NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

A part ɗin Mama kuwa, ba jimawa da fitar Neehal Mama ta miƙe ta shiga ɗakinta, a lokacin ne kuma kiran Ahmad ya shigo wayar Neehal dake hannun su Afrah. Suka dinga shafa wayar har Allah ya ba su sa’a su kay pick ba tare da sun sani ba. Amrah ta ƙara danna wayar a ƙoƙarin ta na ganin sun koma game ɗin da suke, ashe gurin speaker ta danna. Jin muryar Mahaifinsu yana sallama suka ruɗe da murna. “Daddy! Daddy! Daddy!” Kowacce na son ya yi magana da ita. Ya ce “Oh, sweethearts zaku kashewa Daddy kunne fa.” Afrah ta ce “Daddy Aunty ta ce ka tafi ka bar mu.” Ya ce “Ai zan dawo in ɗauke ku soon, ko baku san zama a gurin Aunty.” Suka ce “Muna so.” Ya ce “Yawwa yaran kirki, ina Aunty? Ko bacci take?” Amrah ta ce “Ta fita gurin Uncle Sadik.” A kwance yake amma bai san sanda ya tashi zaune ba. A fili ya ce “What? who is he?” Ya yi maganar a gigice. Afrah ta ce “Daddy yana zuwa gida gurin Aunty, yana da kirki yana ba mu chocolates.” Amrah ta karɓe zancen da faɗin “Shi ya kai mu gidan Aunty Haneefah da ana bikinta.” Ahmad ya had’iye wani abu da ya tsaya masa a mak’oshi, da ƙyar ya iya cewa “Unguwa suka je?” Afrah ta ce “No, Mama ta ce suna waje a zaune.” Ya cize lip ɗinsa da ƙarfi, tare da faɗin “Damm it.” Yaran suka ce “Hello Daddy.” Ya sauke numfashi ya ce “Bye Dear, I will call later.” Ya kashe wayar ya cillar akan gado. Kansa ya dafe da hannunsa yana zancen zuci. Me yasa tun farko bai yi tunanin Neehal tana da wani saurayin ba? a age ɗinta dama dole a ce tana da samari ba ma saurayi ɗaya ba. Hankalin Ahmad fa in ya yi dubu ya tashi, ya maimaita sunan Sadik a cikin ransa ba a dadi, kamar mai neman wani abu a cikin sunan. Ji yake kamar ya yi tsintsuwa ya gan shi a Kano, ya ga wane Sadik ɗin nan da his future wife take kulawa. “Kenan tana son shi?” Ya faɗi haka a fili cikin tsananin damuwa. ‘Tana son shi mana tunda har take kula shi.’ Zuciyarsa ta ba shi amsa da haka. “Ya Allah!” Ya furta haka a fili wani irin kishi na nuk’urk’usar zuciyarsa.

Sai wajen 9 Sadik ya tafi, bayan ya gama wanke mata zuciyarta tass, ya kuma roƙe ta kar ta sanar da Mama abun da ya tambaye ta, bare itama hankalinta ya tashi. Tay masa alƙawarin ba zata faɗa mata ba. A bakin part ɗin Mama tana ƙoƙarin danna door beil, ta ji k’amshin Ameen ya cika mata hanci, ta juya bayanta da sauri suka yi 4 eyes da shi………✍️

NOTE: For just of you that are thinking Ameen zai yiwa Ahmad wani abu na rashin mutunci or something else, har da masu tunanin duka.???????? Let me tell you something, Namijin duniya baya hukunci da faɗa ko wani hargagi, da ido ma kaɗai ya isa ya hukunta mutum, ato, Mama bata haifi sakaran Namiji ba, Jarumi ta haifa mai dakakkiyar zuciya. Har na hango su oo suna washe baki na yabi gwaninsu, to ba Ameen na kare ba, dan Mama na yi.????

By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:56] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

5️⃣4️⃣

Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 080662689511314#

………..Gaba-ɗaya sai ta duburburce ta rasa ina zata saka ranta saboda tsoro da kunya. Ya ƙaraso ba tare da ya ce komai ba ya buɗe ƙofar da key ɗin part ɗin dake gurinsa ya shige. Ta turo baki tare da bin bayansa, a ranta tana faɗin. ‘Ya bar gidan ma amma har yanzu yana tare da key ɗin part ɗinsu.’ Ya tsaya bayan ya shiga falon yana kallon ta, ta sunkuyar da kanta ta ce “Ina yini?” Ya ce “Lafiya, Ya jikin?” Ta ce “Da sauƙi.” Ya ce “Allah ya ƙara sauƙi.” Bai jira amsar ta ba ya nufi upstairs. Ta d’ago kanta tare da sauke ajiyar zuciya ta bi bayan shi zuwa saman. Babu kowa a falon hakan yasa ta nufi bedroom ɗinta, a nan ta tarar da su Afrah kwance akan gado suna bacci. Ta ajiye mayafin jininta tare da kwanciya ta lumshe idonta ta faɗa duniyar tunani. Ameen kuwa ɗakin Mama ya shiga, bayan sun gaisa ta ce “Neehal ta ce mun ka zo da safe ina gurin aiki.” Ya ce “Eh.” Ta ce “Ya jikin Hafsan?” Ya ce “Ta ji sauqi.” Mama ta ce “Allah ya ƙara sauƙi.” Ya miƙe ya ce “Ameen, bari na je gurin Dad.” Mama ta ce “Okay.” Bayan fitar sa Mama ta ɗauki wayar Neehal data karɓa a hannun su Afrah ta nufi ɗakinta, dan dubawa ko ta dawo.” Turo ƙofar ɗakin da Mama ta yi yasa ta buɗe ido, Mama ta ce “Har kin dawo kin kwanta kenan?” Ta ce “Ban jima da dawowa ba.” Mama tana mata kallon tsaf ta ce “Are you Okay?” Ta ɗan yamutsa fuska ta ce “Kaina ke mun ciwo.” Mama ta ce “Allah ya sauqaqe sai ki tashi ki ci abinci ki sha magani.” Ta ce “Toh.” Tare da karɓar wayarta da Mama ke miƙo mata.” Mama ta ce “Sai kiran ki ake, waye yake miki wannan kiran ne haka?” Tana latsa wayar ta ce “Uncle Ahmad ne, yaransa yake son magana da su.” Mama ta ce “Sai ki kira shi ki sanar masa sun yi bacci.” Ta gyaɗa mata kai, amma bata jin zata iya kiran nasa. Mama ta juya ta fita bayan ta ƙara jajjada mata ta fa tashi ta ci abinci ta sha magani. Ta fi awa bayan fitar Mama tana sak’awa da kuncewa sannan ta miƙe ta fito ta sauka ƙasa. Abinci ta ɗebo ta ci, sannan ta dawo ta sha magani. Har time ɗin bata kira Ahmad ba, shi ma bai ƙara kiran ta ba. Ta shiga toilet tay wanka ta fito ta shirya cikin kayan bacci masu taushi ta kwanta, text kawai ta yiwa Sadik ta yi addu’a ta tofa wa su Afrah sannan ta shafa a jikinta, ba jimawa bacci ya ɗauke ta.

Bayan kwana biyu ranar Juma’a da safe ta samu Mama a ɗakinta ta ce mata. “Mama Ya Sadik ya matsa wai sai na je gidansu na gaishe da Maamah.” Mama ta ce “To ki shirya anjima ki je mana.” Ta ce “Ni dai Mama kunya nake ji, kuma ba zan iya zuwa ni kaɗai ba.” Mama ta ce “Maganin rashin zumuncin ki kenan, da kina zuwa ki kaiwa Freind’s ɗinki ziyara da yanzu sai ki kira wata ta raka ki ku je.” Ta ce “Bari in kira zee ta B.U.K.” Mama ta ce “Tunda baki da kunya ba, yarinyar nan haka tay ta zuwa gidan nan amma saboda ba kya zuwar mata itama ta gaji ta daina zuwa, yanzu kuma sai ki kira ta ki ce ta zo ta raka ki ko? Tunda zaman ki take.” Ta marairaice fuska ta ce “Allah sarki, Haneefah tah, ga ranarta ta zo.” Mama ta ce “Bari na kira Hajiya Rabi, idan Salma tana free yau sai ta zo anjima ku je.” Neehal ta yi murmushin jin daɗi ta ce “Yawwa Mamana.” Mama ta ɗauko Wayarta ta kira Hajiya Rabi wadda ta kasance ƙawarta ce, Salma kuma ƴarta ce baza ta fi mate ɗin Neehal ba. Bayan sun gaisa Mama ta roƙe ta alfarmar zuwan Salman idan babu abun da take. Hajiya Rabi ta ce, zata zo insha Allah bayan an sauko daga masallaci. Mama tay mata godiya su kay sallama. Ta dubi Neehal ta ce “Sai ki kira shi ki sanar masa ya zo da yamma ya kai ku.” Ta ce “Toh Mama, amma duk da haka ina jin kunya in na je me zance?” Mama ta ce “To ai ba zama zaku yi ba, gaishe su kawai zaki ku dawo.” Ta ce “Tom, bari na je na kira shi.” A safiyar Ahmad ya kira wayarta, ta d’aga ta saka a speaker sannan ta bawa su Afrah. Tun ranar Larabar nan da ya tafi ba su kuma magana ba, idan ya kira sai dai ta bawa ƴaƴansa, shima kuma ba ya cewa su bata wayar, ko zancen ta ba ya musu, sai dai su in sun masa maganarta yana biye musu. Ta yi shiru tana sauraren voice ɗinsa a cikin wayar, yana magana da ƴaƴansa cikin nishad’i. Sai ta ji ba daɗi sosai a ranta, na ƙin kulatan da yake kwana biyu, ta turo baki kamar yana ganin ta, jin yana cewa su Afrah ranar Sunday zai zo ya ɗauke su. Afrah ta kalle ta, ta ce “Aunty Daddy ya ce zai zo ya ɗauke mu ranar Sunday.” Ba ta ce komai ba, sai lumshe idonta da ta yi. Ahmad ya ɗan lumshe idonsa cikin tsananin kewarta, ambatar sunan ta da Afrah ta yi kawai yasa ya ji ba zai iya jurewa ba sai ya ji muryarta a yanzu. A hankali ya ce “Ina Aunty?” Amrah ta ce “Gata nan, a kwance.” Ya ce “Ku bata wayar.” Suka matso jikinta suna kiran sunan ta, “Aunty, Daddy ya ce ki karb’i wayar.” Tana jin su tay musu shiru, ta kuma ƙi buɗe idonta. Amrah ta ce masa. “Daddy ta yi bacci.” Ya san ba baccin take ba, kawai wayar ce baza ta karɓa ba. Sai yay wa yaran sallama ya katse wayar ya tura mata text. Sai bayan sun gama surutunsu sun fita falo sannan ta tashi ta ɗauki wayar, a lokacin ta ga text da Numbern sa. Cikin sauri ta shiga karanta abun da ya turo. Princess, ya jikin naki, da fatan kin samu lafiya. I MISSED YOU ALOT. Ta ji wani murmushi ya subce mata, ko ba komai ya nuna care a kanta, duk da bata san me yasa 2 days ya daina kula ta ba, ita kuma tsananin kunyarsa ce tasa in ya kira take kasa pick. Tay masa reply da, Ina lafiya Uncle, dafatan kai ma haka? Ta rungume wayar a ƙirjinta zuciyarta na azalzalarta akan ta kira shi, ta ji muryarsa. Duk da ta ji yanzu da suna waya da su Afrah, amma ta yi missed ɗin yanda yake mata magana da ita a cikin kunnenta cikin salo mai narkar da zuciya, tana ta tunanin nasa bata san bacci ya ɗauke ta ba. Sai ƙarfe ɗaya saura Mama ta tashe ta. “Ki tashi, ki shirya ki shirya su Amrah, ko kin manta zaku fita ne?” Ta tashi zaune cikin muryar bacci ta ce “Ban ma san sanda baccin ya ɗauke ni ba.” Mama ta ce “Sai ki tashi yanzu, kafin Salma ta ƙaraso, gidan A’isha zaku fara zuwa sai ya je ya ɗauke ku a can.” Tana sakkowa daga kan gadon ta ce “Toh.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button