NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Hafsah ce ta shigo ɗakin yanayin ta kamar tana cikin damuwa. Hajiya ta dube ta ta ce. “Ke wai ina mijin naki ne? ban gan shi ya zo yau ba.” Cikin damuwa alamar an sosa mata inda yake mata k’aik’ayi ta ce. “Wallahi Hajiya ban sani ba, rabo na da shi tun jiya da yamma, dama ya ce mun dak’yar in zai je gurin dinner. To kuma yau tun safe nake kiran wayoyinsa duka a kashe.” Hajiya ta ce. “Subhallahi, an shiga uku, kar dai baƙin halin Aminu har ya kai ya ƙi zuwa d’aurin Auren Yar’uwarsa guda ɗaya jal a duniya.” Neehal tay karaf ta ce. “Ni Yayana ba shi da baƙin hali.” Ta yi maganar cikin turo baki. Hajiya ta tab’e baki ta ce. “Toh mai Yaya, zamu gani ai in zai zo, halin Aminun ne ban sani ba, kaɗan daga cikin aikinsa ne ya ƙi zuwa.” Hafsah dai bata kuma cewa komai ba. Neehal ta tsugunna ana musu hotu ita da twins ɗinta. Salma Ƴar ƙawar Mama wadda suka je gidansu Sadik tare tana gefen ta a bakin gado tana latsa waya, kallon status take. Da yake sun yi exchanging number ita da batul da suka je gidan sai ta ga ta yi story just now. Ta shiga da sauri dan ganin pics ɗin Namiji ne, a tunaninta kwalliyar Sadik ta ɗora ta angonci. Rubutun da ta gani akan hoton yasa ta waro Ido, ta kalli hoton tare da maimaita karanta rubutun kan hoton ya fi sau biyar. Da sauri ta taso ta miƙawa Neehal wayar tana faɗin. “Neehal! Duba mun hoton nan ba Sadik ɗinki ba ne?” Neehal ta karɓa cikin tashin hankali, hannunta har rawa yake tun kafin ta ga mene a hoton Sadik ɗin. Kowa na ɗakin ya zuba mata ido. Hajiya ta ce. “Me kuma ya samu Sadik ɗin?” Neehal ta zauna dab’as daga tsugunnen da take idanunwanta duka sun yo waje. A fili ta maimaita rubutun da ta karanta a jikin hoton Sadik. “Innalillahiwa’inna’ilaihirraji’un, Be safe Big brother, Allah ya bayyana mana kai ya kare ka a duk inda kake. Yan’uwa musulmai muna barar addu’arku, yau mun tashi cikin tashin hankalin ɓatan Yayanmu Barrister Abubakar Sadik, wanda wasu alamomi suka tabbatar sace shi aka zo akay har cikin gida. Dan Allah a taya mu da addu’ar Allah ya bayyana mana s…..” Ta yarda wayar ba tare data ƙarasa karanta rubutun ba ta hau girgiza kanta kamar dolowa tana faɗin. “No, no ba Sadik ɗina take managa akai ba, wani mai kama da shi ne. Sadik ba zai taɓa ɓata ranar Auren mu ba.” Sai ta fashe da kuka tare da miƙewa zumbur numfashinta na wani irin fuzga. Da sauri aka yo kanta aka riƙe ta, Haneefah ta zo ta ɗauki wayar ta duba ta ƙara karanta abun da Neehal ta karanta a fili cikin tashin hankali. Hakan ba ƙaramin ƙarawa Neehal tashin hankali da razani ya yi ba tare, lokaci ɗaya ta ji kamar an janye iskar da take shaƙar numfashi da ita, idanunta suka daina ganin komai sai duhu, kawai gani aka yi ta tafi luuu ta faɗi a gurin sumammiya. Yan ɗakin gaba-ɗaya suka yo kanta suna kiran sunanta, twins suka fashe da kuka. Hajiya wadda ita kaɗai ce bata motsa ba sai bin su da ido kawai take cikin tsananin shock, ta miƙe tsaye tare da rafka salati cikin d’imuwa………✍️

By
Zeey Kumurya
⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

6️⃣3️⃣

Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 080662689511314#

………..Mama ta ja baya da sauri tana kallon sa kamar yadda shi ma ya tsaya yana kallon ta cikin wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa. Mama ta sauke ajiyar zuciya gaba-d’aya kwandon bala’in data tanada domin sauke masa idan ya dawo ta nemi shi ta rasa saboda yanayin tsantsar damuwar data gan shi a ciki. Cikin sanyin murya ya ce. “Mum.!” Mama ta haɗe rai ta ce, “Malam bani hanya in wuce, ka zo ka wani tsaya mun a kai.” Ya sauke numfashi mai huci ya ce. “Please Mum I want to talk to you.” Mama ta harare shi ta ce. “Bani da wannan lokacin, bani da lokacin magana da kai Ameen, So ka bani hanya in wuce ana jira na, and i have important something to do now.” Ya kama hannunta tare da marairaicewa ya ce. “Please Mum, na san ni mai lefi ne a gurin ki, amma just 5 minutes ki tsaya ki saurare ni.” Mama ta kalle shi tana sauke ajiyar zuciya, ko ba komai ta ji daɗi data gan shi cikin k’oshin lafiya. Ta zare hannunta daga nashi ta juya ta koma cikin falon, ya yi ɗan murmushi tare da bin baya ta sannan ya ce. “Thank you.” Bayan sun zauna Mama ta fara magana cikin sanyin murya mai nuni da damuwa. “Yanzu Ameen abun da ka yi ka kyauta mana kenan? More especially ma ni da ka san zan damu over, muna cikin wannan halin tashin hankalin amma a nemeka a rasa, sannan ka kashe wayoyinka, bayan ka kunna kuma in an kira ka sai ka ƙi d’agawa.” Ya lumshe ido ya buɗe ya ce. “I’m sorry Mum.”Mama ta ce. “I don’t want your stupid sorry, ka riƙe haqurin ka, abun da nake so kawai just tell me what happened to you? Ina ka shiga through out today? And me yasa kuma ka kashe wayoyinka?” Ya kalli fuskarta ya ce. “Nothing Mum, kuma babu abun da ya faru da ni.” A fusace Mama ta ce. “You are lier Ameen, like every time if I asked you to tell me what is wrong with you. Amma yanzu ma i will not force you to tell me kamar kodayaushe, zan barka tunda haka kake so, just i will pray for you kamar yadda kake buƙata.” Ta miƙe tana sauke numfashi da sauri alamun ranta a matuƙar ɓace yake. Ya miƙe shi ma tare da kamo hannunta cikin tsananin damuwa ya ce. “Bana son na ga kina ɓata ranki a kaina Mum, sai in ji gaba-d’aya na tsani kaina, dan Allah ki koma ki zauna mu yi magana.” Mama ta ce. “I think five minutes Ka ce, kuma ta yi har ma ta wuce.” Ya ce. “Please Mum.” Mama ta sauke numfashi cikin sanyin murya ta ce. “Ameen! Ni mahaifiyarka ce?” Ya ce. “Yes you are.” Ta ce. “To meyasa baka son faɗa mun damuwarka? Ameen barin kashi a ciki ba ya maganin yunwa, ni na san akwai abun da yake damun ka, kuma ba ƙaramin abu ba ne, yanayinka ya tabbatar mun da haka, amma ban san dalilin ka na ƙin sanar mun ba, ni kuma indai zanke ganin ka a haka bazan taɓa iya haquri ba sai na tambaye ka. Ameen da damuwarka zan ji ko da ta Neehal?” Ya zaunar da ita shi ma ya zauna cikin damuwa ya ce. “Mama! wani abun da yake cikin ciki wuta ne, wanda idan ya fito zai cinye mutane da yawa, barin shi a cikin shi ya Alkhairi.” Mama tay masa wani kallo ta ce. “Tunda ka san wutar ne me yasa kai zaka bar shi a cikin cikinka? ya cinye ka kenan?” Ya ce. “Ba zai cinye ni ba Insha Allah, I know.” Mama zata kuma magana ya katse ta da faɗin. “Just pray Mum.” Mama ta jinjina kai cikin raunin murya ta ce. “Shikenan Allah yasa mu dace, Amma Ameen ina jin wani iri a raina something so bad, bana son na rasa ka kai da Neehal a rayuwata, ku kaɗai ne garkuwata a duniyar nan, ku kaɗai nake kallo in ji sanyi a raina bayan mahaifiyata, more especially You!” Ya kwantar da kansa akan ƙafaɗarta bai ce komai ba, sai lumshe idonsa da ya yi. Mama ta shafa lallausar bak’ar sumar kansa ta ce. “Ameen! ka ji ƙaddarar data kuma samun mu ko? ban san me marainiyar Allah nan tay musu suke cutar da ita.” Can ƙasan mak’oshi ya ce. “Akwai Allah!” Mama ta ce. “Da shi muka dogara.” Ya janye kansa daga jikin Mama ya ce. “Where is she?” Mama ta nuna masa ɗakin Daddy da hannu dan ta gane Neehal yake nufi ta ce. “Tana can.” Ya miƙe ba tare ya yi magana ba ya nufi ɗakin. Mama ta bi shi da kallo zuciyarta cike da son sanin abun da yake damun tilon ɗan nata k’waya ɗaya jal a duniya da ya sanyaya shi over haka. Ta miƙe tana sauke ajiyar zuciya ta fice daga falon.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button