NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

A Parlour’n Mama suka zauna gaba-ɗayan su, sai a lokacin Neehal ta lura kamar duk suna cikin ɓacin rai. Daddy ya sauke wani gwauron numfashi yana duban Neehal cike da tausayawa. dan shi ma Abba ya faɗa masa komai akan fasa Auren ta da Sadik. Mama ta janyo ta jikinta cikin damuwa ta ce. “Ya kika ga jikin Sadik ɗin?” A hankali ta ce. “Lafiyar sa k’alau.” Mama ta sauke numfashi ta ce. “Ki yi haquri Neehal da rayuwa a duk yanda ta zo miki, duk abun da kika ga kin rasa ba Alkhairi ba ne a gare ki, idan kika yi haquri da tawakkali sai ki ga Ubangiji ya sauya miki da wanda ya fi wanda kika rasa ɗin, komai lokaci ne da shi kuma komai mai wucewa ne, na daɗi ko na wahala. Neehal iyayen Sadik sun ce ba zai aure ki ba.” Ai Neehal ji ta yi kamar Mama ta soka mata mashi a ƙirjinta, ta runtse idanta a ƙoƙarin ta na ganin hawaye sun zubo mata kamar kodayaushe idan tana cikin damuwa ko zata ji abun da ya tokare mata ƙirji ya yi ƙasa, amma sai hawayen suka ƙi zuwa wannan karon. Ta buɗe idonta tare yin murmushi mai ciwo wanda ya matuƙar bawa su Mama mamaki ta ce. “Shikenan Mama, Allah yasa haka shi Alkhairi, dama na san haka zata iya faruwa.” Bata jira amsa ba ta miƙe dak’yar ta nufi upstairs, ko ganin gaban ta bata yi sosai saboda tsananin damuwa. Suka bi ta da kallo gaba-d’ayan su cike da tsantsar tausayawa Aunty A’isha har da k’walla. Hajiya ta fashe da kuka ta ce. “Gaskiya duk mai aikatawa yarinyar nan wannan abun Allah ka wulaqanta rayuwarsa ta duniya da lahira, Allah ka saukar masa bala’in da ya fi ƙarfin sa.” Mama ta lumshe idonta wani tunani na d’arsuwa a cikin ranta wanda take ganin Insha Allahu shine ƙarshen matsalar Neehal. Aunty Sadiya ta ce. “Komai ya kusa zuwa ƙarshe da yardar Allah.” Aunty A’isha ta ce. “Allah yasa.” Suka cigaba da jimanta al’amarin, suna jinjina wulaqanci irin na Hajiyarsu Sadik. Aunty A’isha ta ce. “Ni ban ji daɗin maganganun da kika faɗa mata ba Sadiya, tunda babbar mace ce ta haife ki.” Aunty Sadiya ta ce. “Ai bata da wani girma sai na jikinta, dan abun da ta yi halin ƙananun mutane ne.” Hajiya ta ce. “Gwara da kikai mata hakan ai, da za ji zancen Shari’ah ai shiru ta yi ta kama kukan munafurci, yanzu sai a tattara musu kayansu da kuɗaɗen su a mayar musu.” Daddy ya ce. “Insha Allahu gobe zan kira Alh. Musa da su Usman sai su zo mu mayar musu.” Suka amsa da Allah ya kai mu. Su Aunty’s ba su wani jima a gidan ba suka tafi, saboda yanda zuciyoyinsu gaba-d’aya babu daɗi, Hajiya ma ta ce gobe zata wuce Gombe.

Dak’yar Neehal ta iya ƙarasawa ɗakinta saboda juyawar da kanta yake mata. Ta faɗa kan gado tana maimaita Innalillahiwa’inna’ilaihirraji’un cikin sark’ewar harshe. Jikinta gaba-ɗaya rawa yake kamar yadda take jin zuciyarta na bugawa da ƙarfi, ba rabuwa da Sadik ne yafi damun ta ba, Baƙin tabon da aka yiwa rayuwarta ne ya fi komai damun ta, ta san shikenan an fara kenan, duk wanda ya ƙara fitowa da niyyar Aurenta mutanen gari zasu hana shi ko kuma idan ya ƙi jin maganar mutane iyayensa wanda ya zama dole yay musu biyayya su hana shi, shikenan kuma wataƙila ita da Aure sai a lahira. Ta tuno gawar Jameel data gani lokacin da za’a kai shi makwancinsa na gaskiya, sannan ta tuno Anwar ma, ta tuno Ahmad ranar da suka rabu a soyayya sannan ta tuno moment ɗinsu da Sadik na d’azu, ta tuna yanda yake kallon ta da yanda ta ga jikinsa a sanyaye da damuwar data hango ƙarara akan fuskarsa, ashe duk na rabuwa da ita ne, hirar ƙarshe suka yi, kallon ƙarshe yake mata ashe. Sai a lokacin ta ji wasu hawaye masu d’umi suna bin kuncinta, wanda take jin kamar a zuciyarta suke sauka suna ƙara mata zafin da take ji a cikin zuciyarta_ta. Ta daɗe a cikin wannan halin mai wuyar fassaruwa, wanda ta kasa bambance a sume take ko a normal rayuwa saboda tsananin damuwa. Bata san mintunan data ɗauka ba ko awanni ba sai ji ta yi Mama tana mata magana. Ta d’ago kanta da yay mata nauyi ta dubi Maman, Mama ta taɓa jikinta ta ji ya yi zafi. Ta shafa fuskarta ta ce. “Ki tashi ki yi Sallah, ko baza ki iya ba?” Ta yunƙura ta tashi zaune dak’yar, a zaunen ma sai ta ji kamar jiri yana ɗibar ta, amma saboda kar tayar da hankalin Mama ta ce. “Zan iya.” Mama ta ce. “Sannu kin ji, ki yi Sallar sai ki ci abinci ki sha magani, ki yi ta maimaita sunan Allah da Hasbunallahu’wani’imal’wakil, Insha Allahu zaki ji sauƙin zafin zuciyarki.” Ta gyaɗa mata kai kawai. Mama ta bi ta da kallon tausayawa sannan ta tashi ta fice. Bayan ta yi Sallar a zaune Mama ta kawo mata abinci, favourite ɗinta Mama ta yi hoping zata iya ci, amma lauma ɗaya ta yi ta ji abincin ya kasa wucewa ta mak’oshinta, sai ta ji kamar ƙasa ta watsa a bakin nata, ba shiri ta furzar da abincin. Sai tea Mama ta haɗa mata ta sha shi ma da ƙyar ta iya shan kaɗan. Mama tay mata allura ta kwanta ta samu bacci ya ɗauke ta. Tana cikin baccin ta ji muryar Haneefah a kanta. Ta buɗe ido sai ta gan ta zaune a gefen ta. Haneefah ta ce. “Yau kuma bacci ake, na ɗauka zan zo in tarar kuna hira da Habibin naki.” Neehal ta tashi zaune bata ce mata komai ba ta sauka ta shiga toilet saboda fitsarin data ji ya ɗaure mata mara. Bayan ta fito ta cewa Haneefah. “Yaushe kika zo?” Haneefah ta ce. “Na kai 30 minutes, na gaji da jiran ki har sai kin tashi da kanki shi yasa na tashe ki.” Neehal ta ce. “Kin kyauta ai, gashi nan kin ja mun ciwon kai.” Haneefah ta ce. “Sharri kayan k’walba.” Sai kuma ta yi murmushi ta ce. “Ashe an ga Ya Sadik, dan iskanci shine baki kira ni kin faɗa mun ba.” Neehal ta ce. “Sorry ƙawata, wallahi babu wanda na faɗawa, farinciki ya mantar da ni.” Haneefah ta ce. “Sai fa Mommy ce da muka yi waya d’azu take mun zancen, ta ɗauka ma na sani. Na ce mata ban sani ba wallahi, ta ce mun Mama ce ta kira ta, ta faɗa mata.” Neehal ta ce. “Ya dawo, cikin k’oshin lafiya ma.” Haneefah ta ce. “Masha Allah, haka muke fata dama, yanzu sai k’unci da damuwa su ƙare Tunda Ango ya dawo.” Haneefah ta ƙarashe zancen cikin sigar tsokana. Neehal ta yi murmushi mai ciwo ta ce. “Mu fara yin Sallah Haneefah, na ji an shiga a masallaci sai in baki labari.” Haneefah ta ce. “Toh.”

Duk yanda Neehal take tunanin Haneefah zata ruɗe idan ta ji an fasa Auren su da Sadik sai ta ruɗe fiye da haka, ta miƙe tsaye kamar wata zautacciya tana ambaton Innalillahiwa’inna’ilaihirraji’un, Idanunta a waje. Neehal ta kama hannunta ta zaunar da ita ta ce. “Karki tada hankalin ki Haneefah nina barwa Allah komai, domin shi yake tsara mun rayuwa kuma ya fi ni sanin dai-dai a cikin ta, ki taya ni da addu’a Allah ya ba ni ikon cinye wannan jarabawar tawa.” Ta ƙarashe maganar cikin matuƙar raunin murya. Haneefah ta girgiza kanta idanunta fal da hawaye ta ce. “Abun ya yi yawa Neehal, daga wannan sai wannan, amma ba komai, komai na Allah ne kuma aure lokaci ne da shi idan lokacin yinki ya yi dole ki yi, babu wani mahaluƙi da ya isa ya hana yiyuwar sa.” Neehal ta ce. “Hmmm, Haneefah ni ƴar jarida ce cikakkiya, a kullum cikin jin labarin halin da duniya take ciki nake, haka kuma ina jin labarin ƙaddarar mutane da dama, kowa da irin tasa, wasu matsalar talauci, wasu ciwo, wasu matsalar gidan aure ga suna nan dai matsalolin da yawa barkatai. Amma ban taɓa jin irin nawa ba, Ni kam Haneefah na fitar da rai da Aure har abada, zan cigaba da rayuwata ni kaɗai, in dage da bautawa Ubangiji nah domin samun rabauta a k’iyama. Amma Haneefah na gaji da wannan tashin hankalin, ƴan’uwa da abokan arziki kowa babu kwanciyar hankali. Ki kalli Mama fa, matar da ba ita ta haife ni ba, amma na tabbata damuwata ta kusa saka mata wani ciwon, haka ma Daddy jibi yadda gaba-d’aya ya rame duk saboda ni, ga su Aunty su ma cikin damuwa suke saboda ni, ga ki kema da sauran mutane. A kwanakin nan sai na ji gaba-ɗaya na tsani kaina da rayuwata, amma da nai wani tunani d’azu sai na yi istigfari, na tuna Ubangiji ya bar ni cikin k’oshin lafiya, ga wasu can kwance a gadon asibiti cikin jinya, wanda da zasu ganni na san zasu ce ina ma sune ni yanda nake da lafiyar nan. Rayuwa cike take da k’alubale kala-kala, kuma kowa da irin tasa ƙaddarar, ni kam na karb’i tawa hannu bibbiyu, yanzu addu’a kawai nake Allah ya cire mun son Sadik da tunanin sa daga cikin raina, na san hakan zai rage mun damuwar da nake ciki.” Haneefah ta ja gwauron numfashi ta zare hannunta daga cikin na Neehal ta ɗora su akan ƙafarta, cikin confidence ta ce. “Insha Allahu Neehal zaki yi aure da mijin kere sa’a nan ba da jimawa ba, duk wannan k’uncin da kike ciki zai wuce ya zamto tamkar firlm a gare ki.” Neehal ta lumshe ido tana jin kamar abun da Haneefah ta faɗa ba zai taɓa tabbata a gare ta ba………..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button