NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:46] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

2️⃣7️⃣

Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 08066268951

………..A firgice Umma ta yaye bargon data lullub’a tare da tashi zaune tana kallon bakin ƙofar k’irjinta na dukan tara_tara. Abba kuwa ko kaɗan bai nuna razana ba, kallon mutanen da suke shigo musu ɗakin kawai yake a ransa yana faɗin, “La’ilaha’illa’anta subhanaka’inni’kuntu’minazzlimuun.” Su su biyar ne, suna sanye cikin bak’ak’en kaya, fuskokinsu a ɗaure da wani baƙin k’yalle, hannunsa ɗauke da bindigu. Sosai hantar cikin Umma ta kad’a, addu’ar da take yi a zuci bata san sanda ta fito fili ba. Abba kuwa kallonsu kawai yake amma bece musu komai ba kamar yadda suma ba su ce ba, sai ƙare wa ɗakin kallo kawai suke. Cikin wata irin tafiya ta ƙasaita ɗaya daga cikinsu ya ɗora ƙafarsa ɗaya akan bedside locker ya ɗan sunkuyo da fuskarsa dai-dai inda Abba yake. Cikin wata irin shakakkiyar murya ya ce “Na gaida Jarumi uban Jarumai.” Sannan ya saki wata uwar dariya ya maida dubansa ga Umma ya ce “Ke! ki adana addu’arki zatai miki amfani a gaba dan yanzu baza ta hana mu yin abun da mukai niyya ba.” Umma ta tab’e baki duk da yanayin tsoron da zuciyarta take ciki amma ta dake ta cigaba da karanto addu’arta, domin ta san ita ce kaɗai makaminta a wannan lokacin. Mutumin ya juyo ya yi wa ɗaya daga cikin yaransa inkiya da ido, cikin sauri yaron ya zagaya ta bayan Abba ya ƙarasa kan gado inda Umma take ya damk’o ta, Umma tana cizewa Abba kuma yana faɗin su sakar masa mata cikin tsananin ɓacin rai ganin wani k’aton banza yana taɓa masa mata, ganin Abba ya zabura zai miƙe wani daga cikin yaran ya riƙe shi, tare da ɗora masa bindiga a goshi, Umma ganin haka ta ruɗe ta fara kuka, a kusa da Abba yaron ya cillar da ita, shi kuma wanda ya riƙe Abba ya sake shi tare da koma wa baya. Babban nasu ya ƙara sakin wata kafirar dariya, ya daɗe yana dariyar sannan ya tsagaita ya zira hannunsa a aljihun gaban rigarsa ya ɗauko waya ya latsa ya haska wa su Abba da Umma yana faɗin “Kun san wannan?” A tare Umma da Abba suka kalli juna cikin al’ajabi, Abba ne ya fara ɗauke kallonsa daga kan wayar ya mayar ga mutumin ya ce “Eh na san sa, farin sani ma kuwa.” Mutumin ya yi wani guntun murmushi sannan ya matso da fuskarsa kusa da su Abba sosai ya fara magana ƙasa_ƙasa wanda ni dai zeey ban ji ba. Zuwa can dai na ji Abba cikin d’aga murya wadda ke nuni da tsantsar ɓacin rai ya ce “Ba zan iya wannan haukan da shirmen ba, ƴar tawa guda ɗaya zan yarda in ɓata mata rayuwa in jefa ta a halaka, to bazan yi abun da kuke so ba ku yi duk abunda zaku yi, Allah ya fiku kuma da shi na dogara.” Mutumin ya jinjina kai ya mai da dubansa ga Umma ya ce “Kema kin zaɓi mutuwa akan amincewa da buƙatar mu?” Umma ta saka kuka, cikin kukan ta ce “Ko me zaku mun ba zan taɓa amincewa da buƙatarku ba, kuma ƴarmu ko da bama raye Allah zai kare mana ita daga mugun nufinku, kuma da ku da wanda ya turo kun mun kai ƙarar ku gurin mai duka, shi zai mana maganin ku ya kawo ƙarshen ku da duk wasu irin hali da mummunar d’abi’arku, kuma…….” Ƙarar harbin da ta ji ya katse mata zancenta ta runtse idanta da sauri, kafin ta yi wani yunk’uri ta ƙara jin wani saukar harbin, buɗe idonta ta yi zuciyarta na wani irin bugu tamkar zata faso kirjinta ta fito, wata gigitacciyar ƙara ta saki ganin duk harbin da ta ji a ƙirjin Abba aka yi su, rungume shi ta yi k’am ajikinta tana kiran sunansa cikin fitar hayyaci, amma ko motsi ba ya yi, jini har ya fara ɓata farar jallabiyar dake jikinsa. Janye Abba suka yi da sauri daga jikinta itama suka sakar mata harbin a ƙirji, a take Umma ta bi bayan Abba ta zube a gurin babu alamun numfashi a tattare da ita. kafin kiftawar ido suka fice daga ɗakin a guje suka bi ta inda shigo suka fice daga gidan gaba-d’aya.

Aunty A’isha tana part ɗinta tana bacci ƙarar harbin ne ya tashe ta, amma ko kaɗan ba ta yi tunanin a cikin gidan ba ne, ta yi tunanin wani gidan custom ne da suke mak’ota b’arayi suka shigar masa. Amma duk da haka sai da ta ji gabanta ya faɗi a lokacin da akai harbin ƙarshe, wayarta ta ɗauka ta kira Numbern Abba amma bai ɗauka ba, jin shiru kusan minti talatin da yin harbin Ba’a kuma ba ta sauke ajiyar zuciya ta koma ta kwanta, amma sai ta nemi bacci a idonta ta rasa, haka kawai ta ji jikinta wani iri, zuciyarta har wani rawa take dan fargaba. Ƙara kiran wayar Abba ta yi amma bai d’aga ba, hakan yasa ta kira Umma itama ba ta ɗauka ba, gashi Uncle Usman ba ya nan ya yi tafiya balle ta kira shi, dan ita ta rasa mai yasa hankalinta ya kasa kwanciya da harbukan da akai. Ranar Aunty A’isha bata iya bacci ba, ga wani irin tsoro da ya rufe ta, wadda ko kwakwkwaran motsi tsoron yi take. Sai da aka shiga Sallar Asuba sannan ta iya tashi ta shiga toilet ta ɗauro alwala ta fito ta tada Sallah, tana idarwa kuwa ta yi part ɗin Umma. Da Sallama ta shiga falon Umma amma ta ji shiru, corridor ta nufa inda ɗakunan Umma guda biyu suke suna facing juna, tun daga bakin ƙofar ta fara hango jini ta ƙasan ƙofar, wani mummunar fad’uwa gabanta ya yi, da gudu ta tura ƙofar ɗakin ta shiga, wata gigitacciyar ƙara ta k’walla ganin Umma da Abba kwance cikin jini, kamar kuma wacce aka tsikara ta fito da gudu ta yi waje tana k’wala wa mai_gadi kira, mai gadi da dawowarsa kenan daga masallaci ya fito da sauri yana tambayar “lafiya Hajiya?” Part ɗin Umma kawai Aunty A’isha take nuna masa amma ta kasa mgn, hakan yasa ya nufi part ɗin da sauri a zatonsa ko wuta ce ta kama a ciki. Gigitar da mai_gadi ya shiga baza ta faɗu ba, ga mamakin ta ya ya aka iya shigowa gidan har aka aiwatar da wannan mummunan aikin, dan shi ko da za shi masallaci ma ƙofar gidan a rufe take shi ya bude ta da hannunsa, kuma gidan baza a iya haurowa ba saboda tsayin katangar gidan. Kuka sosai Aunty A’isha ta shiga yi lokacin da mai_gadi ya sanar mata babu numfashi a tattare da su Umma, tana faɗin “Su waye suka kashe ku? Me kukai musu?” Mai_,gadi kuwa da sauri ya fita ya faɗa wa mak’ota, nan da nan kuwa mazan layin suka fara shiga gidan cikin tashin hankali, dan kuwa duk yawanci sun ji harbin da akai, babu ɓata lokaci custom ɗin dake layin ya kira Police aka sanar musu, kafin gari ya yi haske har sun zo gidan. Aunty A’isha kuwa tuni ta suma, wata makociyarsu ce da ta shigo ta ɗauki ƙaramar wayar Umma ta shiga kiran ƴan’uwanta tana sanar musu, haka ma wayar Abba mai_gadi ne ya ɗauka ya kira ƴan’uwa da abokan arziki yana sanar musu. Aunty A’isha bayan an shafa mata ruwa ta farfaɗo itama tana kuka ta shiga kiran mutane tana sanar musu wannan mummunan labarin wanda take ganin tamkar al’amara ko kuma mafarki take zata farka. Mutuwar su Abba ta girgiza zuk’atan mutane, kafin ka ce me, labari ya fara baza gari, musamman da matasan unguwar suka yaɗa a social media.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button