NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

Ta ɗauke idonta daga kallonsa da sauri ta mayar ga su Afrah tana murmushi ta ce “Welcome dear, I missed you alot.” Amrah ta ce “Missed you too Aunty.” Ta ce “Ya school? Dafatan dai kuna karatu sosai?” Suka gyaɗa mata kai. Ta ce “That’s is good, ina Ummi da Aunty Zahrah da Ammi?” Afrah ta ce “Suna gida mun bara su, Aunty Zahrah ta ce zata biyo mu Ummi ta hanata.” Ta zauna sosai a kan carpet ɗin falon ta ɗaura su duka akan cinyarta suna yi mata hira, ko ƙara kallon inda Ahmad yake bata yi ba. Shi ma bai ce mata komai ba sai zama da ya yi yana kallonsu. Har su Dije suka dawo falon suka ajiye masu drinks da snacks. Ganin da gaske ba kula shi zatai ba ta yaranta kawai take sai ya cewa su Afrah su tashi daga jikinta ba su ga bata da lafiya ba. Yaran suka tashi da sauri suna faɗin “I’m sorry Aunty.” Neehal ta ɓata fuska ba ta ce komai ba, ta miƙe ta kamo hannunsu da nufin su wuce sama, a hankali kanta na ƙasa ta ce “Ina kwana.” Ya k’ank’ance ido yana dubanta ya ce “Lafiya, ya jikin naki?” Ta ce “Da sauƙi.” Ya ce “Allah ya ƙara sauƙi.” Tare da miƙewa ya ce wa su Afrah su ya kai su gidan Mamy, da yamma sai ya dawo da su. Neehal ta ce “Daga zuwanku, dan Allah ka bari idan Mama ta dawo sai mu je tare.” Ya ce “Ke da baki da lafiya kuma zaki fita, idan kin ƙara warwarewa sai ku je, tunda za su kwana biyu a nan.” Bata ce komai ba ta saki hannun yaran ba don taso ba. Ya kama hannunsu suka juya za su tafi, ta kalli abubuwan da su Dije suka ajiye masa ta ce “Uncle ko ruwa baka sha ba zaka tafi?” Ya yi mata ɗan murmushi ya ce “Idan na dawo zan sha.” Ta ce “Shikenan sai kun dawo ɗin, Allah ya kiyaye.” Ta d’agawa su Afrah hannu tana faɗin su gaishe mata da Mamy. Bayan fitar su ta zauna akan kujera zuciyarta cike da farincikin zuwan yaran. Ta miƙe dan kai trolley ɗinsu ɗakinta sai ta ga ƙaramar waya keypad akan kujerar da Ahmad ya zauna, da alama dai tasa ce ya manta ta. Wayarta ta ɗauko akan centre table da sauri ta kira shi dan ta sanar masa ya manta wayar tunda bai yi nisa ba ya dawo ya ɗauka. Ringing biyu ya d’aga, ta ce “Uncle ka manta ƙaramar wayarka a nan.” Ya ce “Ohh, ki ajiye mun ita kawai Princess, idan na dawo anjima sai na karb’a.” Ta ce “Tom Allah ya kai mu.” Daga haka ta katse kiran. Ta ɗauki wayar ta ja trollin su Afrah ta yi upstairs. Tana shiga ɗakinta ta ji cikinta ya fara juya mata hakan yasa ta kwanta, ba jimawa da kwanciyar tata bacci ya ɗauke ta.

Sai wajen Azhar Mama ta dawo gidan, ita kaɗai ta dawo Daddy ya wuce gurin sabgoginsa. Kitchen ta faɗa ta ɗora girki, sannan ta barwa su Dije su ƙarasa dan ita Hospital zata tafi aiki, ta bar musu sallanun idan Neehal ta tashi su ce mata ta wuce office, a bakinsu take jin labarin zuwan su Afrah da mahaifinsu, ta ji daɗi itama sosai ta ce Insha Allahu zata dawo da wuri kafin su dawo daga gidan Mamy……

A gidan su Sadik kuwa yau tun safe Kawunsu ya zo gidan shi da Hajiyarsu (Kakar su Sadik) wadda kawun ya biya ya taho da ita. Maamah ta tarb’e su cikin mutuntawa da girmamawa. Umma kuwa yau ita ce da girki tana ɗakin Abba tana zuba masa kissa da kisisina, zuwan su Hajiyan yasa suka fito tare da Abban. Bayan an gama gaggaisa sun taɓa abun da Maamah ta kawo musu Kawu ya gyara zama ya dubi Abba ya ce. “Surajo Rukayya ta kira ni ta sanar da ni wani zance mara daɗin ji da ma’ana.” Abba ya kalli Umma ya ce “Wanne zance kenan Yaya?” Kawu ya ce “Zancen yarinyar da Abubakar yake neman Aurenta mana.” Hajiya ta tari numfashin Abba da faɗin “Au Sadik ɗin har ya fara neman Aure ba mu da labari?” Abba ya ce “A’a, soyayya dai kawai suke, tunda shi batun Aure dole sai an fahimci juna kafin akai ga maganar yin sa.” Hajiya ta ce “Gaskiya ne, To Allah ya taimaka. Amma me ya faru da ita yarinyar?” Kawu ya kwashe duk abun da Umma ta sanar masa ya faɗa musu. Hajiya ta zaro ido tana jinjina kai ta ce “Kai! Gaskiya kuwa matuƙar haka ne da matsala, to ya rabu da ita mana ya nemi wata, ga ƴan mata nan burjik da yawa a gari sai ya zab’a ya darje.” Maamah ta sunkuyar da kanta ƙasa cikin rashin jin daɗi, Umma kuwa murmushin farinciki ta saki a ɓoye.” Abba ya ce “Ni fa Hajiya a gani na wannan duk ba matsala ba ce, yarinyar nan na yi binkice a kanta da iyayenta sosai mutanen kirki ne, mahaifinta ba b’oyayyen mutum ba ne, dan ya taɓa tsayawa takarar shugaban ƙasa, daga baya kuma ya daina siyasar kwata_kwata. Duk da dai ba shi ya haife ta ba, amma a matsayin mahaifi yake a gurinta tunda shi yake riqon ta.” Maamah tay saurin d’ago kanta a karon farko ta ce “Au ba shi ɗin ne ya haife ta ba dagaske?” Abba ya ce “Ehh, amma itama yarinyar an tabbatar mun mahaifinta kafin ya rasu mutumin kirki ne, kuma ɗan asalin jihar nan ne a ƙaramar hukumar Gabasawa.” Kawu ya ce “Wane ne marik’in nata?” Abba ya ce “General Alhaji Muhammad Tafida.” Kawu ya jinjina kai ya ce “Tabbas na san sunan mutumin sananne ne, to amma mu yanzu ba nasabarta ce abun damuwar mu ba, damuwar mu batun kashe duk wanda ya ce zai aure ta da ake yi.” Hajiya ta ce “Gaskiya fa, abun nan abun dubawa ne, dan watakila aljanu ne da ita suka aure ta.” Umma ta ce “Nima abun da na gani kenan Hajiya, hankalina gaba-d’aya ya tashi har na kasa haquri na kira Yaya na sanar masa dan a yiwa tufkar hanci, tunda shi Abban nasu ya ƙi saurara ta.” Abba ya ce “To, gaskiya ni dai duk a iya binciken da na yi ban ci karo da wannan labarin ba, kuma itama Rukayyan ban san a ina ta samo shi ba.” Umma tay karaf ta ce “Ai ita marik’iyar yarinyar akwai ƙanwarta a nan unguwar, nan gaba kaɗan ne da mu babu nisa, to a gurin wata mak’ociyarta na ji wannan labarin, kuma babbar mace ce baza tay mun ƙarya ba.” Abba ya ce “Ka ji fa, watak’ila ma ba gaskiya ba ne zuzutun abu ne irin naku na mata.” Hajiya ta katse shi da faɗin, “Ba wani zuzutun mu na mata, maganar nan fa ya kamata a duba ta, kar mu zo mu yi abun da za’ai dana sani daga baya.” Kawu ya ce “Ato, faɗa masa dai Hajiya.” Abba ya ce “Shikenan, zan yi sabon bincike akan hakan Insha Allahu, idan ya tabbata haka ne sai ya haqura da ita ya nemi wata kawai.” Daga haka suka rufe wannan chapter suka kama wata……

Sai da ƙarfe biyu na rana ta wuce sannan Neehal ta tashi daga baccin da take, shima ƙarar wayar Ahmad da ake ta kira ne ya farkar da ita. Tashi zaune ta yi tana kallon agogon bangon dake ɗakin, mamaki ne ya cika ta ganin ta yi fiye da awa uku tana baccin. Ta sauke numfashi a ranta tana tunanin may be a cikin magungunan data ke sha akwai na bacci, dan wannan baccin nata daga jiya zuwa yau ya yi yawa. Ta sauko daga kan gadon domin yin Sallah, wayar Ahmad ce ta ƙara yin ringing alamun shigowar kira. Kamar ta share sai kuma ta ɗauki wayar ta duba mai kiran, Jamila sunan da ta gani kenan akan ɗan screen ɗin wayar. Ta mayar ta ajiye sannan ta nufi toilet dan yin alwala. Bayan ta fito ta ji still ana kuma kiran wayar, bata bi takan ta ba dan dama dalilin da yasa ta kira shi ya dawo ya ɗauka kenan kar ayi ta kiransa a wayar ba’a same shi ba. Har ta yi Sallarta cikin nutsuwa ta idar ba’a daina kiran wayar ba. Ta yi ɗan tsaki ta tashi ta je ta ɗauki wayar, 17 missed calls ta gani kuma duk mutum ɗaya ce wato Jamila. Ta tab’e baki ta ajiye ta sauka ƙasa. Ƙwaƙwa da dabinon da Daddy ya siyo mata ta ɗauko a cikin fridge ta zauna ta fara ci bayan ta ɗibarwa su Dije. Bayan ta gama ci ta ɗebo abinci kaɗan ta ci. Koda ta koma ɗakinta dan yin sallar la’asar sai tarar wayar tana ringing, still a fili ta ce “Kai wannan mai kiran akwai naci, tunda ta kikkira ta ga ba’a ɗauka ba ai sai ta haqura.” Ta d’aga wayar a kufelen da ita kanta bata san ko ta mecece ba ta ce “Mai wayar ba ya kusa.” Bata jira amsa ba ta katse wayar. 5 missed calls ta gani bayan na d’azu, kuma duk dai mutum ɗaya ce, sai kuma 4 unreaad message data gani. Har zata ajiye wayar sai kuma ta shiga message ɗin ta gani, ɗaya na kamfani ne sauran ukun kuma duk na Hajiya Jamila ne. Ta shiga na farko ta ga abun da ta turo, Please Dear pick my call. ta fita ta shiga na biyu ta ga shi kuma haka ta rubutu, Dama kiran ka nay in ji lafiyar ka, dafatan kana lafiya Habibi? bata karanta na ukun ba ta ajiye wayar saboda takaici. Haka kawai ta ji ranta ya ɓaci ba tare data san dalili ba. Ta nufi kan darduma ta tada ik’amar Sallah dan tana da alwalarta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button