NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Bayan wasu mintuna yana cikin aikin lokaci ɗaya ya yarda wayar hannunsa da system ɗin gabansa a matuƙar gigice. Ya shiga bubbuga hannunsa akan goshinsa yana maimaita kalmar Innalillahiwa’inna’ilaihirraji’un a fili. Ya miƙe tsaye idanunsa a lumshe, wani irin jiri ya ji ya kwashe shi hakan yasa ya yi saurin dafe hannayensa a jikin bango, ƙirjinsa na d’agawa saboda yanda zuciyarsa take bugawa. Ya daɗe a haka kafin ya zame ya zauna a ƙasa hannunsa dafe da ƙirjinsa, idanunsa sun yi ja jajur. Cikin wata irin murya dake nuni da tsantsar tashin hankali yake faɗin. “Ya Allah…! Dad why? Why?” Yana jin wayarsa tana ringing amma ko kallon inda take bai yi ba. Sai da ya ga Magriba tana ƙoƙarin yi sannan ya lallaɓa ya tashi da ƙyar ya ɗauki wayarsa ya kira wani abokinsa jami’in SS, ba tare da tunanin komai ba ya sanar masa da buƙatarsa tare da ƙudirinsa akan Daddy. Sannan ya koma ya kwanta akan gado ruf da ciki, yana son ya ɗauki system ɗinsa ya cigaba da duba abu amma ya san ko ya ɗauka babu abun da zai gane a cikinta, balle har ya fahimci wani abu. Duk wani bincike da zai yi akan al’amarin Neehal ya yi kuma ya gano komai duk abun da yake son gani, sai dai ya yi da na sanin yin binciken, da ya san abun da zai binciko kenan da tun farko bai fara binciken ba. Duk yanda mutum yake tunanin tashin hankalin da Ameen yake ciki ya wuce nan, mahaifi fa! Mahaifinsa wanda yake matsayin uban Neehal a yanzu amma shine da aikata mata wannan abubuwan? A matsayinsa na babban jami’in tsaron ƙasa mai ƙoƙarin ganin ƙasar sa ta gyaru tare da kama duk wani ɓata gari amma shine da kansa a cikin ɓata garin. Shine dalilin da ya saka kenan ya hana shi Auran Neehal ashe yana da wata manufar ne a kanta? Tambayar da yake ta yiwa kansa wanda ba shi da mai ba shi amsa me yasa Daddy ya shiga wannan ƙungiyar? Wanne irin rud’in shaid’an ɗin ne da huɗubar mummunar zuciya suka ɗebe shi ya faɗa cikin halaka ta duniya da lahira? Babban tashin hankalinsa ɗaya halin da Mama zata shiga idan ta ji Daddy ne ke aikata duk waɗannan abubuwan. Ya zata ji? Ya duniya zata ɗauki maganar? Wata zuciyar tasa kuma ta kasa yarda cewa Mahaifinsa ne da wannan ɗanyen aikin, tana ta faɗa masa ya sake bincike may be gaskiya ta bayyana, wataƙila wani ne ya shiryawa Dad ɗin haka, ko kuma wasu abokan nasa suke wannan harkar yake bin su amma shi ba ya yi? Ko ko ko…….Babu abun da bai kissima a ransa ba dangane da wannan harkar da Daddy yake yi. Ya fara bibiyar al’amarin Neehal ne tun lokacin da aka biyo ta har cikin gidansa, ada baya ɗaukar abubuwan da suke faruwa da wata manufar, ya yi zaton daga Allah ne kawai, sai lokacin zuciyarsa ta fara yi masa kokwanton tabbas da wata a ƙasa. A yau ya ji duniyar tay masa zafin da bata taɓa yi masa irinsa ba a rayuwarsa, ya ji ya tsani kansa da Daddy, bai san da idon da zai kalli Mama da Neehal ba, a ce Mahaifinsa wanda Neehal takewa kallon Uba a gare ta shi yake aikata mata haka? Tsananin tashin hankali da damuwar da Ameen ya shiga a yau baza ta faɗu ba. Har bayan Sallar isha’i yana kwance a inda yake cikin mawuyacin halin damuwa, zuciyarsa na k’issima masa abubuwa mara sa kyau a kansa, harda wacce ta bashi shawarar ya kashe kansa saboda damuwa da tsananin takaici da kunyar duniya. A hankali ya fara dawowa cikin nutsuwarsa da taimakon Innalillahiwa’inna’ilaihirraji’un da yay ta maimaita a cikin ransa. Hakan yasa ya iya tashi dariyar cikin k’unar zuci, bai bi takan wayarsa da ake ta kira ba da bugun ƙofar da Hafsat take masa ya shiga toilet ya ƙara watsawa jikinsa da ya ɗauki zafi ruwa tare da dauro alwala. Ya fito ya xora jallabiya ya tayar da Sallar Magriba da isha’i dake kanshi. A kowacce sujjada yana roƙon Allah yasa mafarki yake ba gaske ba ne abin da binciken sa ya nuna masa, tare da roƙon ya farkar da shi cikin gaggawa, ko kuma idan ma gaske ne Allah yasa ba Daddy ba ne, wani ne daban gaskiya zata bayyana a gaba…….

Aunty Sadiya tana tsaye a bakin window’n ɗakin da Mama take tana lek’enta cikin tsananin tausayawa, Maman na kwance akan gadon ƙaramin ɗakin da take ita kaɗai an saka mata robar numfashi (Oxygen) a hancinta. Doguwar ajiyar zuciya ta sauke ta lumshe idonta ta buɗe sannan ta yi baya ta zauna akan kujera tana sauke numfashi cikin yanayin tsantsar damuwa. Wayarta dake hannunta ta latsa, hakan ya yi dai-dai da shigowar kiran mijinta cikin wayar Barrister Ahmad. Ta d’aga tare da karawa a kunne gami da sallama, bayan ya amsa mata cikin taushin murya ya ce. “Haleemah ya jikin Yaya Fateemah da Neehal?” Aunty Sadiya ta sauke numfashi ta ce. “Da sauqi Habibi, naga Ya A’isha ta mun text ta ce Neehal ta farfaɗo, Yaya Fateemah kuma gata nan a kwance har yanzu dai shiru.” Uncle Ahmad ya ce. “Masha Allah, itama Yayan Insha Allahu zata farko cikin k’oshin lafiya, damuwar data riske ta lokaci ɗaya ne yasa ta cikin wannan halin.” Aunty Sadiya ta ce. “Allah yasa.” Uncle Ahmad ya nisa ya ce. “Komai zai wuce Insha Allah, gobe da sassafe nima zan taho Kanon sai mu je can inda Yaya Tafida yake mu san ya za’a yi da case ɗin.” Aunty Sadiya ta ce. “Ɗazun nan Yaya Hamza (Abba) ya bar asibitin nan, kuma daga can inda aka tafi da Daddy yake, ya ce sun ƙi bari ma ya gan shi, sun ma ƙi saurarar shi balle a yi magana.” Uncle Ahmad ya ce. “Kin san case ɗin nan ba ƙaramin case ba ne, musamman ma da bamu san evidence ɗin da Ameen ya ba su ba, amma Insha Allahu zamu yi iya yin mu wajen ganin Yaya Tafida ya fito, su kuma sauran ƴan ƙungiyar an kama su.” Aunty Sadiya ta sauke numfashi ta ce. “Barrister kana ganin Yaya Tafida zai iya fita daga cikin case ɗin nan kuwa? Su kuma sauran ƴan ƙungiyar a iya kama su?” Uncle Ahmad ya ce. “Insha Allah Habibty, babu abun da ya fi ƙarfin Ubangiji, bincike kuma shi zai bayyana gaskiya.” Aunty Sadiya ta ce. “Haka ne.” Uncle Ahmad ya ce. “Ameen ɗin ya zo asibitin kuwa?” Ta ce. “Ina ta kiran wayarsa ba ya pick.” Ya ce. “Allah yasa dai lafiya yake, ki cigaba da kiran sa, Insha Allahu za’a yi sa’a ya ɗauka.” Aunty Sadiya ta ce. “Toh.” Daga haka suka yi sallama ta katse wayar. Layin Ameen ta kira. Har lokacin yana zaune akan sallaya hannunsa dafe da kansa. Yana jin kira ya shigo cikin wayarsa, kamar ya share sai kuma ya yi wani tunani, ya san definitely cikin kiran da ake ta yi masa baza a rasa na Mama ba, rashin ɗaukar mata waya kuma zai ƙara saka ta a cikin damuwa, hakan yasa ya miƙe da sauri ya ɗauko wayar a inda ya yasar da ita cikin tsananin dauriya saboda wani irin juyawa da kansa yake masa. Ganin Aunty Sadiya ce yasa ya ɗaga wayar ya saka ta a handsfree amma bai ce komai ba. Cikin sauri Aunty Sadiya ta ce. “Ameen ina ka shiga ne yau?” Shiru ya yi bai bata amsa ba. Ta kuma cewa. “Kana lafiya Ameen? Ka yi magana mana.” Ya runtse idonsa numfashinsa na fita da sauri da sauri cikin matuƙar sanyin murya ya ce. “I’m fine.” Aunty Sadiya ta sauke ajiyar zuciya ta ce. “Masha Allah.” Cikin matuƙar damuwa ya ce. “Ina Mum?” Ta ce. “Muna tare da ita, tun d’azu take kiran ka tana son magana da kai amma baka pick call ɗin.” Ajiyar zuciyar shi ma ya sauke ya ce. “Zan zo yanzu in gan ta.” Aunty Sadiya ta ce. “Ba ma gida, muna Hospital.” A ruɗe ya ce. “What? Kuna me? Waye ba shi da lafiya?” Aunty Sadiya ta ce. “Neehal ce bata jin daɗi.” Ya taune lip ɗinsa da ƙarfi sannan ya ce. “Wanne asibitin kuke?” Ta ce. “Nasarawa.” Ya ce. “Okay gani nan zuwa.” Bai jira amsarta ba ya katse kiran. Mukullin Mota kawai ya laluba ya buɗe ɗakin ya fita. A falo ya tarar da Hafsat zaune idanunta sun yi jajur alamun ta ci kuka ta k’oshi, ta bi shi da kallo zuciyarta fal kishi. Ya ɗan tsaya yana kallon ta. Miƙewa ta yi ta tako gabansa tana kallon sa cikin firgicin ganin yanda ya fice daga hayyacinsa a yini ɗaya. Ta fashe da kuka a hankali cikin kukan ta ce. “Meke damun ka Al’ameen da ka yi wannan ramar lokaci ɗaya? Tun d’azu ka rufe kanka a ɗaki ka bar ni cikin zullumi da damuwa, ka san kuma dole hankalina zai tashi.” Lumshe idonsa ya yi cikin k’unar zuci, ya san bai kyauta mata ba tunda bata da masaniyar abun da yake faruwa balle tay masa uzuri akan halin da yake ciki. Bai ce komai ba ya kama hannunta da hannunsa ɗaya, ɗayan kuma ya shiga share mata hawayen fuskarta. Ta kwace hannunta tare da faɗawa jikinsa ta rungume shi. A hankali ya kai hannunsa ya ɗan bubbuga bayanta alamun rarrashi, kafin ya zare ta daga jikinsa ya zaunar da ita akan kujera ya fice daga falon ba tare ya yi magana ba. Ta bi shi da kallo cikin tsananin takaici, a tunaninta duk wannan halin da yake ciki saboda Neehal ne, wutar kishi da tsanar Neehal ne ke ƙara ruruwa a cikin ranta. Ita kam wannan shegiyar yarinyar ta zame mata ƙarfen ƙafa a tsakaninta da mijinta, amma zata yi maganin abun, dole ne ta yiwa tufkar hanci tun kafin dare yay mata ta zo tana kuka da idanunta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button