NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

A gidansu Sadik kuwa, tun bayan da k’aninsa Bashir ya je tashin sa da asuba dan su tafi masallaci kamar yadda suka saba kullum, duk wanda ya riga ɗan’uwansa tashi shi zai je ya tashe sa. Tun daga ganin ƙofar ɗakin a ɓalle a ƙasa ya san da matsala, cikin mamaki ya shiga ɗakin yana k’wala masa kira da tambayar sa dalilin ɓalle ƙofar. Jin shiru kusan mintuna biyar yasa ya lek’a toilet inda yake tunanin Sadik ɗin yana ciki, amma sai ya ga wayam babu kowa. Ya fito ya dinga dudduba ɗakin har bayan labule amma babu shi babu alamar sa. Ya fito hankali a tashe ya duba bayan ɗakunan, nan ma babu shi. Sai ya yi tunanin ko masallaci ya tafi ya bar shi, duk da wata zuciyar na faɗa masa ba haka ba ne, amma dai ya nufi masallacin. Yana ta dube_dube amma ko mai kama da Sadik bai gani ba har aka idar da Sallah. Bayan sun fito daga Masallacin sun gaisa da Abban su ya sanar masa. Ba tare da damuwar komai ba, Abban ya ce masa su duba ɗakinsa na part ɗin Maamah may be yana can, tunda dama a can suke kwana saboda baƙi ne yasa suka dawo BQ. Wasa_wasa dai Bashir da Abba sai da suka duba ko’ina na gidan amma ba su ga Sadik ba. Suka dinga kiran wayar shi amma bai ɗauka ba, sai da suka koma ɗakin da ya kwana suka gan ta. Tun daga nan Abba ya san da matsala, Bashir ya ɗauki wayar da yake ya san pin ɗin Sadik ya buɗe wayar, ya duba last wanda suka yi waya ya ga Neehal ce. Har zai kira ta amma ya hana shi, dan ya san Sadik ba zai je gurinta ba tun asuba. Abokanansa suka dinga kira ana tambaya ko suna tare amma kowa sai ya ce A’a. Duk inda Abba yake tunanin Sadik zai je sun kira baya nan. Hankalin su fa ya ƙara tashi, Bashir ya fara kuka. Abba ne ma mai dauriya, ya fita ya tambayi mai gadi ko ya ga alamar wasu sun shigo gidan ko kuma ya ga Sadik ya fita? Mai gadi ya ce, Gaskiya babu wanda ya shigo ko ya fita daga cikin gidan, dan shi ya buɗe gidan ma da kansa da asuba. Hankali a tashe Abba ya kira ƴan’uwansa maza ya sanar musu dan su san abun yi, amma ya roƙe su kar su sanar da kowa, Bashir ma ya gargad’e shi kar ya sake ya sanar da Maamah, Insha Allahu za’a ga Sadik ɗin. Babu jimawa Ƴan’uwan Abba suka zo cikin tashin hankali, kowa na tambayar ina yaron nan ya tafi shi kuwa da sassafe ranar Auransa? Duk wani gidan abokan Sadik da Abba da Bashir suka sani sai da suka je neman sa, duk da sun kira su a waya sun ce basa tare, amma Abba sai yake ganin kamar ɓoye masa suke, Sadik ɗin yana tare da su. Har gurin telan dake masa ɗinki suka je, akan ko nan ya je can karɓar ɗinki, amma telan ya ce bai zo ba, dan tun last week ya gama masa ɗinkunansa duka ya ba shi. Mata na gida suna can suna cigaba da harkar girke_girke da harkokin biki basu san mai yake faruwa ba. Sai Maamah ce ma da ta ga har kusan 11 bai shigo cikin gidan ba ta yi mamaki, amma ko kaɗan bata yi tunanin wani abu ba. Duk wani abu da zai tabbatarwa da su Abba sace Sadik akai ya bayyana, dan haka wani k’ani a gurin Abba ya ce ya kamata a kira iyayen Amaryar a sanar musu halin da ake ciki. Shine Abba ya kira Daddy ya sanar masa. Bashir yana kuka wiwi ya shiga cikin gidan ya sanar da su Maamah abun da yake faruwa, faɗar irin rud’ewa da tashin hankali da Maamah ta shiga ba zai misaltu ba, ƙarshe ma sumewa ta yi saboda tsabar firgici. Cikin lokaci k’ank’ani zancen ɓatan Sadik ya baza gidan, nan fa aka fara koke_koke gidan biki ya koma kamar na zaman makoki. Umma ta dinga faɗin dama ta san haka zata faru, shi yasa ta ce kar a yi bikin nan amma Sadik ya dage, gashi nan ai. Hajiya kuwa iska ta tayar tana faɗin sai ta je gidansu Neehal sun fito mata da jika, kurwar jikanta ta fi ƙarfin su in ma su mayu ne. Da ƙyar aka riƙe ta dan sai fizge_fizge take tana ƙoƙarin k’wacewa ta fita. Ana cikin haka Su Abby (Mahaifin Maamah) suka ƙaraso gidan, sun taho da shirin d’aurin Aure suka tarar da wannan abun tashin hankalin. Daddy da shi da Yayansa da Kawu Musa da Uncle Usman da Uncle Mahmud suka je gidansu Sadik hankali a tashe. Har ƙarfe ɗaya ta wuce lokacin masallaci ya yi babu labarin Sadik, tuni Daddy Ya yi report ga Police da duk wani gurin da ya dace. Tashin hankalin da ahalin Sadik suke ciki a wannan rana ba zai misaltu ba.

Kamar yadda ahalin Sadik suke cikin tashin hankali haka su Mama suke ciki, sai dai su har wannan lokacin ba su bayyana labarin ɓatan Sadik a gidan ba. Daga ita sai Aunty A’isha, da Aunty Sadiya, da Ammi matar Uncle Mahmud sai Umma matar wan Daddy ne kaɗai suka sani, dan ko Hajiya ba su sanarwa ba, ita Mama Babban tashin hankalinta bata san ya Neehal zata yi ba in ta ji labarin ɓatan Sadik. Mama ta kira Daddy yafi sau 20 tana tambayar sa ko an ga Sadik, amma amsar ɗaya ce yake bata A’a. Sauran ƴan biki kuwa suna ta harkokin su, duk da ana ta neman Mama da tambayar ta dan tana part ɗin Daddy bata fito ba, saboda ana kallon ta za’a gane tana cikin tashin hankali. Mommyn Haneefah data fuskanci da akwai wata matsalar ita take replacing ɗinta, tana faɗawa masu tambayar ta cewa suna ɗan tattaunawa ne da ƴan’uwanta, yanzu zata fito.

Duk da halin tashin hankali da ake ciki amma haka su Daddy da su Abba suka tafi masallacin Juma’a, masallacin da aka saka za’a yi d’aurin Auren a can. Ai kuwa masallacin ya cika ɗank’am da jama’a, mutanen Daddy da ƴan’uwa dana Abba kowa ya hallara ana jiran a ɗaura Aure bayan an idar da Sallah. Daddy ya dubi Abba ya ce. “Amma Alhaji ina fata dai ɓatan Sadik ba zai saka a fasa wannan d’aurin Auren ba? duba yanda muka tara wannan dubban jama’ar.” Abba ya nuna Kawu dake gefen sa ya ce. “Ga waliyyin shi nan ku yi magana da shi, ni bani da ta cewa akan wannan maganar.” Daddy ya ja Kawu da Kawu Musa wanda shine waliyyin Neehal ya faɗa musu abun da ya cewa Abba. Kawu da dama jiran k’iris yake tunda ba k’aunar Auren yake ba, ya shiga masifa yana faɗin. “Tunda dama ba ɗansu ba ne ya ɓata ai dole ya faɗi haka, to wallahi ko Allah ya bayyana Sadik a yanzu baza a yi Auren nan ba, su sun fasa, wannan tashin hankalin ma kaɗai ya ishe su, a yanzu ma an sace shi in aka ɗaura Auran kuma ai sai kisa kamar yadda aka yiwa na baya, tunda ƴar tasu ta zama annoba, duk wanda zata aura sai an kashe shi.” Duk da ran Daddy ya ɓaci amma ya dinga ba shi haquri akan ya amince a ɗaura Auran, Insha Allahu Sadik ɗin zai bayyana a yau cikin k’oshin lafiya har su tare da matarsa. Duba da yadda jama’a suka taro dan halartar d’aurin Auren, yanzu kuma kawai sai a ce musu an fasa.” Kawu ya ce, ai kamawa ta yi dan haka batun wani d’aurin Aure ma a bar shi bai taso ba, su yanzu ta ɓatan ɗansu suke bata wani d’aurin Aure ba. Kawu Musa ya lallmi Daddy ganin yanda ya damu, ya ce masa ya bari a idar da Sallah sai su san abun yi, Insha Allahu baza a tara wannan Jama’ar a banza ba.

A dai-dai wannan lokacin aka gama yiwa Neehal make up ɗin, ta shirya cikin wani rantsatstsen farin less, an yi masa ado da golden colour, an ɗaura mata head golden, ta ci ɗan’kunne da sark’a da awarwaro na gold sai walwali suke. An yafa mata wani farin mayafi mai kamar net, sai tashin k’amshi dake. Hajiya tunda aka fara kwalliyar take ɗakin tana ta zuba santin kwalliyar. Kowa na ɗakin sai faɗin. “Masha Allah, amarya kin yi kyau, anya kuwa wannan angon naki zai gane ki in ya gan ki.” Neehal dai murmushin yaƙe kawai take, amma ita kaɗai ta san halin da zuciyarta take ciki. Gashi haka kawai ta ji ta fara damuwa da rashin kiran ta da Sadik bai yi ba, shi da kullum tun safe yake kiran ta, wataran ma shi yake tashin ta daga barci. Amma yau ranar farincikinsu a ce har yanzu bai kira ta ba, yanda yake ta zumud’in nan ta yi tunanin ba ƙaramin addabarta zai yi da kira ba, amma sai ta ga saɓanin haka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button