter mu jira babanki ya dawo, ya ce wani aiki ne ya tsayar da shi amma insha Allahu next week zai dawo, idan ya dawo sai ya je ya samu mahaifin shi Ameen ɗin su yi maganar.” Hafsat ta gyaɗa mata kai ta ce. “To Mom ina son na je gidan Aunty Safiyya na yi kwana biyu, na gaji da zaman nan haka.” Mom ta ce. “Indai hakan zai saka ki ji daɗi to ki shirya anjima driver ya kai ki, kuma ki saki jikinki dan Allah kina cin abinci ko kya yi kyan gani ki ɗan ciko, idan shi Ameen ɗin ma ya gan ki a haka ai sai ya raina ki, ya ce saboda shi kika damu kanki haka.” Ita dai Hafsah bata ce komai ba, koma a yaya Ameen zai gan ta bata damu ba, ita dai fatanta Allah ya dai-daita su ta koma gidanta, babban abun da yake bak’anta mata rai idan ta tuna yana can tare da wannan shegiyar yarinyar data tsana, sai ta ji wani baƙin ciki ya cika mata zuciya, kamar zata haɗi zuciyar ta mutu. Bayan ta je gidan Aunty Safiyya ta ɗauki wayarta a b’oye ta kira Ameen tunda ita Mom ta ƙara k’wace wayartata, sai dai har wayar ta yi ringing ta gama bai ɗauka ba, dama ta yi tunanin hakan. Ta ji daɗin zuwanta gidan Aunty Safiyya, saboda yanda ta daɗa kwantar mata da hankali, ta ce tana nan tana shiri na musamman wanda zai saka dole Ameen ya zo da kukansa yana roqonta ta koma gidansa, lokaci kawai take jira a gama aikin.

Kafin Magriba Ameen ya dawo gida, lokacin Neehal tana zaune a falo tana karatun Alkur’ani kaɗaici ya ishe ta. Ya tsaya yana kallon ta bayan ya yi sallama yana shaƙar daddaɗan ƙamshin dake tashi a cikin parlour’n. Sai da ta kai aya sannan ta rufe Alkur’anin ta ajiye ta ɗago tare da amsa masa sallamar. Ya sakar mata murmushi sannan ya ƙaraso ya tsugunna a gabanta yana kallon ta kamar zai lashe ta. Ƙasa ta yi da kanta cikin sanyin murya ta ce. “Sannu da zuwa.” Ya ɓata fuska ya ce. “Haka aka welcoming ɗin miji dama?” Ta ɗan kalle shi ta ce. “To ya ake yi?” Ya ce. “Special hug and kiss to him.” Ta waro ido sai kuma ta yi saurin rufe fuskarta da hannunta. Ya yi murmushi a ransa yana ƙara hasko wani bambancin na Hafsat da Neehal wato kunya, Hafsat ko a ranar da aka kawo ta gidansa bata nuna kunya ba sam, hasalima da ya je ko irin kukan nan na amare bata yi, babu alamun ma ta yi dan idonta ragal da shi. Ya rungume ta a hankali cikin kulawa da k’auna ya ce. “I missed you so much baby love.” Ta yi shiru tana shaƙar ƙamshinsa tare da sakin ajiyar zuciya a hankali, tana jin wani abu yana yawo a cikin zuciyarta game da shi, kenan ita ma she missed him? Ya kama hannunta yana ɗan murzawa ya ce. “Have you eaten food?” Ta gyaɗa masa kai ta ce. “Kai fa?” Ya ce. “Na ci a gidan Mum.” Ɗago kanta ta yi daga ƙirjinsa tare da ɓata fuska ta ce. “Shine ka je gidan Mama baka tafi da ni ba?” Ya shafa kanta ya ce. “Kin taɓa ganin amarya ta fita kwana biyu da kaita inba wata lalurar ba?” Ta girgiza masa kai. Ya ce. “To kin gani, idan an kwana biyu sai na kaiki ko?” Ta gyaɗa masa kai sannan ta ce. “Ina wayata? Ko baka gama checking ɗin ba ne?” Ya gyaɗa mata kai yana shafa kuncinta. Ta ce. “To ka bani, ina son na kira Family and Friends na yi musu ban gajiya.” Ya ce. “Alright, Mum ma ta bani ɗayar wayarki da kika manta a gida.” Ya zaro ta a aljihunsa ya miƙa mata. Ta karɓa ta ce. “Contacts ɗina duk suna cikin ɗayar ai.” Ya ce, “To bari na ɗauko miki.” Ya sake ta ya miƙe ya shiga ɗakinsa ya d’auko mata wayar ya kawo mata. Ya zauna ya ce. “Ki bari a yi Sallah sai ki kikkira su.” Ta ce. “Toh.” Ya janyo ta jikinsa ya shiga aika mata da saqonninsa masu rikitarwa, sai da aka kira Sallar Magriba sannan ta samu ya k’yale ta. Bayan an yi Sallah ta shiga kiran wayar, Daddy ta fara kira sannan Mama sannan Haneefah. Da suka gama waya da Haneefah sai ta kira Ummin su Ahmad, suka gaisa ta yi mata ya suka je gida da bangajiyar biki gami da godiya sannan ta ce ta bawa Zahra wayar. Bayan ta bata sun gaisa ta ce. “Shine kuka tafi ba ku zo ba, aida ko twins kun kawo mun, amma sai tafiyar ku na ji kawai ko sallama babu.” Zahra ta ce. “Ki yi haquri, wallahi sai da na ce zamu zo washegarin da aka kaiki Ummi ta hana, na ce a kawo miki twins to shi ma Yaya ya hana ya ce sa zo miki wani lokacin.” Neehal ta ce. “Shikenan ina twins ɗin nawa?” Zahra ta ce. “Suna gidan Yaya.” Neehal ta ce. “Ki gaishe mun da su sosai, ko kuma ki turo mun ma numbern Aunty Khadijan sai na kira ta mu gaisa da su.” Zahra ta ce. “Toh shikenan zan tura miki.” Daga haka suka yi sallama ta katse kiran. Ta cigaba da kiran friends ɗinta da abokanan aikinta tana yi musu ban gajiya, har Batul k’anwar Sadik ma sai da ta kira. Ta yi mamakin yanda katin wayarta ya ishe ta wannan kiraye_kirayen, sai bayan ta gama ta duba ta ga ashe Ameen ne ya tura mata credit daga account ɗinsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button