NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Shi kuwa Ameen yana shiga ɗakin ya cire rigar jikinsa ya cillar akan gado sannan ya ɗauki remote ya karo AC, dan ji yake gaba-d’aya jikinsa da zuciyna yi masa wani irin zafi suke masa, kwanciya ya yi rigingine ya lumshe idonsa tare da dafa kansa da yake yi masa ciwo saboda hayaniyar su Hafsat. Kalamanta dana Aunty Safiyya ne suke yi masa kuwwa a cikin kunne, Hafsat har ta yi tsaurin idon da zata ce masa idan ya cika ɗan Halak ta kira sunan iyayensa na ainihi ta ce ya sake ta? ita kuma k’anwar uwarta mai kama da Ngozi ta cewa Mama munafuka! Lallai zai shayar da su ruwan mamaki, wannan shine karo na uku da Hafsah ta yi masa Manyan laifuka a rayuwar Auransu. Kiran Sallar Magriba ne ya tashe shi dan dole ya yi alwala ya fita. Sai da ya kalli ɗakin Neehal sannan ya fice, a ransa yana addu’ar Allah yasa bata yi kuka ba. Ita tana can ma bacci ya ɗauke ta. Sai bayan isha’i ya dawo gidan, lokacin zuciyarsa ta fara sanyi sakamakon Sallah da zikirin da ya yi. Ya buɗe fridge ɗin parlour ya d’auko ruwa mai sanyi ya sha, ajiyar zuciya ya sauke ya nufi ɗakin Neehal. Lokacin bata jima da tashi daga bacci ba, ta shiga toilet ta fito kenan tana zaune a bakin gado tana latsa wayarta. Ya tura ƙofa ya shigo tare yin sallama, ba tare data kalle shi ba ta amsa masa. Ya tsaya a jikin ƙofa yana kallon ta, ta ɗan ɗago ta kalle shi ta tura masa baki sannan ta mayar da idonta kan wayarta. Ya yi murmushi sannan ya ƙaraso ya tsugunna a gabanta, hannayensa duka biyu ya ɗora akan cinyarta, yana kallon fuskarta ya ce. “Baby yau babu magana.” Ta ja numfashi duk wani haushin sa da take ji yana barin zuciyarta, ajiye wayar ta yi ta ɗora hannunta akan lallausar sumar kansa ta shiga shafawa bata ce komai ba. Ya kwantar da kansa akan cinyarta tare da saka hannunsa ya zagaye k’ugunta yana shaƙar daddaɗan ƙamshinta. Duk wani ɓacin rai da su Hafsat suka saka masa yana kallon kyakkyawar fuskarta ya ji ya gushe, yanzu kuma da kansa ke jikinta sai ya manta da shi ma gaba-d’aya. Ta ture kan nasa ta ce. “Bani da lafiya fa.” Da sauri ya ɗago kansa ya ce. “Subhanallahi, da gaske baby baki da lafiya? mene ne yake damunki?” Ganin yanda ya yi maganar a rud’e sai ta ƙara narkewa ta ce. “Ciwon ciki na yi, kuma ka dawo ina maka magana ka ƙi kula ni.” Ya tashi ya hau kan gadon ya janyo ta jikinsa cikin damuwa ya ce. “I’m sorry My love, raina a b’ace yake time ɗin ne, bana son na zauna kusa da nake kar na yi miki tsawa ko abun da baza ki ji daɗi ba akan laifin da ba ke kika mun ba.” Ya kai hannu kan cikinta ya ce. “Yanzu ya jikin naki? Allah yasa dai baki sha wahala ba irin wadda kike sa?” Ta bar jikinsa ta koma ta kwanta akan gadon ta ce. “Sosai ma, kamar zan mutu.” Dafe kansa ya yi ya ce. “Ya Salam! Sannu Baby, ko za mu je asibiti ne?” Ta ce. “Ya daina ai yanzu.” Ya bi ta ya kwanta shi ma cikin jimami da damuwa yana ta jera mata sannu da riri tata, ita kuma tana zuba masa taɓara. Daga baya kuma sai ta saka masa dariya. Ya tsaya yana kallon ta ya ce. “What’s funny?” Tana shafa sajen fuskarsa ta ce. “Wasa fa nake maka ban wani sha wahala ba.” Ya sauke ajiyar zuciya tare jan karan hancinta ya ce. “Shine da zaki ɗaga mun hankali ko?” Ta ce “To ka yi haquri bazan kuma ba.” Ya saka idanunsa a cikin nata ya ce. “Wai ciwon cikin ma na mene ne?” Ta yi murmurshin mugunta ta ce. “Kamar ya?” Ya ce. “Kin fini sani ai.” Ta rufe fuskarta da hannunta tana dariya. Ya ɓata fuska ya ce. “Me yasa abun nan zai mun haka?” Juya masa baya ta yi cikin jin kunya. Ya juyo da ita da hannunsa ya kai hannun ya danna mata ciki. Ta kwabe fuska ta ce. “Ouch! Da zafi fa.” Ya rungume ta ya ce. “Sorry, dannawa na yi dan ya yi ya zube da wuri.” Ta yi murmushi ta ce. “In ka yi haquri ma is just 12 days ne zai tafi.” Ya waro ido ya ce. “Ko 120 days ba, I already knew the days, is just 2 to 3.” Ta ɓata fuska ta ce. “Dama saka mun ido kake yi?” Ya ce. “No, the way da kike acting ne ake ganewa, baki da aiki sai kwanciya kamar ruwa, ga taɓara da raki.” Ta juya masa ido ta ce. “Yanzu na daina to.” Bai kuma magana sai langwab’e kai da ya yi yana kallon ta. Ta san me yasa ya yi hakan, gwalo ta yi masa tana dariya ƙasa_ƙasa. Ya zira hannunsa a cikin rigarta ya ce. “Idan babu can ai da akwai nan.” Ta zaro hannun nasa ta yi kalar tausayi ta ce. “Mu je mu ci abinci yunwa nake ji.” Yana bin ta da wani irin kallo da idanunsa da suka fara sauya kala ya ce. “No let me take this first.” Zata yi magana ya hana ta, ta hanyar haɗe bakunansu guri guda. Ta lumshe idonta a hankali tare da saka hannayenta duka a kansa tana shafa gashin kansa zuwa bayan wuyansa……..

Washegari da yamma Ameen ya je gidan Mama, bai b’oye musu komai ba ita da Daddy na daga cin mutuncin da su Hafsat suka yi masa ba. Cikin tsananin mamaki Mama ta ce. “Yanzu Ameen Hafsan ce ta faɗa maka haka?” Ya gyaɗa mata kai zuciyarsa na yi masa k’una. Daddy ya ce. “To ai ni Mahaifinta ya kira ki ɗazu da safe, ya ce mun jiya_jiya ya dawo daga ƙasar ya tarar da wannan abun mara daɗin ji, amma a yanda muka yi magana da shi gaskiya ga dukkan alamu ba shi da masaniyar wannan cin mutuncin da suka yi.” Mama ta ce. “Allah ya kyauta.” Sannan ta dubi Ameen cikin lallami ta ce. “Ka yi haquri, Ni na tursasaka ka je, ban taɓa tunanin za’a yi haka ba.” Ya ce. “Babu komai Mum kansu suka yiwa ai.” Daddy ya ce. “Ban da abunku na mata mutumin da ya zo sulhu gurinku me ne na tsayawa na neman fitina da shi kuma?” Mama ta ce. “Shaid’an ne kawai, ka yi haquri Ameen tunda bata taɓa yi maka makamancin wannan laifin ba, karka yanke hukunci da baza mu ji daɗi ba dukanmu.” Ya furzar da iska daga bakinsa ya ce. “Ta taɓa mun Mum, lokacin data yi barin ciki abortion ta yi ba miscarriage ba, and kuma suka je ita da k’anwar mahaifiyarta aka juya mata mahaifa wai ita bata shirya haihuwa yanzu ba.” A tare Mama da Daddy suka kama salati cikin tsananin kad’uwa. Mama ta ce. “Ikon Allah, ko na ce shirme, wani yana nema wani yana gudu, shi Ubangiji ai ba’a yi masa wayo, Allah yasa mu dace.” Haka suka cigaba da tattauna maganar Mama sai tausar Ameen take, ita bata son ya ce zai rabu da Hafsat. Dan yanda take hango zallar ɓacin rai a cikin idanunsa ta san zai iya aikata komai. Shi kuma Ameen wani irin d’aci yake ji a cikin zuciyarsa, ji yake tamkar a yanzu ne Hafsat ta b’arar masa da gudan jininsa. A lokacin ji ya yi kamar ya sake ta saboda tsabar baƙin ciki, amma ya taushi zuciyarsa ya haqura. By now kuma ta kai shi bango, dan haka dole ya yi mata abun da zai saka ta dawo cikin nutsuwarta da hankalinta, ta gane ba tsoronta yake ji ba kawaici ne kawai irin nasa yake yi mata. Daga gidan Mama gidansu ya wuce direct, ya tsaya a bakin gate daga waje ya ɗauko Joter da Pen ya rubuta abun da zuciyarsa ta bashi umarni. Bayan ya gama ya karanta sannan ya ninke takardar, horn ya danna mai gadi ya buɗe ƙaramar ƙofar gidan ya lek’o dan ganin waye, Ameen ya fita daga cikin Motar ya ƙarasa ya bashi papern ya ce ya bawa Hafsat sannan ya juya ya shige cikin Motarsa ya bata wuta ya bar layin, ya bar mai gadi da bin sa da kallo riƙe da takarda a hannu baki a sake……….✍️

By
Zeey Kumurya
⚡NEEHAL⚡

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button