NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

By
Zeey Kumurya
⚡ NEEHAL⚡

8️⃣7️⃣

By
Zeey Kumurya

ELEGANT ONLINE WRITER’S

Washegari tun safe Mama ta kira Ameen ta ƙara yi masa tuni akan zuwansa gidansu Hafsah. Da yamma ya shirya cikin manyan kaya light blue ɗin shadda. Neehal tana fesa masa turare ta ce. “Ka yi kyau fa sosai Yayana.” Ya yi murmushi ya ce. “Duk wannan shiryanin da kike yi fa ba sai saka in fasa zuwa zancen da na yi niyya ba.” Ita ma murmurshin ta yi ta ɗauko agogon da zai saka ta fara saka masa ta ce. “Ai bazan so ma ka fasa zuwa ba, ni me iya raka ka zancen ne ma.” Ya janyo ta ya zaunar akan cinyarsa ya ce. “Kar fa ta yi miki duka budurwar tawa, ta ce dan iyayi kin rako saurayinta zance.” Ta juya masa ido ta ce. “Idan ta san me take yi she will never do that.” Ya yi murmushi tare da sauke ta ya miƙe tsaye ya kwashi wayoyinsa. Har bakin Mota ta raka shi ta yi masa addu’a, sai da rungume ta sannan ya shiga Motar ya tafi. Haka kawai ta ji zuciyarta babu daɗi bayan fitarsa dan ta san gurin Hafsat zai je. Wani abu wanda ta tabbatar kishi ne ya tokare mata a ƙirji. Ganin abun na neman yin yawa sai ta kunna karatun Alkur’ani a speaker, tana saurara tana kuma bi a hankali.

Cikin mintuna ƙalilan Ameen ya ƙarasa gidansu Hafsah. Ya yi horn mai gadi ya buɗe masa tangamemen gate ɗin gidan. Ya shiga ya ƙarasa parking space ya yi parking, a ransa yana tunanin ko yaya zai ga Hafsah da irin tarb’ar daza ta yi masa. Har yanzu haushin abun da ta yi masa bai bar cikin ransa ba, dan Mama kawai ya zo wannan bikon. A hankali ya fito daga cikin Motar cikin takunsa na nutsuwa da ƙasaita mai ɗaukar hankali. Ɗaya daga cikin yaran gidan ya aika domin ya yi masa iso. A ɓangaren Hafsah tun ranar data je gidan Aunty Safiyya bata dawo ba sai jiya, shi ma dan saboda yau da daddare Dad ɗinta zai dawo ne. A yau kuma Aunty Safiyya ta zo ta kawo mata magunguna da zata yi amfani da su wanda zai saka Ameen ya zo gare ta. Tun a yau ɗin ta fara amfani da magungunan, ta sha na sha ta turara jiki dana turarawa suka binne na binnewa. Aunty Safiyya ta tabbatar mata da a cikin kwanakin nan Ameen zai zo, dan aikin malamin da ya bayar da magungunan tamkar yankan wuqa yake. Aunty Safiyya ta ɗora mata da huɗubar banza ta rashin mutunci da jan ajin da zata yiwa Ameen idan ya zo.

Suna zaune a main parlour’n part ɗin Mom suna hira, masu aiki nata kaiwa da komowa suna shiryawa mai gidan delicious ɗin tarb’ar shi. Wanda Ameen ya turo ya shigo cikin girmamawa ya sanar musu da zuwan Ameen. Da sauri Hafsat ta kalli mahaifiyarta ta kalli Aunty Safiyya. Mom ta ce ta bayar da umarnin a je a shigo da Ameen ɗin. Aunty Safiyya ta ce. “Kin ga aikin Malam ko Hafsat? Zaki ga yanda zai rud’e yana roqonki ki zo ku tafi, ke kuma ki ja class ɗinki ki gaggasa masa maganganun da na ce miki.” Hafsah da farin ciki ya cika mata zuciya saboda zuwan Ameen ta ce. “Insha Allahu Aunty, abun da kika ce babu fashi.” Mom ta miƙe ta ce. “Bari na shiga ciki kafin ya shigo in fito in yi masa wankin babban bargo nima.” Aunty Safiyya ta miƙe ta bi bayanta. After 3 minutes Ameen ya shigo parlour’n bakinsa ɗauke da sallama. Lokaci ɗaya daddaɗan ƙamshinsa ya cika parlour’n, Hafsah ta lumshe idonta tana jin yanda ta yi missing ƙamshin over a cikin ranta, Sai dai kuma ta ji ƙamshin nasa ya ɗan sauya ya sirka da wani, wanda ko tantama bata yi na Neehal ne, dan is like humra ta mata. Ta buɗe idonta tare da haɗe rai wani zafi ya ziyarci zuciyarta data tuna zuwa yanzu fa ya haɗa jiki fa da wannan yarinyar. Ko kallon inda yake bata yi ba balle ta amsa masa sallamarsa. Idanunta suna kan TV. Kansa ya yiwa mazauni a kujerar dake facing ɗin tata, ya shiga bin ta da kallo cikin mamakin yanda ta share shi. Ya danne zuciyarsa ya ce. “Hafsah Ya kike?” Ta juyo ta yi masa wani mugun kallo gami da harara ta murgud’a masa baki. Sandarewa Ameen ya yi saboda tsananin mamaki ya tambayar kansa abun da take nufi da hakan, ita da yi masa laifi ita ce kuma da yin fushi lallai akwaita da ƙarfin hali. Hafsah da duk zaton ta aikin Malam ne ya yi aiki ga Ameen har ya zo gidansu a yau ta miƙe cikin tsiwa da rashin kunya ta ce. “Ameen me ya kawo ka inda nake? Baka yi auranka ba ka wofantar da ni saboda butulci da rashin tabbas irin naku na maza? Sai yau zaka kwaso jiki ka zo gurina, ni kuma ga sauna sai na washe maka baki na bi ka ko?” Ran Ameen ya fara ɓaci amma bai ce komai ba sai kallon ta kawai yake. Hafsah da zigar Aunty Safiyya take yawo a cikin kanta ta ce. “Ka tashi ga ƙofa nan ka koma inda ka fito, ni Hafsat na gama Auranka har abada Ameen, kuma ina roqon ka da Allah ka sauwaqe mun ƙaddararre Auran ka, dan bazan iya zama da kishiya ba.” Ran Ameen fa ya kai matuƙar ɓaci, a fusace ya buɗe baki zai yiwa Hafsah magana sai kuma ya fasa ya shiga furzar da zazzafan huci. Hafsat ta tab’e bakinta ta ce. “Idan ka cika dan Halak cikin Fateemah da Muhammad in ga takarar sakina a yau ba’a gobe ba.” Cikin matuƙar fusata Ameen ya miƙe tsaye yana jifan ta da wani irin kallo, idanunsa har sun fara sirkawa zuwa ja saboda tsananin ɓacin rai. Ya yi ɗan taku ya ƙarasa gaban Hafsah ya ce. “Hafsat kin san me kike faɗa kuwa? Kina cikin hankalinki kuwa? Ni kike faɗawa haka?” Kafin Hafsah ta yi magana muryar Mom ta karad’e parlour’n da faɗin. “Sannu Ameen, na ce sannunka.” Duk da yanayin ɓacin rai da yake ciki amma haka ya tsugunna ya shiga ƙoƙarin gaishe ta. Ɗaga masa hannu ta yi ta ce. “Riƙe gaisuwarka bana buƙata, yanzu kai Ameen dan baka da kunya ka iya takowa ka zo cikin gidan nan bayan wulaqanci da tozarcin da ka yi mata, ka yi mata kishiya sannan kuma ta taho gida ka ƙi biyo bayanta saboda gaka ishashshe ko? Ka fi ƙarfin zuwa biko. To bari ka ji in faɗa maka in baka sani ba ka sani, ƴata ta fi ƙarfin wulaqancin ɗa Namiji wallahi, me kake da shi? Me kake t’akama da shi? Abun takaicin ma ka rasa da wa zaka haɗa ta kishi sai da yarinyar da asalinta ubanta ba kowa ba ne, ƴar matsiyata da matsiyatan danginta suka kasa riqe ta.” Aunty Safiyya dake bayanta ta tari numfashinta tana turo d’auri gaban goshi ta ce. “To ai Yaaya abun duk shiri ne, shiryawa aka yi, wannan munafukar uwar tasa ce ta shirya komai.” Da sauri Ameen ya miƙe idanunsa sun yi jajur, ba zai iya jurar wannan cin mutuncin ba, abun ya bar kansa ya koma kan Baby love ɗinsa amma duk bai ishe su sai sun haɗa da mahaifiyarsa? Ba ƙaramin danne zuciyarsa ya yi ba na ƙin mayar musu da martani, ya juya kawai ya fice daga parlour’n ransa a matuƙar k’ololowar ɓaci. Bayan fitarsa a tsorace Hafsat ta ce. “Na shiga uku Aunty, maganin nan fa kamar bai yi masa aiki ba, ina jiran na ga ya yi kneeling a gabana yana bani haquri tare da bagging ɗina sai na ga ya tashi kamar zai dake ni.” Ita ma Aunty Safiyya jikinta ya yi sanyi. Amma cikin ƙarfin hali ta ce. “Ya yi masa mana, ke baki lura ba da yanayinsa ba ne? Shegiyar tattaurar zuciyarsa ce ta saka bai nuna ba, amma muna nan dake abun zai cijo sa ne zaki ga ya dawo ni na faɗa miki, ke dai ki cigaba da yin yadda na ce miki kar ki yi kuskure.” Hafsat ta koma ta zauna tana sakin ajiyar zuciya, ita dai tsoronta ɗaya kar ta rasa Ameen.

Tun bayan fitar Ameen ba jimawa Neehal tana zaune ta ji cikinta na ɗan juya mata kaɗan_kaɗan, ko kusa bata yi tunanin period zata yi ba, sai da cikin ya ɗan murɗa mata ta ji abu ya fara fita daga jikinta sannan ta yi realising. Mamaki ne ya kamata ganin yau sau ɗaya a rayuwarta tunda ta fara period ya zo mata ba tare da ta sha wahala ba. Ta miƙe ta shiga ɗakinta ta kimtsa kanta sannan ta kwanta akan gadon dan ba normal take jin ta ba, cikin ya ɗaure mata kamar kodayaushe idan tana period. Ikon Allah ne ya kawo Ameen gida lafiya dan saboda ɓacin rai ko ganin gabansa sosai baya yi. Neehal ta yi murmushi jin shigowar motarsa, duk da bacci ya fara fizgarta amma ta yage shi ta miƙe dan tarb’ar mijinta, zuciyarta cike fal da tsokanar sa da zata yi. A falo suka ci karo, ta tsaya turus tana kallon shi kamar wani mayunwacin zaki yanda yake huci. Cikin mamakin yanayinsa ta ce masa. “Sannu da zuwa.” Bai ko kalli inda take ba ya tura ƙofar ɗakinsa ya shiga ya banko ƙofar da ƙarfi. Cikin fad’uwar gaban ganin yanayin da ya shigo ta bi bayan shi, amma tana tura ƙofar sai ta ji ta kulle. Ta tsaya tana kallon ƙofar kamar zata gan shi a jikin ƙofar sannan ta juya ta bar gurin zuciyarta babu daɗi. Zama ta yi akan kujera tare da yin tagumi da hannu bibbiyu tana tambayar kanta me ya ɓata masa rai haka? Tashi ta yi ta ƙara komawa bakin ƙofar ɗakin nasa ta shiga yin knocking amma ta ji bai buɗe mata ba. Sai ta ji haushi ta koma ɗakinta ta kwanta, ita ba ita ta yi masa laifi ba amma shine zai yi mata haka, tana yi masa magana ya share ta ya shiga ɗaki ya kulle, ta bubbuga masa ƙofa kuma yana ji ya ƙi buɗewa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button