NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Mama sai kallon su take cike da tausayawa, haka ma Musbahu da bakinsa ya kasa rufuwa dan murna. Ahmad ya manta da kowa da yake gurin yaransa kawai yake biyewa suna hirarsu, wani irin wasai yake jin zuciyarsa ta masa, gaba-ɗaya damuwar dake cikinta ta gushe sai wani sanyi ne yake ratsata. Su Afrah sai labarin new Aunty’nsu (Neehal) suke bashi da kuma school ɗin da suke zuwa. Tun kafin ya ga Antin tasu ya ji yana k’aunarta saboda kulawar da ta yi da sanyin idaniyarsa, ya fara tunanin mai zai mata a duniyar nan wanda zai faranta mata a matsayin tukuici. Lokaci ɗaya ya koma ainihin Ahmad ɗinsa mai yawan fara’a da saurin sabo da mutane. Kasa daurewa ya yi ya kira Mahaifiyarsa ya sanar mata wannan abun farinciki. Farincikin data tsinci kanta a ciki ba zai misaltu ba, ta cewa Ahmad kar ya taho Abuja ya jira komai dare za su zo Kano su yiwa gidan da suka riƙi su Afrah godiya. Suna gama wayar kuma ta shiga kiran ƴan’uwa da abokan arziki tana sanar musu anga su Afrah.

Hajiya Neehal tana kwance tana chatting da Habibinta bata san mai yake faruwa a gidan nasu ba. Shigowar Mama yasa ta tashi zaune. Mama ta ce “Har yanzu bacci kike ne?” Ta ce “A’a idona biyu, yanzu ma so nake na tashi na je saloon a wanke mun kai na.” Mama ta ce “Jiya da kika je ɗauko su Afrah ashe kin gamu da wani yace miki ya san su?” Gabanta ya faɗi ta dubi Mama da sauri ta ce “Eh, amma wa ya faɗa miki?” Mama ta ce “Da kansa ya zo ya faɗa mun, yanzu haka ma suna part ɗin baƙi shi da Mahaifin su Afran.” Neehal ta waro Idanunta sosai ta ce “Ta yaya suka san suna gidan nan to? Mama anya kuwa dagaske mahaifin nasu ne? Kar fa wasu su zo su miki ƙarya.” Mama ba ta ce komai ba ta girgiza kai kawai ta juya ta fice. Neehal ta sauko daga kan gadon da sauri ta biyo bayan Mama ƙirjinta na dokawa. A falo ta ci karo da Amrah sanye cikin uniform, cikin murna Amrah ta kama hannunta ta ce “Aunty Daddy ya zo, ki zo mu je ki gan shi ya ce mu kirawo ki, ashe dama ya san gidan nan?” Neehal ta shafa fuskar yarinyar ta ce “Dagaske Daddy’nku ya zo? Yana ina?” Amrah ta ce “Yana wani falo, mu je ki gan sa.” Neehal ta tsaya cak cikin tsananin shock, zuciyarta cike da murnar bayyanar iyayensu. Ta kama hannun Amrah tana murmushi suka koma ɗakinta ta ɗauko Hijab ta zira, sannan ta ƙara kamo hannunta suka fito. A kitchen ta tarar da Mama da su Dije suna ƙoƙarin haɗa girki dan tarb’ar baƙi, dan Ahmad ya sanar mata su Umminsu suna nan tafe. Haka Kawai Neehal ta tsinci kanta cikin farinciki, duk da ta san lokacin rabuwa da twins ɗinta ya yi za su koma gurin iyayensu, tunda Allah ya bayyana su. Sai dai kuma suna zuwa part ɗin baƙin ta ji gabanta ya faɗi, ta ɗan tsaya a bakin ƙofar falon tana jin jikinta wani iri. Amrah ta ce “Aunty Daddy’n yana cikin falon nan mu je ki gan shi.” Neehal ta ce “Toh.” Cikin sauke numfashi, sannan ta ƙarasa ta tura ƙofar falon a hankali ta shiga bakinta ɗauke da sallama cikin zazzak’ar muryarta. Ahmad wanda yake ta murmushi yana sauraren hirar da Afrah take masa ya d’ago ya dubi ƙofar falon, karaf idanunsa suka sauka akan Neehal wadda kanta ke ƙasa, hannunta riƙe da na Amrah……..✍️

By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:55] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

4️⃣0️⃣

………..Samun kansa ya yi da kafe ta da ido kamar mai san gano wani abu a tattare da ita. Afrah ta sauka daga jikinsa ta tafi gurin Neehal da gudu cikin murna tana faɗin “Aunty! Daddy’nmu ya zo, kin gan shi.” Ta ƙarashe maganar tare da kamo hannunta tana nuna mata Ahmad. Neehal ta d’ago kanta tana murmushi ta shafa kan Afrah ta ce “Thank God.” Ai Ahmad ji ya yi gaba-ɗaya yawun bakinsa ya ƙafe ƙaf tare da wani irin bugawa da zuciyarsa ta yi. Ƙara ware idanunsa ya yi a kanta dan tabbatar da abun da yake gani kar ya je ko idon ne yake masa gizo, har abada ba zai taɓa manta wannan kyakkyawar fuskar ba. Neehal ta ɗan saci kallonsa a hankali cikin sanyin muryarta ta ce “Ina yini.” Ahmad ya sauke wani dogon numfashi yana murmushi ya ce “Lafiya k’alau Aunty.” Neehal bata kuma ce masa komai ba saboda tsintar kanta da ta yi uncomfortable tun shigowar ta falon, ta mayar da kallonta ga Musbahu wanda yake ta aikin latsa waya, posting ɗin hotunan su Afrah yake a social media tare da yin note ɗin bayyanarsu. Gaishe sa ta yi, ya d’ago ya dube ta tare amsa mata cikin fara’a, ita kuwa duk sai ta ji kunya ta kama ta saboda abun da ta masa jiya dan ta shaida sa. A hankali ta ƙarasa kan kujera ta zauna, su Afrah na jikinta suna mata hirar Daddy’nsu, duk da gashi nan a zaune a gabanta ya zuba mata na mujiya, ko kifta idanunsa ba ya yi. Amrah ta koma jikinsa tana masa surutu, amma ba ya ma saurarar abun take cewa, zuciyarsa gaba_ɗaya tana gurin Neehal. Ita kuwa Neehal tun tana daurewa tana biyewa Afrah har ta yi mata shiru tare da turo bakinta gaba, duk d’agowar da zata yi sai sun haɗa ido da shi, gashi idanun nasa sun sa ta fara jin wani iri ajikinta, gaba-ɗaya  ya dabaibaye ta da kallonsa. Gajiya ta yi da kallon nasa ta miƙe ta fice daga falon a ranta tana faɗin “Wannan kuwa lafiyarsa k’alau? Ko dai ganin yaransa ne ya zautar da shi?” Ahmad ya sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi tare da lumshe idonsa bayan ta fice. Fateemah,Neehal,Princess. Ita ce ko mai kama da ita? Dagaske ita ya gani ko kuma dai mafarki yake? Idan ita ce wacce irin lucky day ce wannan a rayuwarsa? “Oh my God!” Ya faɗa cikin siririyar murya, at the first da ya ganta ji ya yi kamar ya je ya rungume ta, ba ƙaramin control ɗin zuciyarsa ya yi ba wajen ganin bai aikata hakan ba, sai dai duk yadda ya so ɗauke idonsa daga kanta kasawa ya yi, wani maganaɗisun abu ya ji yana fizgar zuciyarsa a game ita, wadda bai taɓa jin irinsa akan wani mahaluƙi ba.

        Neehal ta koma part ɗin Mama tana ɓaɓɓata fuska, a ranta tana ta gulmar Ahmad. Sosai ta ga kamminsa da yaransa kamar ma ya fi su kyau. Kitchen ta shiga suka cigaba da aiki tare da su Mama. Sai da su Ahmad suka tafi masallaci sannan su Afrah suka dawo part ɗin Mama, a lokacin ne kuma Daddy ya ƙaraso gidan. Bayan sun dawo daga masallaci Mama ta aika musu da drinks da ɗan abun tab'awa. Neehal tana cikin Sallah Afrah ta shigo ɗakinta tana faɗin "Aunty ki zo in ji Daddy'nmu." Ganin tana Sallah sai yarinyar ta fita. Ko da ta idar ƙin fita ta yi, ta ɗauko wayarta dan kiran Haneefah da Sadik ta sanar musu bayyanar iyayensu Amrah.


          Kafin la'asar Su ummi sun ƙaraso Kano zuciyoyinsu cike fal da farinciki, Ahmad da kansa ya je ya ɗauko su a Airport. Su uku suka zo, da Ummi da wata ƙanwarta Aunty Mardiyya sai Zahra ƙanwar Ahmad. Cikin fara'a da mutuntawa Mama ta karɓe su hannu bibbiyu. Aunty A'isha ma ta zo a lokacin, Aunty Sadiya ce dai ba ta zo ba tana gurin aiki. A part ɗin Mama aka sauke su, hakan yasa su Ahmad su ma suka dawo nan. Ummi ta rungume su Afrah a jikinta tana hawaye tare da godiya ga Ubangiji, murnarta guda biyu ce a wannan rana, ta farko bayyanar jikokin nata, na biyu kuma ta san yanzu farinciki da walwalar ɗanta za su dawo, kuma lafiyarsa zata samu Insha Allah. Su Afrah kam yau take Sallah a gurinsu, kowa sai rungumar su yake da murnar ganin su, suma daɗi suke ji ba kaɗan ba na ganin su cikin ahalinsu. Bayan an gama murnar, su Ummi sun yi sallar la'asar Mama ta gabatar musu da abinci. Ahmad kuwa duk wannan abun da ake rabin hankalinsa ne a gurin, rabi yana gurin Neehal, gashi ko wulgawarta bai ƙara gani ba, ya tura su Afrah ya kai sau biyar su kira ta amma Neehal ta ƙi fitowa, sai dai su dawo su ce masa bacci take. Bai taɓa tunanin akwai abun da zai iya ɗauke masa hankalin murnar ganin Ƴaƴansa ba, sai gashi tozalin da ya yi da Neehal ya raba masa hankali, wani irin farinciki yake ji a cikin ransa, burinsa kawai yanzu ya samu ya tattauna da ita dan ya tabbatar ita ɗin ce.





         Bayan su ummi sun gama cin abincin aka zauna zaman mai da zance. Ummi ta dubi Mama ta ce "Yanzu duk tsawon watannin nan yaran nan suna tare da ku a gidan nan? Tsintar su kuka yi ko yaya?" Mama ta bawa Ummi labarin yanda Neehal ta tsinci su Afrah, da yanda akai ta cikiyar neman iyayensu . Cikin al'ajabi Ummi ta ce "Ikon Allah, Ubangiji ne ya kub'utar da yaran nan daga hannun azzaluman da suka ɗauke su, domin kuwa duk wanda ya ɗauki yaran nan da wani mugun nufin ya ɗauke su sai kuma Allah bai bashi nasarar cimma abun da ya yi niyya ba akansu." Aunty A'isha ta ce "Fita suka yi waje aka ɗauke su ko kuma a makaranta ne?" Ummi ta ce "Ba ɗaya, har cikin gida har falonsu aka shigo aka ɗauke su. Ita mai kula da su ta shiga wanka a ɗaki, su kuma suna falo suna kallo, sai fitowa ta yi ta ga babu su a falon, ta shiga ƙwala musu kira tana zaga ko ina na gidan amma bata gan su  ba, ta fito ta tambayi mai gadi a ruɗe ko ya ga fitarsu ko kuma shigowar wani ya fita da su, amma ya ce babu wanda ya shigo kuma babu wanda ya fita. Hankali a tashe ta kira ni ta sanar mun, na kira mahaifinsu na tambaye shi ko shi ya dawo ya ɗauke su, ya ce shi bai ma koma gida ba yana office, na kira gidan kakaninsu nan ma suka ce ba su zo ba. Wasa_wasa ƙaramin abu ya zama babba, muka fahimci yara fa sace su akai, tunda har dare babu su babu labarinsu. Tashin hankalin da muka shiga ba zai misaltu ba, mahaifinsu kuwa yanke jiki ya yi ya faɗi a sume ciwonsa ya tashi. In tak'aice miki zance ya sha jinya kamar ba zai rayu ba, har waje sai da aka fita da shi, daga baya kuma Ubangiji ya kawo masa sauƙi, har ya warware. Ba mu fi wata da dawowa daga India ba, satinsa biyu ma da komawa gurin aiki." Mama ta ce "Allah sarki, yaran mahaifiyarsu ta rasu ko?" Ummi ta ce "Ehh, a gurin haihuwar su Allah ya mata rasuwa." Mama ta ce "Allah ya ji k'anta ya gafarta mata." Nan dai sukai ta tattaunawa akan batun, Ummi ta kira Ammi kakar su Afrah ta haɗa ta da Mama, ta yi mata godiya sosai, sannan ta bawa su Afrah wayar ta ji muryar ƴan jikokin nata kafin ta gan su. Ummi ta kalli su Afrah ta ce "Ni fa tun d'azu ana ta bani labarin Aunty amma har yanzu ban gan ta ba." Mama ta ce "Au bata sakko ba, ban ma lura ba muna ta hira bari na kira ta." Mama ta miƙe ta hau sama su Afrah na biye da ita a baya. Fitowarta kenan daga wanka Mama ta shigo ɗakin, Mama tana kallonta ta ce "Kakannin su Afrah sun zo amma shine baki sauko kun gaisa ba dan iskanci." Neehal ta ce "Mama bacci ne fa ya ɗauke ni, yanzu na tashi." Mama bata ce komai ba ta juya ta fita. Afrah ta ce "Aunty, Ummi da Aunty Zahra sun zo suna falon ƙasa." Neehal ta ce "To bari na shirya mu je na gan su." 


       Tare suka sauko da su Afrah, tunda ta fara sakkowa ya zira mata na mujiya yana sakin ajiyar zuciya, sai ya ga kamar ta ƙara yi masa kyau fiye da d'azu. Neehal bata lura da shi ba ma a falon, ta gaishe da Ummi cikin girmamawa, Ummi ta rungume ta tana sanya mata albarka tare da yi mata godiya cikin k'aunarta. Tana dariya ta ce "Zauna anan kusa da ni kin ji d'iyata ƴar albarka." Neehal ta yi ƙasa da kanta cikin jin kunya. Zahra ta waro Ido ta ce "Laaa kamar Neehal ɗin ASTV." Aunty A'isha ta yi murmushi ta ce "Ita ce." Zahra ta dawo kusa da Neehal tana murmushi ta ce "Nice to meet you Aunty Neehal and I love You." Ta yi murmushi itama ta ce "Thank you, ya kike?" Zahra ta ce "Lafiya k'alau." Hira Zahra ta shiga yiwa Neehal, dan ba laifi akwaita da surutu. Neehal kuwa gaba_ɗaya jinta take a takure, ta rasa dalili kuma, nan kuwa kaifin idanun Ahmad ne yake yawo a jikinta. Ta ɗan juyo dan ta gaishe da Aunty Mardiyya karaf suka haɗa ido da shi ya mata ƙuri, ta ɗauke idanunta da sauri a ranta tana mitar yau ta gamu da gamunta, mutum daga zuwa ya mayar da ita TV'nsa. Bayan sun gaisa da Aunty Mardiyya ta janyo Afrah ta mata raɗa a kunnenta da faɗin "Je ki cewa Daddy ya daina kallo na." Yarinyar ta kalle ta zata yi magana Neehal ta ce "Shiiii, go and tell him I will give you chocolate." Afrah ta tafi da sauri ta haye jikinsa, cikin raɗa kamar yadda Neehal ta ce mata ta ce "Daddy, Aunty ta ce ka daina kallon ta." Ahmad ya ja hancin yarinyar ya ce "Go and tell her, ciwo idona yake mun idan ban kalle ta ba." Afrah ta ce "Daddy kasa glass ɗinka zai daina ciwon." Ya girgiza mata kai ya ce "No, idan ina kallon Aunty ne kawai zai daina." Afrah ta tashi daga jikinsa ta koma gurin Neehal ta faɗa mata abun ya ce. Neehal ta kalle shi tana turo baki gaba, shi kuma ya wani marairaice fuska yana ƙara tsare ta ido tare da sakar mata murmushinsa wanda yasa ta ji gabanta ya faɗi, da sauri ta ɗauke kanta daga kallon sa tana ɓata fuska. Wajen ƙarfe biyar suka fara shirin tafiya, Mama ta ce Su bari sai gobe mana, amma Ummi ta ce "Ba zai yiyu ba, dan Family suna can suna jiran dawowar su, kowa yana d'okin ganin su Afrah, tun yanzu an fara addabarta da kira inaga sun kwana."  Mama ta dubi Neehal ta ce "Je ki haɗowa su Afrah kayansu." Ta miƙe da sauri dama duk a takure take da kallon da Ahmad ya addabe ta da shi, Zahra ta bi bayanta dan taya ta haɗa kayan. Jiki a matuƙar sanyaye ta shiga haɗa musu kayan, tare da ƙoƙarin danne kukan da yake ƙoƙarin k'wace mata. Bata taɓa tunanin zata rabu da twins ɗinta nan kusa ba, tana son yaran sosai ta shak'u da su over, suna matuƙar ɗebe mata kewa, yanzu gashi rana ratsa Allah zai raba su kamar yadda ya haɗa su. Ta haɗa musu kayan sawarsu a wata ƙatuwar jaka, suka kama ita da Zahra suka sauka da ita ƙasa. Ahmad ya taso da sauri ya karɓe su yana faɗin "Sannu Aunty, thank you so much." Ta masa shiru ba ta ce komai ba sai ma juyawa da ta yi ta koma sama. Ummi ta dubi Zahrah ta ce "Ta tattara kayan da suka ci abinci ta kai kitchen." Ahmad ya faki idon mutanen falon ya bi bayan Neehal da sauri. Yana shiga falon sama ita kuma tana rufo ƙofar ɗakinta, hakan yasa ya gane nan ta shiga ya nufi ɗakin cikin murna ya tura ƙofar ya shiga. Tana shiga ita kuma kukan da take ta dannewa ya kufce mata, ta kwantar da kanta a jikin gado ta shiga rera shi. Ya tsaya a bakin ƙofa tare da hard'e hannuwansa a ƙirjinsa yana sauraren sautin kukan da take, wanda ko ba'a faɗa masa ba ya san na rabuwa da twins ne........✍️

By
Zeey Kumurya
[10/03, 08:56] Zeey Kumurya: ⚡ NEEHAL⚡

By
Zeey Kumurya

4️⃣1️⃣

Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial 1314# or 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.
Subscription for DStv gotv star time electric pay bills Whatsapp OR
Call 08066268951

……….A hankali ya fara takawa ya ƙarasa inda take, tsugunnawa ya yi a daf da ita cikin sanyin murya tare da marairaicewa ya ce “Please Aunty stop crying.” Neehal ta d’ago kanta da sauri tare juyowa a tsorace dan ba ta ji shigowar sa ba, sai maganarsa kawai ta ji. Ta ɗan ja baya tare da kallonsa cikin mamakin ƙarfin hankalinsa na shigo mata har cikin daki. Ya marairaice fuska kamar ƙaramin yaro tare yi mata alamar rok’o da hannunsa. Ta tsaida kukan da take cikin jan numfashi tare da ƙoƙarin miƙewa tsaye, hannu ya zira a aljihun wandonsa ya ɗauko handkerchief ɗinsa ya miƙa mata, ta karb’a ba tare da ta ce komai ba, ta shiga share hawayen fuskarta. Wani sassayan k’amshi ya daki hancinta wanda yasa ta sakin ajiyar zuciya ba tare da ta shirya ba tare da lumshe idanunta. “Princesss!” Ya faɗa murya ƙasa_ƙasa tare da jan sunan, buɗe idonta ta yi da sauri ta sauke su akan fuskarsa cikin nazartar wani abu. ‘Princess?’ ta maimaita sunan a ranta kamar mai son tuno wani abu, kusancin da suka samu a yanzu yasa ta samu damar ƙarewa fuskarsa kallo sosai, sai ta ga kamar ta san fuskar, amma ta rasa a ina ta santa, ko kuma dan yana kama da su Afrah ne shi yasa. Ta kawar da kanta da sauri ganin yanda yake sakar mata wani murmushi wanda yake ƙoƙarin zautar da zuciyarta. ‘He is Handsome.’ ta faɗa a ranta tare da miƙewa tsaye da sauri kamar wadda aka tsikara, shima miƙewar ya yi still idanunsa na kanta. Ba tare da ta kalle shi ba ta miƙa masa hancky ɗinsa tare da faɗin “Thank you.” Ya karɓa tare da faɗin “You are welcome, and I want to talk to you.” Da sauri ta kalle shi ta ce “Ni kuma.” Ya gyaɗa mata kai, ta ce “Okay ina jinka.” Ya ɗan ja numfashi sannan ya fara magan “Tun d’azu nake son na miki godiya akan tsintar yarana da kikai a titi kika ɗauke su ba tare da ƙyama ko tsoron wani abu ba, and…..” “Kar ka damu ai yiwa kai ne.” Ta katse shi da faɗin haka. Ya yi murmushi ya ce “Duk da haka ba kowa ne zai iya abun da kika kai ba, hakan ya nuna kina da kyakkyawar zuciya mai cike da tausayi da jin ƙai. Allah ya biya ki ya albarkaci rayuwarki, ya yaye miki duk wani abu da yake damunki a cikin rayuwarki, ya yi miki tukuci da gidan Aljanna.” Cikin jin daɗin addu’arsa ta ce “Ameen ya Allah na gode sosai, Allah ya raya mana twins.” Ya ce “Amin, and secondly I……” Turo ƙofar ɗakin da akai ya katse masa maganar da yake yi. Zahra ce ta shigo ɗakin bakinta ɗauke da Sallama. Da mamaki ta ce “Yaya Doctor dama kana nan, muna ta nemanka zamu tafi, Ummi ta kira wayarka baka d’aga ba.” Ya juya ya nufi ƙofa yan faɗin “Ina nan ina yiwa Aunty godiya.” Zahra ta yi murmushi ta ce “Gaskiya ne.” Neehal ta ƙirƙiro murmushi tana kallon Zahra bayan ya fice ta ce “Har kun fito?” Zahra ta ce “Ehh, sai tafiya.” Neehal bata kuma cewa komai ba ta ɗauki wata leda dake cike da kayan wasan su Afrah suka fice daga ɗakin zuwa downstairs.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button