NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Bayan Sallar Magriba Haneefah suka zo gidan ita da Mijinta Faruq, ta ƙara kyau abinta kana ganinta ka ga amarya. Mama ta tarbe ta cikin mamakin ganin ta tana faɗin “Yau Amarya ce a gidan namu?” Haneefah tana murmushi ta ce “Ni ce Mama, dama ina so in zo muku sallama jibi zamu wuce Kogi, ga kuma rashin lafiyar Besty, shine na ce mu zo yanzu kawai na duba jikin nata.” Mama ta ce “Har tafiyar ta zo? Sai yaushe kuma zaku dawo?” Haneefah ta ce “Sai week ɗin da za’ai resuming School.” Mama ta ce “To Allah ya kiyaye hanya, ki hau sama tana ɗakinta.” Ta amsa sannan ta wuce upstairs. Tana kwance rigingine tana latsa waya Haneefah ta shigo ɗakin da sallama. Ta d’ago kanta da sauri ido waje ta ce “Amarya!” Haneefah ta ce “Na’am Ango.” Neehal ta tashi zaune tana murmushi ta ce “Welcome dear.” Haneefah ta zauna a bakin gado kusa da ita ta ce “Yawwa ya jikin naki? Gaskiya kina jin jiki Besty duk kin rame.” Neehal ta ce “Da sauqi, ai na yi kyan gani ma yanzu.” Haneefah ta ce “Sannu, Allah ya ƙara sauƙi yasa kaffara ne.” Ta ce “Amin ƙawata, ina Yah Faruq?” Haneefah ta ce “Yana cikin Mota, tare muka zo.” Neehal ta ce “Shine kuma kika bar shi a waje, ki ce ya shigo mana.” Ta ɗauko wayarta a jaka ta kira shi ta ce ya shigo ciki. Neehal ta ce “Ko ke fa, ya amarci?” Haneefah ta ce “Mu sauka ƙasa ki tambayi Ya Faruq zai baki amsa.” Neehal ta yi murmushi. Sun ɗan taɓa hira Haneefah ta sanar mata tafiyarsu Kogi, Neehal ta musu fatan sauka lafiya. Sannan suka sauka ƙasa inda suka tarar da Ya Faruq da Mama suna hira. Haneefah ta ɗauki juice ɗin dake gaban Ya Faruq tana duban Mama cikin zolayarta ta ce “Mama shi ne ni ba’a kawo mun ba sai shi?” Mama ta ce “Ɗana kawai na sani, ke ai gidan ba baƙon ki ba ne.” Haneefah ta ce “Allah sarki ni Mama ta daina yina yanzu.” Faruq ya yi murmushi tare da yiwa Haneefah gwalo a fakaice. Sannan ya dubi Neehal suka gaisa yay wa Neehal ya jiki yana tsokanarta gawa ta ƙi rami. Ana kiran sallar isha’i suka tafi saboda daga nan gidan iyayen Faruq za su biya. Bayan fitarsu Mama ta zubowa Neehal abinci ta tilasta mata ta ci, tunda ta ji sauƙi har tana iya surutu abincin ma zata iya ci. Tana tutturo baki ta fara cin abincin kamar bata so, kaɗan_kaɗan take tsakurar sa tana kaiwa baki kamar mai irgawa, gashi Mama ta ce sai ta cinye wanda ta zubo mata duka. Tana zaune ita kaɗai a falo fiye da mintuna ashirin akan abincin da ba wani yawa ne da shi ba, Ameen da Hajiya suka shigo Falon. Hajiya ta ce “Ke kaɗai ina Faɗiman? ta bar ki ke kaɗai kuma ke da ba lafiya ba” Ciki_ciki ta ce “Tana sama.” Hajiya ta ce “To ya jikin naki?” Ta ce “Da sauqi.” Hajiya ta ce “Ke gashi kin warware, ita kuwa waccan da na je dubowa tunda na je tana nad’e akan gado, sai masu aiki ne ke ta kai kawo.” Neehal ta saci kallon Ameen wanda ya zauna akan kujera yana kallon Hajiya. Ta mayar da duban ta ga Hajiyan ta ce “To ai bata da lafiya ne.” Hajiya ta ce “Duk da rashin lafiyar, amma kuma da rakin tsiya ma, sai langwab’ewa take kamar lagwani.” Neehal ta ce “Dan ciwon ba’a jikin yake ba dole ki ce haka.” Hajiya ta wuce sama bata tanka ba. Ameen ya tashi ya koma hannun kujerar da Neehal take kai ba tabo ba fallasa ya ce “How was your body?” Kanta a ƙasa ta ce “Alhamdulillah.” Ya ce “Na ga kin ji sauqi har da magana haka.” Ta ce “Ya jikin Aunty Hafsat?” Ya ce “Da sauqi.” Ta ce “Allah ya ƙara sauƙi, ka yi mata sannu.” Idansa akan abincin da take ta juyawa da spoon ya ce “Zata ji.” Suka yi shiru dukan su, ita bata cigaba da jin abincin ba, shi kuma ya zuba mata ido. A hankali ta ji ya ce “Ki ajiye abincin mana idan kin k’oshi.” Ta ɓata fuska cikin shagwab’a ta ce “Mama ta ce dole sai na cinye, kuma da ƙyar nake ci bakina babu daɗi.” Sai kuma ta kalli fuskarsa iya gaskiyarta ta ce “Yaya ka cinye sauran Please kafin ta sauko.” Ya ce “Uhm, jagwalgwalon naki zan ci?” Ta kalli abincin dan ita bata ga wani jagwalgwalawa da ta yi ba, ta turo baki ta ce “Taimakona fa zaka yi Please.” Ya yi wani ɗan murmushi ya ce “Sai dai in zaki bani a baki.” Ta kalle shi da sauri ta ga fuskarsa babu alamun wasa ya sha mur, kamar bashi ya gama maganar yanzu ba.” Ta yi shiru ta rasa me zata ce, shi kuma ya tab’e baki irin zaɓi ya rage natan nan.” Jin taku ta d’aga kai ta kalli steps, ganin Mama ce ke saukowa sai ta ɗibi abincin ta kai baki tana yamutsa fuska kamar mai cin kashi. Mama ta dube ta bayan ta ƙaraso cikin falon ta ce “Tashi ki kai kitchen ki rufe, cin ɗan wannan abincin fiye da 30 minutes kamar mai cin gandar da bata gama dahuwa ba.” Ta miƙe da sauri ta nufi kitchen ɗin. Ameen ya raka ta da ido. Mama ta ce masa “Ya jikin Hafsan?” Ya ce “Da sauqi.” Ta ce “Allah ya ƙara sauƙi, da safe Insha Allahu zamu zo ni da Dad mu duba jikin nata.” Ya ce “Allah ya kai mu.” Daga haka ya miƙe yay mata sallama ya tafi. Bayan Neehal ta yi Sallah suka yi waya da Sadik, sannan ta kwanta. Kafin ta kai ga yin baccin Mama ta shigo ta yi mata allura wanda da ƙyar ta bari aka yi dan bata son allura ko kaɗan, gwara ta sha magani duk da shi ma ba wani son shi take ba, amma duk da gwara shi sau dubu akan allurar. Tana cikin rakinta da shagwab’arta bacci ya yi awon gaba da ita………✍️

By
Zeey kumurya
[10/03, 08:56] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

5️⃣2️⃣

Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 080662689511314#

……….A hankali take tafiya kamar bata son taka ƙasa, as always shi kuma tunda ya hango ta ya ƙura mata ido. Kanta a ƙasa ta ƙaraso cikin falon ta zauna a kan carpet ɗan nesa da shi tare da kawar da kanta gefe, su Afrah kuwa gurinsa suka nufa, wayoyinsa guda biyu ya basu bayan ya kunna musu game, cikin murna suka karb’a suka fara yi. Ba tare da ta kalli inda yake ba kamar an mata dole ta ce, “Ina yini.” Bai amsa ba sai tashi da ya yi ya dawo kusa da ita ya zauna ganin yanayinta ya kira ainihin sunanta. “Fateemah.” Ta d’ago ta dube shi cikin mamaki dan ko da can bai taɓa kiran ta da Fateemah ba. A hankali ta ce “Na’am.” Ya ce “Jikin naki ne har yanzu?” Ta girgiza masa kai, ya ce “To me ya faru na ga ranki a ɓace, ko nine ba kya son gani ko kuma kawo miki su Afrah da na yi ne ba ki ji daɗi ba?” Ta ɗan saki fuskarta ta ce “A’a ba komai Uncle.” Ya ƙara matsowa kusa da ita ya sassauta murya ya ce “To me yasa ba kya farin ciki, Please be happy, bana so na ganki a haka Pleaseee..” ya ƙarashe maganar da jan kalmar ƙarshe cikin wani irin wani salo da yasa ta ji wani iri a jikinta. Ta ɗan yi murmushi tana kallon shi ta ce “To na yi Uncle, ya kuka baro Mamy?” Shima yana murmushin ya ce “Lafiya k’alau, tana ta tambayar ki, ta yi zaton ma tare zamu zo.” Bata kuma cewa komai ba ta miƙa masa wayarsa dake hannunta, ya karɓa tare da faɗin. “Oh, na ma manta, thank you.” Yana ƙoƙarin zira wayar a aljihu ba tare daya latsa ta ba ta ce “An kira ka fa.” Ta yi maganar cikin ɓata fuska. Cikin mamaki ya zaro wayar ya duba dan ba permanent sim ɗinsa ba ne a ciki bai yi tunanin wani zai kira shi a wayar ba. Tab’e baki ya yi bayan ya ga mai kiran ya saka wayar a aljihu ba tare da ya bi bayan kiran ba. Neehal ta ɗauke kanta daga kallon sa ta ɗan turo baki gaba. Ya saka tafin hannunsa ya taɓa goshinta ya ce “Har yanzu da sauran zazzaɓi a jikinki Princess, kina shan magani kuwa?” Ta ce “Uhm.” Kawai. Ya ƙura mata cikin nazartar ta, ya lura kamar akwai abun da ke damunta tunda ta fito, ko kuma wacce ke cikin ɓacin rai. Ya ɗauke hannunsa daga goshinta ya d’ago hab’arta be serious ya ce “Neehal me yake damunki?” Ta lumshe idonta tare da girgiza masa kai tana ƙoƙarin saka hannunta ta cire nasa daga fuskarta. Ya riƙe hannun nata ya ce “Please talk to me Princess, ko kina so ki ganni a cikin damuwa nima?” Ta yi shiru. Ya ƙara tambayar ta, nan ma bata tanka masa ba. Ya sauke numfashi ya cire hannunsa daga hab’arta tare da sakar mata hannunta ya ce “Okay, Good bye Dear, tunda na fuskanci kamar nine ba kya son gani.” Ta buɗe idonta da sauri sai hawaye sharr wanda bata san sanda suka zubo ba. Ya dafe kansa tare da faɗin “Oh my God, Dan Allah Princess me yake damunki ne, ko na miki wani abun ne da baki ji daɗi ba?” Ya yi maganar a ɗan ruɗe yana kallon ta. Ita kanta bata san me ya saka ta a cikin wannan yanayin ba, kuma ta yi ƙoƙarin ta danne kar ya fuskanta amma ta kasa. Ta turo baki gaba sosai ta ce “Ka ce mun tunda Maman twins ta rasu baka ƙara kula wata mace ba, and now kuma naga wata ta kira ka harda text, who is she?” Ta yi maganar iya gaskiyar ta. Sai yanzu ya gane bakin zaren, shi dariya ma ta ba shi ba kaɗan ba, amma yanda take a sama ɗin nan in ya dara ya san da matsala, musamman yanda ta tsare shi da kyakkyawan idanunwan nan nata tana jiran amsa. Ya danne dariyarsa ya ce “Oh wai Jamila, she is my cousin, ƴar ƙanwar Dad ce.” Ta juya masa idonta ba tare da ta ce komai ba, amma bata gamsu da abun da ya faɗa ba. Ya yi ɗan murmushi tare da matsowa daf da ita, ya kai bakinsa dai_dai saitin kunnenta ya ce “Princess ce kaɗai a zuciyar Uncle ɗinta, since, now and for ever, daga ita kuma babu ƙari.” Ta rufe fuskarta da hannunta cikin jin kunyar gano ta da ya yi. Ya yi ƴar dariya ya ce “Ashe Babin Uncle ta fara sonsa har da su kishi?” Ta juya masa baya a shagwab’e ta ce “Ni ba kishi nake ba?” Ya ce “To me kike? Jealous? Kamar zata yi kuka ta ce “Ni fa Allah ba kishi nake ba.” Ya juyo da ita da hannunsa ya sa tafin hannunsa ya share mata hawayen data zubar d’azu, zuciyarsa fess da yanda ta nuna tana kishin nasa. Ya zubawa fuskarta ido yana jin kamar ya mayar da ita cikin jikinsa saboda k’auna. Jin maganar Afrah a kusa da shi yasa ya ɗauke idonsa daga kallon ta ya mayar kan yarinyar da take miƙo masa wayarsa tana faɗin “Daddy kiran Sallah ake a cikin wayar.” Ya karɓa ya ce “To aje a yi alwala a yi Sallah.” Ta ce “Tom Daddy.” Ya yi mata kiss a goshi itama ta mayar masa tana dariya sannan ta nufi upstairs da ɗan gudunta tana cewa Amrah sai ta riga ta hawa saman. Jin haka itama Amrah ta kawo masa ɗaya wayar ta bi bayan ta. Neehal ta bi su da kallo cikin k’auna. Ya ce “Princess zan wuce?” Ta juyo ta ce “Sai yaushe?” Ya ce “Gobe da safe Insha Kafin na wuce.” Ta ce “Allah ya kai mu.” Ya miƙe tsaye yana faɗin “Amin.” Itama miƙewar ta yi, ya ja karan hancinta ya ce “Bye, I love You.” Ta ce “Allah ya kiyaye.” Ya ɓata fuska tare da langwab’ar da kansa ya ce “Ba feedback?” ta yi murmushi bata ce komai ba, ya ce “Shikenan.” Ta ce “Thank you for coming, and…” “Kawo miki twins ko?” Ya ƙarasa mata dan ya san haka zata faɗa. Ta yi murmushi tare da gyaɗa masa kai. Ya yi mata murmushin nan nasa mai kyau tare daga mata hannu sannan ya juya ya tafi. Ta sauke ajiyar zuciya bayan ya fice, a ranta tana faɗin ‘Ko sallama bai yi da ƴaƴansa ba.’ Ta juya ta haye upstairs, ɗakin Mama ta shiga ta tarar da ita tana ƙoƙarin shimfid’a darduma, su Afrah suna taya ta. Amrah ta ce mata “Aunty ina Daddy? Ya tafi?” Ta ce “Eh ya tafi gidan Mamy, amma gobe da safe zai dawo.” Mama ta ce “Ki je ki yi alwala ki zo ki yi Sallah, tunda kin warke sai ki shiga kitchen ki yi masa something special gobe in ya zo sai ki ba shi ya tafi da shi” Ta ɓata fuska ta zauna a bakin gado ta ce “Mama ban fa warke ba, cikina ma tun safe ya fara mun ciwo.” Mama ta ce “Allah ya sauwaqe.” Daga haka ta tayar da Sallar ta. Miƙewa ta yi itama ta shiga toilet ta fito ta tayar da Sallar.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button